✨ *MATANA* ✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*EXQUISITE WRITERS FORUM*
*Wannan labarin ƙirƙirarre ne, banyi shi ɗan cin zarafin wani ko wata ba! Sannan idan yayi shige da labarinka/labarinki coincidence ne Yawwa*
*Comments share and vote dinku yana da matukar mahimmanci idan yayi karanci zan maida abuna ba kudi💃*
*Masu tambaya daga farko kuyi min maga ta Wannan number kar kiyi mgn ta group ban kulaki ba sbd ban fiye duba messages na groups ba. 08142904255**008*
Bayan Ammar ya isa Kano gidansu ya yafara nufa. A zaune ya tarar da Mami, Bilki, Maryam da kuma Fatima a falo suna kallo. Karasawa yayi bakinsa dauke da sallama. Maryam ce ta amsa sallamar. Zama yayi a kan kujera cikin ladabi ya ce, "Mami ina yini? "Lafiya lau" Mami ta amsa without second look. Shafa kansa yayi kaɗan yana dan murmushi, kallonsa ya mayar kan Maryam ya ce, "Yau ba makaranta ne? "Fatima sun gama neco ai, ni kuma yau da gudawa na tashi shiyasa" Taɓa baki yayi kadan yana gyara zamansa. Mami ce ta dinga zungurin Bilkisu dake kallo.. da ido tayi mata magana, a hankali Bilkisu ta tashi ta nufi kitchen, ta dan jima kafin ta fito rike da babban tray, a gabansa ta ajiye tana fad'in " Sannu da zuwa" "Uhm" Ya amsa ba tare da ya kalleta ba. "In zuba abincin? Ta kara fada looking at his cute face. "Kaɗan! Ya fada shortly. Kaɗan ɗin ta zuba tana ajiye masa.. wajen zamanta ta koma ta cigaba da kallo. Bayan sallar magrib Aunty Sadiya da Bilkisu ne a dakin Mami, ko minti 20 Aunty Sadiya batayi da zuwan gidan ba.. kallon Bilkisu take sosai fuska a haɗe ta ce, " Are you serious? Duk abinda na faɗa miki kinyi kuwa? A hankali ta gyada kanta alamar tabbatar wa. "Turaren da na biya 150k aka baki kina nufin baiyi aiki ba? A sanyaye Bilkisu ta ce, "Umma nayi amfani fa da komai yadda kika ce, har turaren, ya dai ce baya so in kara sawa kuma ko yau ma sai dana turarashi a jikina, na shafawarma duk na shafa" Ajiyar zuciya Aunty Sadiya ta sauke tana kallon ta da kyau ta ce, "Ke baki iya kissa bane Bilki? Komai sai an koya miki? Karki yarda ki bashi wata kofar tunanin wata mace! Da zarar anyi sau daya toh zance ya kare! Dan bazai ma iya hakuri ba, duk wannan girman kan da yake ji dashi da jijji da kai zai sauka wallahi" Ita dai Bilkisu bata ce komai ba. "Tashi ki bishi ku tafi, Yaya tace bayan magriba zaku wuce" Da toh ta amsa tana tashi ta fito daga dakin. Ammar kuwa na zaune kusa da kafafun maminsa, cikin nutsuwa Mami ke magana.. "Idan dai ka sani farinciki kasan kanka ka saka, na gama magana da kai tashi kuje, dare na yi" Da ok ya amsa yana tashi ya fito daga dakin, Bilkisu na zaune kusa da su Maryam, kallo daya yayi mata yana nufar bakin ƙofa. Tashi tayi ta nufi dakin Mami tayi mata sallama sannan ta bishi. Har suka isa gida uffan bai shiga tsakaninsu ba. A cikin mota ya fita ya barta dan tayi nisa cikin tunanin yadda zata bullowa lamarin nan! Ta tabbatar da ace Zara'u ce he won't be abounding her like this, Amma ai shi namiji kamar yaro yake, tasan abinda zatayi masa bazata zura masa idanu haka ba kamar sokuwa! Sai a lokacin ta lura baya cikin motar, fitowa tayi tana sauke ajiyar zuciya sannan ta shiga cikin gidan. Sai da Ammar yayi wanka sannan ya kwanta. Kaya Bilkisu ta cire ta saka kayan bacci sannan ta kwanta a