✨ *MATANA* ✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*Comments*
*Vote &*
*Share fisabilillah*: Assalamu alaikum wa rahmatullah.
Na ce bara in tunasar daku cewar na shirya aji tsaf don ci gaban mata iyayen gida,A wannan lokacin da sanyi yayiwa mata yawa a matsayin ki na mace yaya kike kula da kanki don kariya daga ɗaukar cutar sanyi ko da mai gida ya na ɗauke da shi?
: Shin kinada labarin sai kin isa ake tafiya dake? Aure nawa ke suke mutuwa saboda mazaje sun gaji da rashin damun isashiyar gamsuwa awurin matayensu?
Da yawan mata basuda labari game da kansu ma bare su nemi maganin matsalar su abu ɗaya suka sani sanyi ko dryness
Kina zaune kinashan maganin da ba shine matsalar taki ba
Kiyi ƙoƙarin shiga wannan ajin da naira dubu ɗaya jal, inda zaki mallaki ilimin da babu mai ƙwace miki shi har abada; A wannan ajin namu zamu baki ilimi akan sanin wace kalar macece ke acikin mata, menene matsalar ki a ɓangaren jikinki, yanda zaki kula da kanki a lokacin saduea da bayan saduwa, dabarun samun gamsuwa yayin jima'a musamman da ragon namiji.
Hanyoyi inganta tukunyar gidan ki, zamu kawo daɗaɗan abubuwan da zasj taimakawa mai gida idan kin mishi ya dawo da ƙarfinsa, ga koyar da kayan mata najinna faɗa daga er mutan sokoto 👍🏻👍🏻👍🏻
Duk fa wannan akan kuɗi naira dubu ɗaya kacal!
To me kike jira? Maza hanzarta biyan kuɗinki ta wannan asusun akawunt ɗin
Tallafawa tukunyar azuminki ta hanyar koyar dake ƙayatattun girke girke, shu'umar humrah da kuma kulacham ga turaren tsugono don zama tauraruwa👍🏻👍🏻👍🏻
Duk fa wannan akan kuɗi naira dubu ɗaya kacal!
To me kike jira? Maza hanzarta biyan kuɗinki ta wannan asusun akawunt ɗin Saiki tura shaidar biya ta nan👉🏻 07084161619.
Na gode.
2073065733
UBA BANK
SHA'AWA IBRAHIM*047*
Kuka Bilkisu ta fashe da shi tana kallon Ammar da ya runtsa idanuwan shi da alama ranshi a matuƙar ɓace yake. "Ƙarya suke min kawai tsabar sharri ne" "Wai bazaki karɓi laifin ki bane? Wace iriyar zuciya gareki? Cewar Maryam kamar zata dake ta. "Ta yaya zan karɓi laifin da ban aikata ba? Kawa... "Ya isa!" Cewar Ammar cikin tsawa. Da sauri ta haɗiye sauran maganarta tana hawaye, babban tashin hankalinta a yanzu shine Ammar ya ce ya saketa. Ga mamakin su gani su kayi Ammar ya wuce ya barsu ba tare da ya ƙara cewa uffan ba. "Wallahi sai kunyi nadama, a haka za kuyi ta zama ba aure" Cewar Bilkisu tana ɓallawa su Fatima harara. "Ai kuwa ƙaryarki ta sha ƙarya wallahi, ki zuba idanu kiga mijin da Maryam zata aura nima kuma ban fidda rai daga rahamar Allah ba, kece a ciki banza matar shige! Cewar Fatima tana hararar Bilkisu. Bilkisu bata iya cewa komai ba ta wuce ɗakinta. Dogon tsaki Maryam taja tana fad'in "kaɗan ma kika gani" Ammar ya kai at least minti 20 da shiga ɗaki kafin Zarah ta bi bayan shi. A zaune ta gan shi kamar ma daga wanka ya fito. Jin ta shigo kuma taki cewa komai ya saka shi ɗagowa ya kalleta. "What? Ya faɗa yana kallon cikin idanuwanta. " Tambayata kake what? Haka zaka barta without any action? Ajiyar zuciya ya sauke yana tashi tsaye ya riƙo hannunta cikin sanyin murya ya ce, " Zarah me kike so nayi? Ni babu abinda zan yi ma ta na barta da Allah" kwace hannunta tayi daga cikin na shi tana kallon shi ta ce, " Kasan irin wahalar dana sha? Ko da cutar Hydar aka barni da ita ai an cuceni, kawai kuma sai kace baxaka ɗauki mataki a kanta ba? "Zarah ki fahimceni ni bansan me zanyi mata ba amma Allah ya sani, shiyasa nace na barta da shi" "Ai wannan zaman cutuwa za muyi da ni da kai da ita, gaskiya bazan iya zama da mutum irin Bilkisu ba domin babu Allah a ranta! Kana gani har yanzu ba wai saduda tayi ba maimakon ta karɓi laifinta amma tana ƙaryata su Fatima! Toh wallahi baxan zauna da ita sai dai ka zaba ko ni ko ita! Daga haka ta fice ta barshi ta jin zafi a zuciyar shi. Fatima na ganin ta fito tabi bayanta zuwa kitchen tana fad'in "Kiyi haƙuri Aunty Zarah" "Ba komai Fatima" Ta faɗa tana kashe