✨ *MATANA* ✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
*Comment*
*Vote* &
*Share* Fisabilillah*My WhatsApp group link, Dan Allah mata kawai*
https://chat.whatsapp.com/BrUNywiBsPxDJjxclwHfdU'''Assalamualaikum jama a ina sanar daku cewa wanna shaharariyar Mai makeup dinna Wanda akaf maiduguri babu kamarta wato AMMIS GLAM tana sanar daku cewa akwai ingantatun man gyara gashi ga Mai bukata zai iya tutubar number ta kamar haka..... 08030687711 muna bada sari a kowani state kike za a iya aika Miki kedai Yar uwa kiyi Kokarin mallakar naki kamin ya kare 500 ne kachal Amma idan sari zakiyi akwai discount sanna wanna man gyaran gashin Yana Kara tsowon gashi da laushi sanna Yana hana karyewar gashi sanna Yana sa gashinki yayi baki sosai sanna Yana maganin amotsrin gashi Yar uwa karki Bari a baki labarin don wanna man Basu da wani illa domin an hada sune da ingantataun kuma nagartatun mayuka masu aminci da karfi da basu da wata illa sai ma taimakawa da yakeyi karde ku Bari abaku labarin wanna Mai gashi na AMMIS HAIR OIL/CREAM'''
'''sanna pls don Allah idan kinsan ba siya ko sari zakiyi ba pls karkimin magana ko kikirani'''
*024*
Washe gari da misalin ƙarfe 10 na safe aka sallamesu, Ammar bai samu zuwa ba saboda yana theater, inna, Saude da kuma Zainab ne sukayi musu rakiya zuwa airport. Sai da suka shiga jirgi sannan su Inna suka bar airport ɗin... A kusa da Zarah ya zauna yana kallon Hydar ya ce, "Wannan katon hancin naki ne ba nawa ba" da sauri ta kalleshi ganin Hydar yake kallo ya saka tayi murmushi ta kalleshi kaɗan ta ce " Kaima kasan banda katon hanci, after all yafi na mummunar budurwarka" kallonta yayi na ƴan seconni kafin ya ce, "Kinyi min budurwa ne? "Aysha! Ta faɗa a gajarce. "Aysha! Aysha! Huhuhhh, sau nawa zan faɗa miki ƙawata ce, tare fa mukai school, she's brilliant shiyasa ma muka zamana class ɗaya da ita, why are you thinking alot? "Naji, Amma ai tana sonka! Don't you notice? Are you not aware of her attitude? She loves you alot! C'mon just agree! "But i love You! Ya fada yana kafeta da idanu ko ƙiftawa bayayi.. shuru tayi tana kallonsa, matsowa yayi kusa da ita yana riƙo hannunta cikin sanyi murya ya ce, "I love you Zarah! "Uhmmmm... Mustapha... Ummi! Ta faɗa tana jan Nunfashi.. "i don't care Zarah, please karki saka na zama lonely! "But i think we have closed this chapter already! Why are you behaving like this? Runtsa idanunsa yayi kaɗan.. iska ya furzar daga bakinsa yana gyara zamansa tare da furta kalmar "Ok I'm sorry! "It's ok" ta amsa tana satar kallon su Ummi dake lateral to them. Jinginar da kansa yayi jikin kujera yana jin zuciyarsa na wani irin abu da bazai iya misaltawa ba, tun farko daya san abinda zai faru tsakaninsa da Zarah kenan bazai yarda da maganar aurensu ba, amma ƙaddara ta riga fata! Aysha kuwa ta shaƙa dayawa dan duk abinda sukeyi tana kallonsu kasancewar ta saka ɓakin shade a idanunta bai zama lallai a gane inda take kalla ba. "Bacci nake ji" cewar Zarah tana kallonsa.. "ok kawoshi" ya faɗa yana karɓar Hydar.. lumshe idanu tayi, a hankali ya kwato da ita jikinsa.. feeling more comfortable tayi murmushi tare da faɗin "Thanks! "You're welcome your majesty! Buɗa idanunta tayi tana tashi daga jikinsa fuskarta dauke da wani expression ta ce, "Your majesty? Hhhh you made me laugh, like how? Bayan ko jinin saurata babu a jikina? Dariya yayi yana