gefansa. Runtsa ido Ammar yayi yana shaƙar khamshinta dake masa wani daɗi. A dan kasalance ya ce, "Baki ji me nace ba Bilkisu? "Na me fa? Ta fada cike da rashin fahimtarsa. " Banyi warning ɗinki akan saka wannan turaren ba? Ko kin mayar dani abun wasa da zan fada miki abu kiƙi ji? Tashi zaune tayi tana kallon sa fuska a haɗe ta ce, "Ai ba sawa nake ba, a haka nake dama chan" Tsaki yayi jin tana son raina masa hankali. Tashi yayi ya dauki pillow, da sauri itama ta sakko tana shan gabansa ta ce, " Ina kuma zakaje? Cike da mamaki ya kalleta, kara tsuke fuska yayi yana kallon cikin idanunta ya ce, " Matsa daga gabana! "This is unfair! Is in proper gaskiya, after all I'm your wife! Stop behaving like a kid mana! Ta fada ba tare da ta kalleshi ba. Mamaki ne ya cika Ammar ganin yadda take magana without any fear, chan ƙasan zuciyar Bilkisu kuwa dukan uku² kawai takeyi amma ko kadan fuskarta bata nuna ba. Tureta yayi yana fita daga ɗakin.. cikin tsantsar takaici ta zauna a bakin gado wasu hawaye na zubowa bisa kuncinta, she won't give up so easily! Ta fada a fili tare da goge hawayen dake kumatunta. Tashi tayi ta fito daga dakin, room din data san yana ciki ta nufa tare da murdawa taji a rufe.. knocking ta farayi tana fad'in " Yaya Ammar! Yana jinta yayi banza da ita har ta gaji ta koma daki.. Washegari da misalin karfe 12 na safe Fa'iza, Maryam da kuma Fatima suka zo gidan. "Bikisss! Cewar Fa'iza da karfi ganin falon wayam. Bilkisu dake zaune a gefan gado ta taso da sauri jin muryar Fa'iza. A falo ta gansu zaune, Fa'iza kuma tana niyyar shigowa dakinta.. "Ai mun dauka ba kowa" Cewar Fa'iza tana kare mata kallo kamar meson gano wani abu. "Shine ko sanarwa babu? "Uhmm kedai bari mu mafa bamu san da zuwan ba, yanzu ma daga gidanku muke shine Aunty Sadiya tace muzo nan" Nunfashi Bilkisu ta sauke tana jan hannun Fa'iza zuwa falon idanunta kan su Maryam. "Wai yaushene saukar ku Maryam? Bilkisu ta faɗa. " Tab izun mu 30 fa, ba yanzu ba" "Toh Allah ya kaimu" Da Amin suka amsa. "Wai ko ruwa bazaki bamu ba? Fatima ta tambaya idanunta kan Bilki. "Indai ni zan kawo miki ashe bazaki taba sha ba" Bilkisu ta bata amsa. Dariya sukayi, sannan Fa'iza tayi ƙasa da murya ta ce, "Wai baya nanne? "Eh, tun safe ya fita" Taba baki Fa'iza tayi tana sakin muryarta ta ɗora da faɗin " Lokacin bikinku sai dana turawa shegiar bakar budurwarsa hotuna da videos dama naji Yaya yace wai ya bata wannan arniyar wayar daya siya, mayya, ni nasan ba haka ta barshi ba wallahi, bari kiga fa hotanta, shekaran jiya na tura a wayar Yaya Umar" Taba baki Bilkisu tayi tana kallon Fa'iza dake latsa wayarta dan lalubo hotan. "Nima dai haka nace, kinsan fa day before yesterday mun hadu da zabiyar ƙanwarta nasan bata sanni ba, bansan me ya kaita gidansu Waheeda ba" Cewar Maryam fuska a kwabe.. "Banda kwadayi me zai kaita? Itama yayarta ai kwadayine yasaka ta nanewa Ammar ɗin, shegu dangin tsiya" Dariya suka saka gaba ɗaya.. portrait ne me kyau Ammar yayi mata kuma its seems unexpected tasha jalbab tayi kyau sosai bakinta a dan ture ta dan karkata, hotan yayi kyau... Dogon tsaki Bilkisu taja tana fad'in " Shegia! "Ta karshe ma kuwa, kinga gidansu kuwa? cewar Fa'iza tana fashewa da wata iriyar dariya. "Barni in bata labarin yadda gidan yake" Fatima ta