✨ *MATANA* ✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*Comments*
*Vote &*
*Share fisabilillah*: Assalamu alaikum wa rahmatullah.
Na ce bara in tunasar daku cewar na shirya aji tsaf don ci gaban mata iyayen gida,A wannan lokacin da sanyi yayiwa mata yawa a matsayin ki na mace yaya kike kula da kanki don kariya daga ɗaukar cutar sanyi ko da mai gida ya na ɗauke da shi?
: Shin kinada labarin sai kin isa ake tafiya dake? Aure nawa ke suke mutuwa saboda mazaje sun gaji da rashin damun isashiyar gamsuwa awurin matayensu?
Da yawan mata basuda labari game da kansu ma bare su nemi maganin matsalar su abu ɗaya suka sani sanyi ko dryness
Kina zaune kinashan maganin da ba shine matsalar taki ba
Kiyi ƙoƙarin shiga wannan ajin da naira dubu ɗaya jal, inda zaki mallaki ilimin da babu mai ƙwace miki shi har abada; A wannan ajin namu zamu baki ilimi akan sanin wace kalar macece ke acikin mata, menene matsalar ki a ɓangaren jikinki, yanda zaki kula da kanki a lokacin saduea da bayan saduwa, dabarun samun gamsuwa yayin jima'a musamman da ragon namiji.
Hanyoyi inganta tukunyar gidan ki, zamu kawo daɗaɗan abubuwan da zasj taimakawa mai gida idan kin mishi ya dawo da ƙarfinsa, ga koyar da kayan mata najinna faɗa daga er mutan sokoto 👍🏻👍🏻👍🏻
Duk fa wannan akan kuɗi naira dubu ɗaya kacal!
To me kike jira? Maza hanzarta biyan kuɗinki ta wannan asusun akawunt ɗin
Tallafawa tukunyar azuminki ta hanyar koyar dake ƙayatattun girke girke, shu'umar humrah da kuma kulacham ga turaren tsugono don zama tauraruwa👍🏻👍🏻👍🏻
Duk fa wannan akan kuɗi naira dubu ɗaya kacal!
To me kike jira? Maza hanzarta biyan kuɗinki ta wannan asusun akawunt ɗin Saiki tura shaidar biya ta nan👉🏻 07084161619.
Na gode.
2073065733
UBA BANK
SHA'AWA IBRAHIM*049*
Kuka take me tsuma zuciya, sosai zuciyarta take mata zafi da raɗaɗi, ita kaɗai tasan yadda take ji especially ma yau da yazo ɗaukar Raihan, lallai ta tafka babban kuskure da take biyewa Aunty Sadiya, tana kaunar mijinta, amma gashi yanzu babu sauran igiya tsakanin su, wace iriyar ƙaddara ce haka? Bata taɓa tunanin soyayyar Ammar tayi mata mugun kamu ba irin yau ɗin nan" a wannan yanayin Aunty Sadiya ta shigo ɗakin ta sameta. "Ke! Kukan me kike ne? Ta faɗa tana kallonta. Ɗagowa tayi tana kallon Aunty Sadiya ta ce, "Umma wallahi ina son Ammar dan Allah ki bashi haƙuri ya mai dani ɗakina" Wani wawan kallo tayi mata kafin ta ce, "Amma anyi banzar yarinya wallahi! Uwar me soyayyar ta shi ta tsinana miki? Kai ta girgiza tana jan majina ta ce, "Dan Allah Umma wallahi zan iya mutuwa idan be mayar dani ba" "ta yaya zai mayar dake bayan ya tsinke duka igiyoyin? Ke kika tashi hankalin ki! Ai Ammar babu yadda zai yi yace ya raba alaƙa dake! Ko babu Raihan ai akwai alakar jini dan haka babu yadda ya iya! Kuma duk daren daɗewa sai ya rabu da wannan bak'ar yarinyar! Yanzu dai ba wannan ba, ina ce gobe ne saukar Maryam? Ki shirya kije kuma ki basu haƙuri akan abubuwan da suka faru a baya... "Haba Umma ta yaya xanje abinda ba'a kawo min kati ba? "Ai kece shashasha! Ace wajen watanni 6 ko zuwa gidan baki sake