kallonta ya ce, "I have the right ae! Zan iya kiranki da abinda yafi hakan ma, my little sis! Murmushi tayi tana komawa ta kwanta a jikinsa.. Lokaci² Ummi na kallonsu, ji take dama duk abinda ya faru a baya be faru ba, tabbas sunyi mugun dacewa da junansu! Gani take dan Mustapha akayi Zarah! But bata san me Destiny ya tanadar ba! She will wait and see, indai da rai da lafiya, tana fatan ya zamana Alkhairi.. .. Bayan sun sauka, driver ne yazo ya daukesu zuwa gida.... Ɗakin Farida na gidan aka bawa Aysha, ita kuma Zarah dakinta takoma, tas an gyare ko ina dan yanzu ummi tana da maids kuma ta sanar dasu su gyara suyi girki kafin ta dawo.. ko ina tas yake.. Ruwan wanka ta haɗawa Zarah dai dai misali, dan a asibiti an hana ayi mata wankan jego.... "Toh taso kiyi wanka" Da toh ta amsa tana tashi ta shiga toilet, ta daɗe a ciki sannan ta fito tana sanye da bathrobe pinkish me laushi.... Turo kofar ɗakin akayi, Aysha ce ta shigo riƙe da Hydar dake tsandara kuka, haɗe fuska Zarah tayi tana ƙarasawa ta karbi yaronta ba tare da tace wa Aysha komai ba.. "Dakinki yayi kyau! Ta faɗa dan son jan magana.. "Nagode! Cewar Zarah tana jijjiga yaronta.. "Kafin Mustapha ya sakeki kin tare ne a gidansa ko anan kuka cigaba da zama? "Who the heck are you to asked me such kind of question? Are you mad? Ko dan Kinga Mustapha ya baki duk wani privacy da zaki dinga masa surutu ba kwaɓa shine zakiyi tunanin trying such sh***t dani? "I'm sorry, i just asked! Kuma ban tambaya da wani manufa ba, kawai dai naga kamar abun ya faru da wuri ne! It seems that akwai babban dalilin daya saka Mustapha sakinki, I like you Zarah! Bansan meyasa bakya Sona ba! Ki zama free minded dani, kuma I'm not befriending your ex husband kamar yadda kike tunani, I'm just his school friend! Zarah bazan taba cutarki ba, i like you, ke da Mustapha kun dace be kamata ace kun bari petty² things sun shiga tsakaninku har ta kai ga saki ba, Please Zarah you should seat and talk to your husband hun? Ki ƙoƙarta, na barki lafiya" daga haka ta fita tana sakin wani evil smile.. Dogon tsaki Zarah ta ja tana zama a gefan gado tare da faɗin "Yenyenyenyenyen, shegia kamar ta Allah! I know my profession very well! Psychology da sociology ɗin da nayi a school ba'a banza ba! Nonsense! But zan buga wasan dake sakarya kawai! Daga haka ta kunce robe din jikin rigarta ta fara bawa Hydar nono.... Ummi ce ta shigo hannunta riƙe da tray din abinci.. kulle ƙofar ɗakin tayi tana ƙarasowa inda Zarah take, " ki gama bashi abincin kema ga naki, kici sai ki kwanta, insha Allah jibi za'ayi taron suna gobe me kunshi zata zo, zaki daure Mustapha ya kaiki saloon a gyara miki gashi kinji ko? "Toh Ummi" ta faɗa tana sunkuyar da kanta. "Yawwa, kammala bashi sai na tafi dashi nayi masa wanka, tun safe yau bega ruwa ba".. bayan Zarah ta gama shayar da Hydar ta bawa Ummi shi, sannan ta fara cin delicious food din da ummi ta kawo mata. Kaɗan ta rage, ta nufi toilet ta wanke hannunta, wardrobe ta buɗe, kayanta ta gani dayawa a ciki, riga mara nauyi ta ɗauko tare da dankwali.. turare kaɗan ta fesa sannan ta fito daga daki tare da kayan data ci abinci. Kitchen ta kai sannan ta nufi dakin Ummi... A zaune ta tarar da Aysha riƙe da yaronta tana saka masa hula.. Daga toilet ummi ta fito tana fad'in " Yanzu nake shirin zuwa dakinki! Kije ga abincin Mustapha chan a dining ki kai masa! "Ai na kai tun ɗazu" Aysha ta faɗa tana yiwa Ummi murmushi.. "Ok by now zai iya gamawa, Zarah jeki dauko me aiki ta samu ta wanke saboda da yamma take tafiya gida" "Ba komai ta huta bari naje na dauko! Aysha ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa. "No! Karki wani damu! Ai naji sauki kuma yawan motsa jiki ai yana da kyau! Daga haka Zarah ta fita ta barta da murmushin dole a fuska... A zaune ta tarar dashi akan kujera yana kallo ko abincin be taɓa ba.. "Ya baka ci komai ba? Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta ba tare da yace komai ba.. kai ta girgiza tana tsugunnawa tayi serving dinsa... "Ungo! Karbar plate din yayi yana kallon abincin ya ce, " Ke ummi tace ki kawo abincin ko Aysha? "Shishigi zai barta ta tsaya iya matsayinta ne! Cewar Zarah tana wani buda hanci.. "Ok ta barki ki kula da babban yayanki ko? "Mtsww, nifa wallahi ta fara kaini bango! Dan Allah ka maida ita gidansu! "A gabanki ai nayi mata maganar, kuma bazaiyu naje America na ƙara dawowa ba, kiyi haƙuri" "Ok amma kayi mata magana! Ba ruwanta da personal issues dinmu! Kuma ban yarda ka faɗa mata komai ba! "Meyasa zan faɗa mata? Ban taɓa sanar da ita komai ba! Maganar mutuwar auren mu nasan bazai wuce a bakin Zainab ta sani ba! Meyasa zan fadawa wata sirrinmu? This is our secret! Babu wanda ya kamata ya sani! Su Ummi ma da suka sani dan ya zama dole ne! "Shikenan toh" Ta fada tana tashi tsaye... "Gobe Ummi ta ce zan kaiki saloon" "Eh ta faɗa min"Cewar Zarah tana kallonsa. "Good! So you should be ready kar nazo ina jiranki" "Ok, zanje na kwanta" "Oh na dauka zaki zauna muyi hira" kai ta girgiza sannan ta ce, "Ummi zata ga na dade" "Amma ai tasan inda kike, after all kina tare da big brother! Murmushi tayi tana zama kusa dashi... MBC max ya kai musu, luckily ana Film din frozen 2.. nutsuwa tayi dan dama tana kaunar Film din... Ganin yadda ya nutsu ya saka shi ajiye remote din hannunsa yana murmushi ya ce, "Shikenan idan Hydar ya girma ke dashi sai ku zauna kuyi ta kallon cartoon! Murmushi tayi ta ɗan kalleshi ta ce " Film ɗinfa yana da kyau" daga haka ta cigaba da kallonta.. idanu ya zuba mata ganin yadda ta ke kallo kamar ace kyat ta zura a guje.... "Is more comfortable right? Cewarsa yana kallonta.. gyara kanta tayi a kafadarsa tana sauke ajiyar zuciya. Tallah aka tafi hakan ya bata damar tafiya duniya tunani... "She wonder how he's coping with himself now! Did they both take the right decision? Anya kuwa bata zalunci Mustapha dayawa ba? Abinda zata sakawa su Ummi dashi kenan? Amma kuma ya xatayi idan ba hakan ba? Me zata aikata ta tseratar da kanta daga azabar Allah? Ta yaya zata cigaba da rayuwa da mijinta bayan zuciyarta tana tare da wani chan daban! Toh tasan tayi taking right decision, why is she feeling guilty? Meyasa take ganin kamar bata kyauta! Meyasa take yawan tunanin abubuwan nan a ƴan kwanakin nan! Sabon step din da zata taka arayuwarta ta shirya masa ne? Tunda abinnan yake faruwa ta taɓa neman zabin Ubangijin ta? Kullum bata da buri sai na mallakar Ammar! Ammar alkhairi ne a gareta? "Of course yes! Saboda idan ba alkhairi bane Mustapha bazai saketa ba! Ta bawa kanta amsa.. ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe idanunta.... Mustapha ya dauka bacci tayi, gyara mata kwanciyarta yayi yana murza hannunta cikin soyayyarta.... Turo ƙofar dakin nashi akayi.. Ummi ce ta shigo, kallo ɗaya tayi wa yanayin da suke ta ɗauke kai tana haɗe fuska ta ce " Nasan kai ka tilasta mata ta zauna a dakin nan! Zarah kuwa kirjinta ne ya buga tana kara pretending as bacci fa take... "Bana son irin wannan keɓewar da kukeyi kaji ko? Yanzu Zarah ba matarka bace! Abu kaɗan zai iya jan ra'ayinka gareta! Karku jawo min abin kunya dan Allah! Duk da cewa zanfi kowa farinciki idan kuka gyara tsakaninku aka maida aurenku amma dai daga yau kar na sake gani ka riketa haka kaji ko? Calmly ya ce "Babu abinda zai faru Ummi! Nasan matsayin Zarah awajena Ummi! Insha Allah babu abinda zai faru! "Naji dai amma ka kula kuma kar na sake gani! Ka gama cin abincin ne? "Eh" Ya amsa yana kallonta. Kwashe kayan tayi ta fita.. Zarah najin fitarta ta buɗe idanunta tana ƙoƙarin tashi daga jikinsa.. riketa yayi yana kallon fuskarta ya ce, "Ina zakije? "Ɗakina zan koma" ta fada tana ƙoƙarin tashi.. "baki gama kallon Film ɗin ba" "Meyasa ka fiya son magana? "Saboda ina jin daɗin hakan indai ina tare da ke" "Uhmm, naji toh sakeni" "idan naƙi fa? "Zan maka ihu incewa Ummi ka rikeni! "Ok go ahead! Buɗa baki tayi kamar zatayi ihu sai kuma ta fashe da dariya tana fad'in " Har kaji tsoro! Dariya shima yayi yana kallon ta ya ce, " Nasan zaki aikata ai, matar da zata zauna kallon cartoon as if her life depends on it, ai abinda yafi haka ma zaki aikata! "Oh yanzu dai tsokanata kake? "Yes! Ai gaskiya na faɗa! Faɗa min yaushe zaki girma? You just gave birth! Bllnt kice sai kin haihu blablabla... "Nifa na girma kuma kaima ai ka kalla kuma kaji dadin Film din" "Not bad! Amma ai ba kamar ke ba, now tell me saura shekara nawa kuyi graduation? "Munyi shekara daya da rabi saura daya da rabi" "Ok, idan kinaso zan iya nema miki aiki a America idan kin karbi licensed dinki" "Are you serious? "Uhmm" ya faɗa yana shafa gefan kumatunta. " Ok, Allah ya kaimu lokacin" Shuru yayi dan totally he's lost! Ya kafeta da idanu murmushi kwance akan fuskarsa, "uhmm, zan tafi! Zarah ta fada tana riƙe hannunsa.. be kulata ba itama bata kara kokarin sauka ba, this days she feels much better when he's around! And more comfortable when they are together.. ajiyar zuciya ta sauke tana alaƙanta hakan da sabon bond ɗin da suka fara sharing na matsayin parents... Gyaran murya suka ji, da sauri ta kalli kofar dakin dan tayi zaton Ummi ce.. ganin Aysha a tsaye ya sakata tsuke fuska tana fad'in " Ai Ummi ta fita da kayan! "Ba wanan ya kawo ni ba Mrs romance! Ummi tace kije! Daga haka ta fita tana matse wayar dake hannunta zuciyarta na zafi... Sakinta yayi ta sakko daga kan sofa tana gyara rigar jikinta ta fita.. a falo ta tarar da Ummi tana rike da Hydar... "Ummi gani" "zo nan! Cewar ummi tana nuna mata kusa da ita. A hankali ta zauna tana sunkuyar da kanta. "Yawwa, ga ɗanki! Kuka kamar wanda ake mintsini? Karbar shi tayi tana dan murmushi.. "Sannan kuma this should be the first and last da zan kara ganinki jikin Mustapha kinji ko? Idan kuna so a mayar muku da aurenku ba abune mai wahala ba! Amma bana son wannan shashancin kinji ko? 'toh" ta amsa tana yin ƙasa da kanta. "Yawwa! Daga haka Ummi ta maida hankalinta kan TV... "Ummi, wayata tana chan Kano idan Inna zasu zo jibi ki sanar da ita ta kawo min" cewar Zarah kanta a ƙasa. "Shikenan zan kirata, kije daki ki huta ko kinfi son zaman nan? Kai ta girgiza tana miƙewa tsaye ta nufi hanyar dakinta....