amshe zancen.. "Lokacin da muka je Ni, Aunty Sadiya, da kuma Mami ke kinga tsakar gidan siminti duk ya farfashe? Ko famfo basu dashi, igiyoyin shanya ta ko ina a tsakar gidan, ga wata wakekiyar rijiya a tsakar gidan, ga uban gawayi na siyarwa da itace, ke! Dan ba baki gani ba" Itama ta ƙarashe zancen tana dariya. "Uhmm ita dai ta sani, Ammar dai na aureshi ya zama mallakina, sai taje ta ƙarata ai" cewar Bilkisu tana miƙewa tsaye... "Aikam dai, sai abi wani sarkin, taje chan ta nemi mijinta dai dai ita" Cewar Fa'iza. Bangaren Ammar kuwa ABJ ya wuce, gaba daya ya kasa sukuni saboda tunanin yanayin jikin Zarah. Kasancewar a mota ya tafi sai bayan axahara ya isa, horn yayi wa gate man din gidansu Musty, lekowa yayi ganin bakuwar mota ya sashi fitowa yana kallon motar da kyau, sauke glass Ammar yayi yana fad'in " Please bude! "Kai amma da naci mutumin nan yake, banda Alhaji da yace adinga bude maka kofa da sai dai kasan inda dare yayi maka! Cewar gateman din ciki². Buɗe masa gate din yayi ya shiga da motarsa ciki, parking yayi a wajen da aka tanada sannan ya fito duk jinsa yake a gajiye. Knocking din kofar falon yayi, Zainab dake kunna Bulb ta kalli kofar tana fad'in " Wai har Yaya ya dawo? Banyi wankin bandakin daya sani ba! Dariya Farida tayi tana kallon expression din fuskarta ta ce, "Da kyau! Sake knocking yayi.. da sauri Zainab ta bar wajen ta nufi dakin Musty. Tashi Farida tayi ta bude kofar.. kallonsan ta tsaya yi, lokaci daya ta tsuke fuskarta tana masa kallon up and down. "Zan iyaa shigowa? Ammar ya fada yana sakin murmushi. "Toh ba kowa a gidan, Ummi bata nan, Yaya da Daddy ma haka! Shafa kansa yayi kafin ya ce, "Ok zan zauna a verandah, but please turo min Zarah! Bata ce komai ta rufe kofar, ajiyar zuciya ya sauke yana neman wajen zama. Ya kai kusan 20mins kafin yaji an bude kofar.. itace, tasha dogon hijabi har ƙasa, hannunta sanye da cannula, fuskarta ta rame sosai. Tashi yayi ya bata waje ta zauna. "Ya jikin Zarah? "Da sauki" ta amsa so calmly. "Allah ya ƙara sauki, inaso ki daina yawan tunani da saka useless things a zuciyarki" Wani irin murmushi tayi me ciwo kafin ta ce, "U'r right! I should stop bothering and hurting my self for useless things, i hv bear nothing but pain after meeting u, I regret knowing you in my Life Ammar! Na rokeka ka kyaleni! Just go! Kaje ka cigaba da zama da matarka! You should leave me alone! I hate you! Durkusawa yayi yana kallon fuskarta data wanke da hawaye ya ce, "Karya kike Zarah! Bazaki taba dena sona ba, You can utter your anger by saying anything but don't you dare say that again! Ya fada yana kafeta da idanu.. goge fuskarta ta fara yi ta mike tsaye tana kallonsa, muryarta a raunane ta ce, "Dan Allah karka sake zuwa inda nake Dan Allah! "Hakan kika fi so? Ya fada looking onto her. Kai kawai ta gyada masa alamar eh. Ajiyar zuciya ya sauke yana dauke idanunsa daga kanta ya ce, "Shikanan bazan sake zuwa ba amma kiyi min alkhawarin daukar waya idan na kiraki" Bata ce komai ba ta shige cikin falon. Nunfashi me karfi ya sauke yana jingina da bangon wajen. Ya kai minti goma sannan ya nufi motarsa jikinsa duk a sanyaye. Zara'u kuwa na shiga daki kuka ta fashe da shi, haryanzu ta saka sawa zuciyarta salama, ta kasa bawa zuciyarta hakuri akan Ammar, ashe haka