yi ba, idan anyi magana kice kinyi zuciya, toh waye yake wahala yanzu? "Ni dai kawai kin cuceni, da kin barni da yanzu mijina bai sake n... Bata karasa ba Aunty Sadiya ta bige mata baki tana fad'in "Ni zaki cewa na cuceki saboda baki da hankali? Duk irin ƙoƙarin da nayi miki a kan auren nan? Tashi Bilkisu tayi tana hawaye ta ce, "Eh! Kece kika janyo komai ai! Kuma Allah idan be mayar dani gidan shi ba sai na kashe kaina!"kin daɗe baki kashe kanki ba dan Kutumar ubanki! Ni zaki faɗawa maganar banza saboda baki da hankali? Ficewa Bilki tayi ta barta tana ta ɓaɓatu. A chan gidan Ammar kuwa Zarah da Fatima na kitchen suna aikin kayan da za'a zuba a takeaway na sauka, sosai Zarah take karfin hali domin cikinta ya tsufa kuma tunda aka kusa saukar bata samu wani hutu ba saboda basu shiryawa saukar ba dan Ammar yace baza'ayi da ita a shekarar ba sai wata, saboda ta kuma dandakar karatun amma kuma admission ɗinta ta fito zuwa Oxford University ta samu shiyasa aka sunanta a ƴan sauka kuma tayi screening ta haye. Daga saloon Maryam ta dawo, a kitchen ɗin ta same su, meat pie ta dauka tana fad'in "Sannun ku, yanzu Aunty Hafsat ta ce zata kawo ragowar snacks ɗin, baki ga memon da tayi min ba me kyau wallahi, shi kuma Yaya Umar Calendar, jaka da key holder, yanzu ma idan yazo tace zamu je kasuwa a fanso Alqur'anan da za'a raba, kinga kawai sai ki bani kuɗin na siyo athkar ɗin ba sai an jira Yaya ba" "Eh ki duba cikin jakata tana kan gado" Cewar Xarah. Kafin Maryam ta bar kitchen ɗin Aunty Hafsat tazo gidan, tana goye da babynta a baya. Sai da suka gaisa da Zarah da kuma Fatima sannan suka wuce kasuwa ita da Maryam. Basu dawo ba sai bayan magariba. Har Ammar ya kawo ragowar kayan, an karbo memo, stickers, jaka ruwa da kuma lemuka. Sai 12na dare sannan suka kammala shirya komai. A ɗakin Ammar aka ajiye kayan. Wa she gari da safe tun kafin ta wuce filin sauka su Hajiya babba, aunty Khadija da matan baffa da yara suka zazzo... Cikin atamfar ankon zuwa filin sauka ta shirya sannan ta saka hijabi dogo milk har ƙasa. Turare Zarah ta fesa mata tana murmushi ta ce, "Muna alfahari da hafizar mu" Murmushin Maryam tayi tana kallonta ta ce, "Burin Mami shine na haddace Alqur'ani mai girma kuma gashi bata nan" Maryam ta ƙarashe maganar hawaye na taruwa a Idanunta. "Karki bata kwalliyarki, Mami na alfahari dake, ki cigaba da yi mata addu'a kinji ko? Kai ta gyada sannan suka fito daga ɗakin. "Allah ya ji kan Aishatu, burinta yau ya cika ɗaya daga cikin yaranta ta zama mahaddaciya, Allah yayi miki albarka Maryam' Cewar Aunty Khadija bayan fitowar Maryam. Ammar ne ya kai ta har makarantar. By 10 su Zarah sun shirya zuwa filin sauka. Suna zaune inda aka tanada dan zaman baki aka kira sunan Maryam dan tayi karatu.. Idanunta cike da kwalla ta taso, babu abinda take tunawa irin waccan saukar da tayi Mami na zaune daga gaba tana kallonta cikin annashuwa fuskarta ɗauke da tsantsar farinciki amma yau babu ita, jigon rayuwarta ta tafi... Kallon in da su Ammar suke tayi, gasu baffa, Ammar da kuma Umar, daga ɓangaren mata kuwa Aunty