✨ *MATANA* ✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*Comments*
*Vote &*
*Share fisabilillah**036*
" Bai kamata a ce ka bar matarka a gidan nan ba dan bata da lafiya, ita ɗin responsibility ɗinka ce, ga Raihan Sadiya ta ce wajenta zai zauna, nifa bana son wannan raba-raban kan family ɗin! Ka je ka ɗauko ɗanka sannan ka ɗauki matarka ku wuce ko da gobe ne kaji ko? "Waye zai kula da ita a chan? Kin san fa ba wani zama nake ba, kuma basa shiri da Zarah, ita kanta Zaran ba lafiya ce ta isheta ba" Cewar Ammar. "Toh ga Maryam nan ai, sai ta koma chan da zama kafin taji sauƙi ko? Ya kamata ka dinga yi wa kanka faɗa Ammar! Aurenfa Bilkisu kake yi! Baka bata haƙoƙinta da suka kamata, ka share yarinya ka mayar da ita ba komai ba? Yanzu idan wani ya aurar maka ƴa ya mayar da ita kamar yadda ka mayar da Bilkisu ya zakaji a ranka? Ka dinga sara kana duban bakin gatari mana Ammaru! Duka² rayuwar nan nawa take? Kamar Ammar zaiyi kuka ya kalli Maminsa ya ce, "Wallahi Mami bana son yarinyar nan! Haƙuri kawai nake ina zama da ita! Ina yin komai ne saboda ke, if not da tuni na sawwaƙe mata itama ta huta! Nasan Zarah da Bilkisu duk MATANA ne amma there is a huge differences btw the two of them! Ko da ace nayi kokarin kyautatawa Bilkisu toh tabbas baxan iya haɗata da Zarah ba! Zarah zaɓina ce! Zaɓin zuciyata! Wadda nake ƙauna kuma na gani da kaina ya yaba! Amma Bilkisu matar shige ce! Zabin Aunty Sadiya dan bazan ce zaɓinki ba! Kawai ki dinga min addu'a Mami" Ajiyar zuciya Mami ta sauke tana kallonsa ba tare da tace komai ba. "Ni na tafi" "Allah ya kiyaye" Mami ta faɗa tana kallon bayansa har ya fice. Har lokacin suna zaune a falo, kallonta yayi ya ce, " Allah ya ƙara sauki" Bata amsa ba shima be damu da amsawarta ba ya fice abun shi.
Zarah na zaune a falonta tana latsa wayarta, tana sanye cikin simple dress ta kanti, turo ƙofar falonta yayi bakinsa ɗauke da sallama. Amsawa tayi ba tare da ta kalli direction ɗin da yake ba. Kayan hannunsa ya ajiye a kusa da ita yana nufar fridge ya ɗauko ruwa sannan ya dawo kusa da ita ya zauna. "Ba sannu da zuwa? Ya faɗa yana kallonta. " Ai ba wani wajen kaje ba shi yasa" Cewar Zarah still bata kalleshi ba. Bai ce komai ba ya sha ruwa ya ajiye ragowar.. relaxing yayi a kujera sannan ya kuma faɗin "Ga ankon bikin Fatima, zan turo miki da kalar ɗinkin da zakiyi" "Wai har bikin ya matso ne? Ta faɗa tana maida dubanta gare shi. "Eh saura wata daya ina jin dai" Gyaɗa kai tayi a hankali ta ce, "Allah y basu zaman lafiya, na gode Allah ya ƙara buɗi" Da Amin Ammar ya amsa yana matsar da kayan ya dawo kusa da ita.. idanun shi a kanta ya ce, "Kiyi haƙuri" "Me kayi min? Xarah ta faɗa cike da rashin fahimtarsa. "Naga kina fushi ne, Ni kaina bansan me nayi ba, Please stop this attitude of yours please Zarah, wai ina tsohuwar Zarah ta ne? So lovely and romantic? Inason tsohuwar Zarata ta dawo wadda bata jin kunyar faɗa min abinda ke ranta, wadda bata fushi, wadda take bani nutsuwa a ko yaushe, Please old Zarah ki dawo" ya ƙarashe maganar yana ɗan matse hannunta dake cikin nashi... "Wannan ba ita ce iriyar rayuwar auren da nake imagine zamuyi ba Ammar! Komai naga kamar ya sauya! I find nothing but sorrow instead of happiness, Ni kaina bansan yadda zan gayyato wa kaina farincikin ba! Banda kwanakin baya muna America babu ranar dana tsinci kaina cikin farin ciki sosai tun ranar da mukayi aure" Xarah ta faɗa tana kallonsa. "Kece baki kwantar da hankalin ki ba Xarah! Indai kika saki jikinki, hankalinki ya kwanta in sha Allah zakiga sauyi, ba ruwanki da kowa, domin ni kike zaune a cikin gidan nan so make your self and also your husband happy, Zarah... Ya faɗa yana riƙo hannunta sosai.. bata iya amsawa ba sai idanu kawai data zuba masa.. "kina so na kuma Nima ina kaunarki, bazan taɓa barinki ba in sha Allah, sai dai mutuwa, ragowar rayuwar data rage mana let's try and enjoy it Zarah, mufa ma'aurata ne, lokacin da bamu da aure mu kan farantawa junan mu rai ballantana yanzu da ibada muke yi, let's change our marriage life together please! Kai ta gyaɗa masa a hankali, "Good! Ya faɗa yana sakin hannunta. Ajiyar zuciya ta sauke tana komawa jikin kujera a