so yake? Tasha jin labarin yadda soyayya take musanman zafinta amma bata taɓa kawowa ta kai haka ba! Ko dai nata zafin daban? Turo kofar dakin akayi, Farida ce ta shigo tana kallonta. Da sauri ta goge hawayen da takeyi, rufo kofar dakin Farida tayi ta dawo kusa da ita ta zauna tana fad'in " Zara'u kiyi hakuri wannan kukan bashi da amfani wallahi, shi yana chan tare da Matarsa ke kina nan kina asarar hawayenki, dama rayuwarnan ba komai kake so kk samu ba, idan kika miƙa lamuranki zuwa ga Ubangiji tabbas zakiga sakamako me kyau, insha Allah zaki auri wanda yafishi, just keep praying Kinji ko? Zara'u bata iya ce mata komai ba, itama Farida bata damu da tace din ba ta fita daga dakin cikin tausayawa halin da Zarah ke ciki. Bayan komawarsa Kano gidan Hajiya Babba ya wuce saboda ciwan da kansa yake yi.. a kan kujera me cin mutun uku ya kwanta yana furzar da iska.. Fa'iza dake kallo a falon ta dan Kwabe baki ta ce, "Ina yini? "Lafiya lau, Hajiya da Umar fa? "Hajiya na daki, Yaya kuma ya tafi hira" bai kara ce mata komai ba ya tashi ya nufi dakin Hajiya Babba. A zaune ya ganta tana karanta littafin tarihin Annabi YUSUF AS. Zama yayi a gefan gado yana fad'in " Barka da dare Hajiya" Murmushi tayi kaɗan tana kallnsa tare da amsawa da yawwa. "Dazu nake zancenka ashe kana hanyar zuwa, ya iyalin? "Lafiya lau" Ya amsa yana dan bata fuska. "Baka jin dadi ne? Cewar Hajiya babba. "No stress ne kawai, Umar ya dade da fita ne? "Eh ya ɗan dade anjima kadan zaka ganshi baya jimawa ai" Kai kwai ya gyada yana kwanciya abinsa. Sai 10pm Umar ya dawo har bacci ya fara daukar Ammar. "Kai me kake yi har goma a gidan jama'a? Cewar Umar cikin tsokana. Karamin tsaki Ammar yayi ya tashi ya fita daga dakin Hajiya.. Dariya Hajiya tayi tana kallon Umar ta ce, "Dan Umari ba dai tsokana ba" Murmushi yayi yana fita shima. A dakinsa ya tarar da Ammar zaune ya rike kansa.. kusa dashi ya zauna yana fad'in "Lafiya dai ko? "Uhmm, da sauki dai Xarah tana bani ciwan kai da HBP wallahi" "Me kuma ya faru? Sai da Ammar ya sauke numfashi sannan ya ce, " Daga Abuja nake tun safe na tafi amma Xarah wai kar na ƙara zuwa inda take, kamar ma bata tausayina, naga kamar haushina ma take ji, kwata-kwata dama hankalina be kwanta da zamanta gidan ƙanwar mamanta ba, nasan kannen wanann Mustapha da shi kanshi munafukin Mustaphan zugata zasu dinga yi! Murmushi Umar yayi yana kallonsa ya ce, "Ka bata lokaci, ba maganar zuga ko rashinta bane, dole taji ba daɗi, kuma ba kowa zaka fadawa maganar nan ya yarda da kai ba, tabbas za'a ce yaudararta kayi, amma ka cigaba da addu'a stop worrying your self kar kaje asibiti kayi wa me zazzaɓi allurar nakuda! Ya ƙarashe maganar yana dariya. Murmushi kawai Ammar yayi yana miƙewa tare da gyara rigar jikinsa ya ce, " Sai da safe.... A kwance ya tarar da Bilkisu da alama bacci ya dade da daukarta.. Fukarta ya tsaya kalla for almost 5mins, kafin ya taba baki ya shiga toilet ya dan bata lokaci sannan ya fito sai da yayi Nafila kafin ya kwanta.. Buda idanunta tayi dan taji motsin kwnaciyarsa.. numfashi ta sauke a hankali tana juyowa su fara facing din juna, haɗe rai yayi ganin yadda ta kafeshi da ido. Rufe idanunta tayi tana jan duvet ta rufe har fuskarta. Numfashi ya sauke a hankali yana lumshe idanunsa, rayuwa bata