Khadija da matan Baffa sai Aunty Sadiya har da Bilkisu ga kuma Zarah, Fa'iza, Hafsat da Fatima. Goge hawayenta tayi tana jin zuciyarta tayi mata nauyi.. karɓar microphone ɗin tayi tun da fara karatun ta rufe idanunta kana jin muryarta zaka san kiris ya rage tayi kuka, izu daya tayi cikin suratul baqarah sannan ta mikawa yasaiyadin su mic ɗin. Kabbara akayi mata sannan aka bata lambar yabo a kan daliba me tarbiyya da kuma tsafta. Wata aka kira itama tayi nata karatun har kusan 12 sannan aka ɗanyi jawabai aka fara bada allo. Sai 1 sannan aka kammala komai, kuka kuwa Maryam ta sha shi da kyar suka rarrasheta, duk yawanci hotunan da akayi mata tana hawaye. Bayan sun koma gida, da kyar ta saita kanta, pictures akayi sosai sannan Zarah ta saka tayi wanka, ita da Fatima suka wuce gidan kwalliya. Sosai gidan ya kachame da jama'a, ko sau ɗaya Zarah bata kalli in da Aunty Sadiya da Bilki suke ba, har gwanda Fa'iza sun gai sa. Daɗinta daya da Ammar ya ɗauki hydar suka bar gidan. Amaryar sauka bata dawo ba sai 5pm saura, tayi wani kyau na musanman, ga makeup din beyi hauka ba everything so nice! Ma sha Allah sauka tayi daɗi, anci an sha an kuma sha pictures kuma ba'ayi faɗa ba kamar yadda Fatima tayi tunanin su Aunty Sadiya zasu janyo fadan. Bayan sallar Isha'i gidan ya ragu sai yan uwa kawai. Zarah na zauna a bedroom ɗinta bayan ta fito daga wanka kira ya shigo wayarta. Ganin sunan Dr Aminatu ya saka ta ɗaukar wayar cike da mamaki. "Hello Xarah! Taji ta faɗa cikin sanyin murya. "Na'am Dr ina yini? "Alhamdulillah, ya gida? Ya kuma Hydar? Da Lafiya lau Zarah ta amsa tana jiran taji me zata ce. " Ɗazu Mustapha ya sameni da maganar yana so muyi sorting everything out, Zarah Ina ganin kamar ana sashi dole ne, kece kuke tare kuma zance kin fini sanin abubuwan da suka faru lokacin yana Nigeria, ina ƙaunar shi amma bana so nayi auren da zan fara samun matsala tun da wuri, na kiraki ki faɗa min gaskiya Please" Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce, "Babu wanda ya tilasta shi, kawai dai nasan Ummi ta ce ya fito da matar aure kafin tayi fushi, tun da kika ga yazo yana neman hakan ki ƙara bashi wata damar" "Shikenan na gode bye" Da ok Zarah ta amsa tana ajiye wayar. Ta ɗauka sun gama magana da Mustapha amma meyasa zai mata haka bayan har Ammar ta faɗawa? Tabbas bata so tayi ruining ɗin farincikin Dr Aminatu, kawai zata bar maganar ne, maybe yaga Maryam ɗin bata mishi bane ko yana ganin tayi yarinya da yawa. Kaya marasa nauyi ta saka tana tashi da ƙyar, tun safe take jin ciwan baya ta ɗauka gajiya ce amma zuwa yanzu tasan labour ne. Fitowa tayi falo, duk suna zazzauna ana buɗe gifts ɗin da Maryam ta samu. Bata kai ga zama ba Ammar ya shigo riƙe da Raihan da kuma Hydar. "Ya dai? Cewar Ammar yana kallon Zarah ganin yadda take bata fuska ga hannunta a bayanta. Dukansu kallonta suka fara yi hakan yasa tayi saurin amsawa da "Ba komai" "Hajiya Hafsatu, thanks alot, kije mijinki na jira, kema Fa'iza bita zai kaiki gida kuma gobe ki dawo zaki tayasu aiki" da toh ta amsa. Ɗaukar ɗan Umar tayi ita kuma Hafsat