gas cooker. "Na ga kin kashe gas ɗin kuma shinkafar zata jiƙe fa" Fatima ta kuma faɗa tana kallon Zarah. "Kar ki damu" Daga haka Zarah ta fito tana nufar ɗakinta. Kullewa tayi dan kar Fatima ta biyo ta, sai data sha kuka sannan ta fara ɗibar kayanta a akwati, ita sam baxata iya cigaba da zama da muguwar mace irin Bilkisu ba tunda har bazai iya ɗaukar mataki ba. Wanko fuskarta tayi tana saka hijabi sannan ta janyo akwatin ta fito. Da sauri Fatima ta miƙe daga zaunen da ta ke ganin Zarah da akwati. "Aunty Zarah ina kuma zaki je? Ta faɗa tana ƙarasawa in da ta ke" "Zan je gida ne, ina ganin ina bukatar Hutu" Zarah ta bata amsa. "Bangane Hutu ba? Dama ana ɗaukar hutu ne a gidan aure? Me yayan yace miki ɗazu? "Karki damu ba daɗewa zanyi ba" cewar Zarah tana jan akwatin. Sunan Ammar ta shiga kira da ƙarfi. Maryam ce ta fara fitowa daga ɗaki tana kallon Zarah da har ta isa bakin ƙofa. "Lafiya? Meyasa Aunty Zarah zata tafi? Cewar Maryam tana nufar Zarah. Bilkisu ce ta fito kafin Ammar. Maryam kuwa riƙe Xarah tayi tana fad'in "Aunty Zarah me ya faru ina kuma zakije? Zarah bata ce komai ba ta fara ƙoƙarin raba hannunta dana Maryam. "Ta ce gida zata je, ba mamaki yaya ne yace ta tafi" Cewar Fatima tana kallon shi. "Bance ta je ko ina ba, me tayi min? Cewar Ammar yana kallon Fatima. " Toh meyasa zata tafi? Cewar Maryam tana ƙara riƙeta gam. "I guess, maybe Aunty Zarah taji haushi kan rashin matakin da yaya be ɗauka ba a kan Bilkisu, amma AUNTY Zarah in dai haka ne ba tafiya ya kamata kiyi ba, ki zauna ki nunawa matar shige matsayinta! Cewar Fatima tana nufar Zarah. Kai Zarah ta girgiza dan ita kaɗai yasan yadda take ji. Maryam kuwa sakin Zarah tayi ta nufi Bilkisu ta janyo ta da ƙarfi tana fad'in "Mayya! Kece zaki bar gidan nan wallahi! Tureta Bilkisu tayi ai kuwa Maryam ta faɗi tana ƙume kai a bango. "Innalillahi! Cewar Fatima tana nufar Maryam da sauri. "Bana son hauka, me yake damunku ne? Da me kuke so naji? Ke da ya kamata ki samo wa matsalar mafita amma kina cewa zaki tafi? Meyasa a ko da wani lokaci kike son bani ciwan kai ne Zarah? Nifa mijinki ne, duk abinda ya faru kuma sai kice zaki tafi gida? Ba fa haka ake zaman aure ba, ya kamata ki tsaya tsayin daka wajen ganin kin ceto rayuwar aurenki" ba tare da Zarah ta juyo ba ta ce, "Bazai yu na ceto rayuwar aure na ba ni kaɗai, na faɗa maka ba zan iya zama da ita ba, nan gaba bansan me zata aikata a gareni ba ko kuma yarana! Tunda ka zaɓi zama da ita shikenan" Daga haka ta fice. "Gaskiya nima bazan zauna ba! Cewar Fatima tana nufar ɗakinsu. Maryam na miƙewa tayi tana kallon Bilkisu ta ce, "Wallahi bakici bulus ba" Daga haka ta wuce ɗakinsu. Tsaf Fatima ta haɗa musu kayan su. Tana kallon Maryam ta ce, "Mu tafi gidan Hajiya Babba dan bazan zauna da Bilkisu ba" Gyaɗa kai Maryam tayi tana jan trolley ta fito dasu. A tsaye suka ga Ammar ya haɗe fuska kamar be taɓa dariya ba. "Yaya zamuje Hutu" Cewar Fatima tana gyara hijabinta. "Zaku koma ɗaki ko sai na saka jikinku yayi tsami? "Gaskiya yaya bazamu zauna da me bin boka ba" cewar Maryam tana turo baki. "Wallahi idan na buɗe idona baku koma ciki ba sai jikin ku yayi tsami" Maryam na shirin komawa Fatima ta janyota, tasan dai duk rintsi Ammar bazai daketa da tsohon ciki ba. "Na fara wasa daku ko? Ya faɗa yana kallon su. "Yaya abinda kayi fa baka kyauta ba, yanzu ka zaɓi zama da Bilki a kan Zarah? "Zaku ɓace min da gani ko sai na hukunta ku?! Ya faɗa cikin tsawa. Da sauri Maryam taja hannun Fatima suka koma daki tare da trolley. "Da kin barni dashi wallahi da sai na faɗa masa abinda yayi ba dae² bane" Cewar Fatima tana kallon Maryam. "Kyale shi, mu zauna amma in dai Bilkisu tana gidan nan zata ci ubanta wallahi sai ta gwamnace ita ta tafi ba Zarah ba, ni wallahi sai naji dama ba ƴar uwata ba ce" "Duk Aunty Sadiya ce ta lalata ta wallahi" cewar Fatima tana hura hanci... Ammar kuwa shirin aiki yayi ya fice daga gidan...