✨ *MATANA* ✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
*Comment*
*Vote* &
*Share* Fisabilillah*My WhatsApp group link, Dan Allah mata kawai*
https://chat.whatsapp.com/BrUNywiBsPxDJjxclwHfdU'''Assalamualaikum jama a ina sanar daku cewa wanna shaharariyar Mai makeup dinna Wanda akaf maiduguri babu kamarta wato AMMIS GLAM tana sanar daku cewa akwai ingantatun man gyara gashi ga Mai bukata zai iya tutubar number ta kamar haka..... 08030687711 muna bada sari a kowani state kike za a iya aika Miki kedai Yar uwa kiyi Kokarin mallakar naki kamin ya kare 500 ne kachal Amma idan sari zakiyi akwai discount sanna wanna man gyaran gashin Yana Kara tsowon gashi da laushi sanna Yana hana karyewar gashi sanna Yana sa gashinki yayi baki sosai sanna Yana maganin amotsrin gashi Yar uwa karki Bari a baki labarin don wanna man Basu da wani illa domin an hada sune da ingantataun kuma nagartatun mayuka masu aminci da karfi da basu da wata illa sai ma taimakawa da yakeyi karde ku Bari abaku labarin wanna Mai gashi na AMMIS HAIR OIL/CREAM'''
'''sanna pls don Allah idan kinsan ba siya ko sari zakiyi ba pls karkimin magana ko kikirani'''
*028*
Tun daga wannan ranar Mustapha bai ƙara saka Aysha a idanunsa ba, hakan kuma bai dameshi ba dan a ganin sa hakan shi yafi masa alkhairi. A ɓangaren Zarah kuwa shirin biki kawai akeyi saboda lokaci ya matso kusa sosai. Tun asubah ita da Saude suka tashi dan yi abinda za'a sallami masu kawo lefe. Karfe 10 na safe suka kammala ayyukan su sannan suka kai gidan Baffa, by 12pm ƙannen mahaifin Ammar suka kawo lefan Zarah, an musu tukwici dai-dai misali, basu wani ɓata lokaci ba suka tafi bayan an tsayar da lokaci nan da two weeks. Sai magariba sannan su Inna suka dawo gida. Wanka kawai Zarah tayi tana kwanciya a kan gado dan ta gaji. Saude na zaune tana danna waya mijinta ya kirata, kallon Zarah tayi ta ce, "Ni dai na wuce nasan yazo" "Toh ki gaida gida, Allah ya huce gajiya" Da toh ta amsa sannan ta fita. Gajeran saƙo me ɗauke da kalamai masu nuna godiya da jin daɗi Zarah ta turawa Ammar sannan tayi silencing wayarta tana lumshe idanunta.
A chan gidansu Ammar kuwa, Aunty Sadiya ce zaune a falo tana faman cika da batsewa, tun bayan sallar la"asar take gidan tana jiran shigowar Ammar amma shuru kamar an aiki bawa garinsu. Mami ce ta shigo falon tana kallonta ta ce, "Yasan abinda ya aikata fa, bazaki ganshi ba sai wajen 12am ko 1am na dare, da haƙura kikayi kika tafi gida" kamar jira take aikuwa ta miƙe tsaye tana fad'in " Ai wallahi bana ganin laifin Ammar kamar yadda nake ganin naki Yaya! Ya za'ayi ki haifi ɗa a cikin ki ya ga-gareki? Nawa Ammar din yake? Har yau fa bai cika 30yrs ba! Tun farko ke kika aminta da auren nan ai! Ƴar gidan uban waye ita da zai kai mata akwati 8 har da sarƙar gwal guda uku saboda hauka akeyi? Kuma dan tsabar gulma da iya shege a cikin gidana a ka ajiye lefan ban sani ba? Lokacin daya auri bilkisu da kyar da sidin goshi ya saka gwal daya! Dan wulakanci shine zai auri wata yar talakawa ya saka gwal har uku? Ko kayan faɗar kishiya babu! Haka zai bar Bilkin? "Toh ai naga babu aure tsakaninsu, Kinga maganar kayan faɗar kishiya bai taso ba! Cewar Mami cikin sanyin murya. "Ba wani nan! Idan haka ne itama ya hado mata nata lefan mana! Ai dukansu zaurawa ne, gwanda ita bilkin gidan mijinta zata koma, amma ita Zara'u ai sabon aure ne ko budurwa be zama lallai ta samu irin kayan da ta samu ba! "Shikenan kiyi hakuri zan masa magana itama bilkisu yayi mata" "Yawwa! Sannan idan za'a daura aure sai an fara daura na Bilkisu tukun kafin a daura na Zara'un idan ba haka Allah Yaya babu ni babu ke tunda tozarta ni kike son yi! "Allah ya baki haƙuri Sadiya, ki dinga kokarin tausa-sa zuciyarki kinji ko? Cikin bala'i Aunty Sadiya ta ce, "Ai ke tausa-sa zuciyar taki da kike yi ne ya saka komai ya ƙara kwaɓewa! Kin bani kunya ma da kika bari har auren nan zai tabbata" Murmushi Mami tayi tana kallon ƙanwarta ta ce, "Ai idan bamu yarda da abinda yake so ba shima bazai taɓa yarda da abinda muke so ba Sadiya! Ba Zara'u yake so ba? Gashi nan da ita ai" Ita dai Aunty Sadiya bata ce komai ba Zuciyarta sai tafasa takeyi. Ƙarfe 10 da ƴan mintuna ta wuce gida dan Ammar bai da niyyar dawowa.