ta shiga ta ɗauko hijabi sannan sukayi sallama. "Ita Bilki sai takwana idan an kammala aikin sai ta dawo gida yafi sauƙi, tunda nima chan ba wani aiki ne dani ba tunda Saude bata nan anje anji daɗin turai kasan abinda ba'a saba ba" Cewar Aunty Sadiya tana kallon Zarah. Ko uffan babu wanda yace mata. "Aunty Khadija ki gai da gida Allah ya huta gajiya" Cewar Zarah tana nufar ɗakinta. Bin bayanta Maryam tayi zuwa ɗaki, small box din hannunta ta mika mata tana fad'in "Ɗazu bayan magriba aka kawo min toh ina tsoron nunawa Yaya " karɓar box ɗin earrings din zarah tayi tana buɗewa... "Ai gold ne" cewar Zarah tana ƙara duba ɗan kunnen. "Eh, shiyasa ai nake tsoron nuna masa" Maryam ta kuma faɗa duk a tsorace. " Waye ya baki? Sai da Maryam ta zauna kafin ta ce, "Yayan ƙawata ce na islamiyya dama ya ce yana sona ni kuma nasan halin yaya zaice makaranta shiyasa naki cewa yazo wajen yaya" "Baki son Yaya Mustapha ɗin? Cewar Zarah tana kallonta. "Eh gaskiya shifa bai ce yana Sona ba" "Ok bakwa magana ta online? "Muna yi fa, shima ya turo min da kuɗi ta account har vds ɗina da pictures na sauka ya saka na tura masa amma dai ni ba sonshi nake ba yayi min tsufa" Dariya Zarah tayi tana fad'in " Baki san irinsu sun fi iya soyayya ba? Amma babu me miki dole, abinda kuma nake so ki sani, duk wanda yace yana kaunarki ki faɗawa yayanki ki daina ɓoyewa, idan dagaske yake yazo yayi magana da Ammar kinji ko? "Nasan yaya bazai bari ba, shiyasa nace ya bari na dawo daga karatu" "Toh shikenan, idan kinje ki dage kiyi abinda ya kaiki ba ruwanki da kowa Kinji ko? A hankali ta gyaɗa kanta alamar toh. "Yawwa haka nake so, Allah ya taimaka" Da Amin ta amsa tana ɗorawa da faɗin " zaki ajiye ɗan kunnen a wajenki? Kai Zarah ta girgiza tana fad'in "Ki saka abunki amma zan sanar da Ammar" da toh ta amsa sannan ta fita. Zarah na zaune har 12na dare sannan Ammar ya shigo. Zama yayi a kan kujerar yana fad'in "Bakya jin daɗi ne? "Ina ka tsaya? Ta faɗa tana kafeshi da idanu. "Ina gidan Umar yaran ma suna chan" "Ok, Amma goben zata tafi ko? Cike da rashin fahimta ya ce, "Wa kenan? "Bilkisu! Ta bashi amsa a gajarce. "In sha Allah, idan Fa'iza tazo zan mai dasu gida" bata ce dashi komai ba ta tashi ta wuce bedroom dan Bacci take ji. Fita yayi ya wuce ɗakin shi. Misalin karfe biyu na dare Zarah ta farka. Sam bacci yaƙi samuwa saboda ciwo, tun tana daurewa har taji abun yana fin ƙarfinta. Cikin ƙarfin hali ta fito daga ɗakinta ta kunna switch ɗin falo, ɗakin Ammar ta nufa tana knocking, kasa jure tsayuwar tayi hakan yasaka ta durƙushe tana kiran sunan shi. Ƙofar aka buɗe, Bilki ta gani cikin sleeping wears tana murza idanu. Tsananin ciwan da take ciki ya saka ta cigaba da kiran sunan Ammar. Kulle kofar Bilkisu tayi tana jan tsaki. Cikin tsananin ciwo take buga ƙofar har ƙarfinta ya ƙare. A nan wajen Zarah ta haifi babyn kukan yaro kawai Fatima ta dinga ji cikin bacci. Buɗe Idanunta tayi taga ba yaronta bane, jin kukan na ƙaruwa ya saka ta mike zaune tana tashin Maryam. "Baki ji kukan yaro ba? Maryam na murza idanu tace "Naji! Ko dai Aunty