fiya zuwar wa ɗan adam yadda ya tsara ta ba, tunda ya hadu da Zarah be taba tunanin ba ita zai aura ba, ko da wasa be taba kawowa cewa za'a ce an bashi mace a family dinsu ba.. buɗe idanunsa yayi yana tashi ya jingina da jikin gado, Wayarsa ya ciro a chaji ya hau kiran layin Zarah, Bilkisu kuwa mamaki ne ya cika, toh wa yake kira wajen 12 na dare? Bude duvet din tayi tana kallonsa. Tashi yayi ya fita daga dakin, kamar zuciyarta zata buga ta tabbata Zarah yake kira, wani abu taji ta tokare a wuyanta kamar ta fasa ihu dan takaici, kasa jurewa tayi ta tashi tabi bayansa, a jikin kofa ta tsaya tana kallon bayansa waya kare a kunnensa.. slowly taji ya ce, "Ya jikin naki? Bata ji me aka ce daga dayan bangaren ba ta sake ji ya ce, "Ok sorry zan kiraki da safe good nite" Daga haka ya katse wayar. Da sauri ta koma daki ta kwanta. Washe gari da safe da wuri ya wuce wajen aiki.. Ko abinci Bilkisu bata ci ba ta dauki wayarta ta shiga kiran layin mahaifiyarta.. ringing uku ta dauka tana fad'in " Lafiya kira da safe haka Bilki? "Nidai gaskiya na gaji wallahi, jiya fa raba dare sukayi suna waya da budurwarsa gaskiya bazan iya ba" Ta ƙarashe maganar tana sakin kuka. "Shi Ammar dinne ya raba dare yana waya da yarinya? Cewar Aunty Sadiya cike da mamaki. "Meyasa kike mamaki Umma? Ai kullum ma haka suke yi" "Kece sakarai ai! Kina me zaki bar mijinki ya samu damar waya da wata banza? Kamar ba Ni na haifeki ba Bilki? Yanzu ba wannan ba faɗa min komai ya tafi yadda ake so? Wani kukan Bilkisu ta fashe dashi tana fad'in " Wallahi Umma Ammar ya wuce tunaninki, kamar ma besan da zamana a gidan ba, ko magana baya min, kullum cikin haɗe min fuska yake" "Daina kuka, zaici ubansa zamuyi magana da uwarsa" Da toh ta amsa sannan ta kashe wayar. Number Fa'iza ta kira, sai data kusa tsinkewa ta dauka cikin Muryar bacci ta ce, "Hello! "Yawwa Fa'iza dan Allah turo min da number Zara'u" da ok ta amsa tana kashe wayar.. har 11 Bilkisu jiran Fa'iza take.. tana kokarin sake kiranta taga number ta Shigo. Da sauri ta kwashe ta zubasu a log dinta tana dialing.. bugu uku aka dauka.. sallama tayi, daga dayan bangaren aka amsa cikin cool voice. " Xarah ce? Cewar Bilki. "Da baki san wa kika kira ba? Taji an fada daga dayen bangaren. "Ke! Daga tambaya? Toh inaso na ja miki warning akan kiran mijina da kike wallahi ki fita a gonar mijina! This is the first and last time da zanga kiranki a wayar mijina if not u will surely regret it. Dariya aka fashe da ita kafin taji an ce " idan kin isa mace ki hanashi daukar wayar mana banza kawai! Daga haka aka kaste wayar. Cike da mamki Bilkisu ke kallon screen din wayarta. Number Fa'iza ta sake dialing, Bugu biyu ta dauka tana fad'in "Kinga number kuwa? "Eh na gani, kiranta nayi, hau Whatsapp na turo miki da wayar da mukayi" da toh Fa'iza ta amsa. Recording din da tayi ta tura mata, bayan minti kadan Fa'iza tayi replying da.. *_Ba ita bace ba, Muryar Zara'u bata kai hayaniyar haka ba, kuma bana tunanin ta iya masifa haka a yadda dai nake ganinta da kuma yadda naji mijinki na fadarta_* reply tayi da *_Toh yanzu ya za'ayi kenan?_* Fa'iza ce tayi mata reply da *_Dakin sani baki kirata ba, amma dai karki kara kiranta zanso zamuyi magana_* da ok Bilkisu tayi reply tana ajiye wayarta takaici duk ya isheta....