hankali. "When zamu je gidan Umar? Ya fada idanunsa a kan TV "Kaga dai next week zamu koma school, so a wannan week ɗin zanje duk inda zanje, next week Kuma mkrnt" "hakane, gobe tunda bani da aiki zan fara kai ki gida ki duba Bilkisu, ko bazaki ba? "Zanje" Ta faɗa a hankali. "Good, sai muje wajen Saude kiga ɗanku" murmushi tayi tana fad'in " Na ganshi a waya ae, yaron Masha Allah" "Hakane Ya ɗauko farin mamansa, soon kema in sha Allah, wai ya maganar magani na ne? "Toh da shekaruna zan siya maka? Ta fada tana ɗauke kanta daga kallonsa. "Madam ke kuma haka akeyi? Ai sai kice na bada kuɗi, anyway price? "Sai na tambaya tukunna" ta faɗa tana ƙoƙarin tashi. Dawo da ita yayi yana kallon cikin idanunta murmushi ya ɗanyi yana fad'in "Shikenan kuma bazaki zauna muyi hira ba? Bata ce uffan ta sai gyara zamanta da tayi tana zancen zuci. Ammar kuwa tsayawa yayi kawai yana kallonta, sosai Zarah ta yi nisa cikin saƙe²n da zuciyarta take mata, me kyau da akasin hakan. Kiran sallar magrib ne ya saka Ammar tashi yana fad'in " Zan wuce masallaci, kema tashi kiyi sallah" Sam bata ji me yace da ita ba, kafaɗarta ya taɓa hakan yasa ta kalleshi alamar menene? "Sallah! Ya faɗa da ɗan karfi. Numfashi ta fitar da ɗan karfi sannan ta tashi ta shiga banɗaki. Shima ficewa yayi abunsa. Bayan ta idar da sallah kitchen ta shiga ta ɗora girki, ɗaki ta dawo ta shiga wanka dan rabonta da yin wanka tun na safe da tayi. Harta fito ta shirya Ammar be dawo ba, kitchen ta koma ta haɗa abincin sannan ta zauna a kan stool ta fara latsa waya. Tsoro Ammar ɗin yaso bata bayan ya shigo ganin gaba daya hankalinta yana kan wayarta.. ɓata rai tayi tana kallonsa ta ce " Yanzu dana yarda wayata fa? " Sai na baki tawa, me kike dafawa ne ƙhamshi tun daga compound? Maimakon ta amsa ta jefo masa tambayar "a ina ka tsaya? " Na tsaya anyi Isha'i ne fa, babu inda naje" Ya ƙarashe maganar yana buda hannayensa alamar he's innocent. "Ok" daga haka ta cigaba da latsa wayar ta. Kwace wayar yayi yana duba abinda take yi na ƴan seconni sai kuma ya taɓa baki ya ce " Ashe dai kina chatting sosai har haka? Na ɗauka baki da abinda yafi miki mahimmanci irin handout" "Ai komai da lokacinsa, bani wayata magana fa nake mai mahimmanci" "Ok duk mahimmancin maganar ta fi ni? "A'a, amma... "Amma me? Tunda kin bani amsata shikenan, chat ya ƙare a yau dai" ya ƙarashe maganar yana kashe mata data. Kamar zatayi kuka ta ce, " Kaɗan zanyi DR Aminatu ce kuma kaga karatu muke" "Karatu? Banga alama ba kam, banda emojies ɗin dariya babu abinda na gani a chat ɗin, yanzu dai duba mana abinci karya ƙone" Bata mu sa ba ta miƙe ta nufi tukunyar girkinta, rage wuta tayi tana fad'in "Gobe kafin mu tafi inaso zanyi stew kuma ba kayan miya" "Ok, in sha Allah da safe zan aiki Rabi'u yaje ya siyo" Kai ta gyaɗa masa tana karɓe wayarta dake hannunsa. "Bakya jin magana ashe? "Nifa ba chat zan yi ba ba, game zanyi" daga haka ta shiga game, karɓe wayar yayi yaga dagaske game din take yi. Fita yayi daga game ɗin yana matsowa inda take tare da faɗin " Lokacina ne yanzun babu game or chat infact babu rike waya kinji ko? Bata ce komai ba sai Gyaɗa kai kamar wata ƙadangaruwa. "Good, i love You" nan ma bata ce komai ba. A haka suka karanci zaman kitchen ɗin har girkin ya dahu ta zubo musu, tare suka ci a main falo na gidan sannan ta kai kayan kitchen da niyyar gobe ta wanke dan yanzu dare yayi. Already dama ta shirya cikin kayan baccinta zani kawai ta ɗora sannan tayi Isha'i. Ammar kuwa har ya kwanta ya fara danna waya. Bayan ta idar itama kan gadon ta hau tana fad'in " Ka dai ji tsoran Allah" da sauri ya kalleta ya ce, "Me nayi? "Ka hanani danna waya kai gashi nan ai danna wayar kake" Dariya yayi me sauti yana fad'in "PT ɗina ne yake son zuwa wajena dama yana zuwa checkup so kinga ai bazanƙi attending ɗinsa ba ko? "Toh ai baka zuwa aiki, hutunka bai kare ba" "Yes amma ina zuwa call, so Shiyasa na tsaya nayi masa bayani, is better yaje wajen DR Sadeeq" "Toh naji dai ka ajiye waya" "an gama ranki ya daɗe" daga haka Ammar ya saka wayarsa a charji ya na gyara kwanciyarsa. A jikinsa Zarah ta kwanta tana sauke numfashi a hankali, bata daɗe ba bacci ya ɗauketa haka shima Ammaru.