Zarah ce ta haihu? Ta faɗa da sauri tana mikewa, riƙeta Fatimah tayi da sauri tana fad'in "Muyi addu'a sai mu fita" Da toh ta amsa sannan suka fara addu'a. Bayan sun kammala suka fito suna sanɗa, ganin Zarah a kwance a kan tiles ya saka su ƙàrasawa da sauri. Ko placenta bata fito ba ga yaro sai tsandara kuka yake jini da fluid ko ina. Da ƙarfi Fatima ta fara bugawa Ammar kofa kamar zata balla ta. Bilkisu ce ta buɗe, cike da mamaki Fatima ta ce, "Me kike a nan? Dogon tsaki taja tana niyyar kulle kofar Maryam ta hankaɗata baya da ƙarfi tana shiga ɗakin. A kwance taga Ammar sai sharar bacci yake. Gado ta fara bubbugawa tana fad'in "Yaya! Ganin bai motsa ba ya saka ta fara jijjiga shi. Da kyar ya buɗe idanun shi da suka yi nauyi, dishi² yake ganinta kuma sama² yake jin abinda take fadi. Kamar zatayi kuka haka taji, fitowa tayi tana kallon su Fatima ta ce, "Yaƙi tashi fa" ficewa Bilkisu tayi ta koma tsohon ɗakinta tana tsaki. Kuka Maryam ta fara yi ganin Zarah ta daina motsi kuma sai bleeding take yi. Fatima ta rasa abin yi, ɗakin ta shiga itama duk ƙoƙarinta bai tashi ba. Wayarshi ta ɗauko ta shiga kiran Layin Umar, sai data kira sau biyar sannan ya ɗauka. Cikin tashin hankali ta ce, "Yaya umar ni ce, Xarah ce ta haihu tana ta zubar da jini kuma yaya yaƙi tashi daga bacci bansan me ya sameshi ba" "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ina zuwa gidan ku jira" Umar ya faɗa yana katse wayar. Ajiye wayar tayi ta cigaba da ƙoƙarin tashin Ammar da yayi kamar zai tashi sai ya ƙara komawa. A falo Umar da Hafsat suka tarar dasu zuwa lokacin har yaron ya daina kuka Zarah ma ta daina motsi. Kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun kawai Umar ya dinga mai-maita. Shi ya ɗau Zarah da ta zama unconscious Hafsat kuma ta ɗauko yaron kamar ma ya daina motsi. A gida suka bar su Maryam, da kyar aka karɓesu bayan sun isa asibiti. Cikin ƙanƙanin lokacin aka gyara baby da uwar sannan aka kai babyn nursery dan bai da lafiya Zarah kuma aka cigaba da dubata. Bayan an kaita word nurse ta fito tana kallon Umar da jikin shi duk jini. Numfashi ta sauke tana fad'in "Kana ina ka bar matarka cikin wannan yanayin? Kasan kuma tana da hawan jini? Kullum ana Educating ɗinku akan illar barin mace me tsohon ciki ta kwana ita kaɗai bakwa ji! Anyway ana bukatar blood transfusion Kuma as soon as possible bamu da blood group ɗinta a asibitin na saka an duba blood bank! Dan Allah ko a family ne a samo me irin jininta kafin zuwa gobe da rana saboda ta zubar da jini, gobe da safe sai kaje wajen cashier ka biya kuɗin gado da kuma drugs da likita zai rubuta! Kun auna babban Sa'a akwai doctor on call" Daga haka ta wuce ta barsu. "Ban san ne ya samu Ammar ba! Tun da nake dashi bai taba bacci irin haka ba! Cewar Umar yana kallon Hafsat. "Something is fishy, definitely akwai matsala" ajiyar zuciya ta sauke tana kallon shi ta dora da fadin " Ka tafi gida kayi wanka zan kula da ita" "Ok take care" "Yawwa take care of my sons" Gyada kai yayi sannan ya fita. Ward din da aka kwantar da Zarah ta shiga jikinta duk a sanyaye.