✨ *MATANA* ✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
*Comment*
*Vote* &
*Share* Fisabilillah*My WhatsApp group link, Dan Allah mata kawai*
https://chat.whatsapp.com/BrUNywiBsPxDJjxclwHfdU'''Assalamualaikum jama a ina sanar daku cewa wanna shaharariyar Mai makeup dinna Wanda akaf maiduguri babu kamarta wato AMMIS GLAM tana sanar daku cewa akwai ingantatun man gyara gashi ga Mai bukata zai iya tutubar number ta kamar haka..... 08030687711 muna bada sari a kowani state kike za a iya aika Miki kedai Yar uwa kiyi Kokarin mallakar naki kamin ya kare 500 ne kachal Amma idan sari zakiyi akwai discount sanna wanna man gyaran gashin Yana Kara tsowon gashi da laushi sanna Yana hana karyewar gashi sanna Yana sa gashinki yayi baki sosai sanna Yana maganin amotsrin gashi Yar uwa karki Bari a baki labarin don wanna man Basu da wani illa domin an hada sune da ingantataun kuma nagartatun mayuka masu aminci da karfi da basu da wata illa sai ma taimakawa da yakeyi karde ku Bari abaku labarin wanna Mai gashi na AMMIS HAIR OIL/CREAM'''
'''sanna pls don Allah idan kinsan ba siya ko sari zakiyi ba pls karkimin magana ko kikirani'''
*025*
Zarah na zaune riƙe da yaronta Innarta a kusa da ita tana dama mata furar da Daddy ya siyo, wayar Zarah ce ta fara ruri, ɗan satar kallon Inna tayi taga hankalinta baya kanta.. ɗaukar wayar tayi tana ƙoƙarin tashi Inna ta ce, "Da kinyi zamanki nasan bazai wuce Ammaru ba" "zan kiraka anjima" cewar Zarah tana disconnecting ɗin kiran. Furar Inna ta miƙa mata tana fad'in " Ki sake tunani Zarah! Mustapha sai yafi kowa sanin darajarki a halin yanzu, yaron nan baida wata illa, bai da wata makusa" "Inna kiyi min addu'a kawai" cewar Zarah tana riƙe hannun inna. "Addu'a ai kullum cikin yi muku nake, Allah ya shige mana gaba, ya zaba miki mafi Alkhairi" "Yawwa Inna haka nake so ki dinga cewa" Inna bata ce komai ba ta tashi ta fita. Bata jima da fita ba Aysha ta shigo fuska dauke da murmushi.. kayan hannunta ta zube akan gado tana fad'in "Kayan fitar suna ne nawa da naki" Sau ɗaya Zarah ta kalli kayan ta ɗauke kai tana fad'in " waye ya baki? "Ni na siyo, Kinsan ina da tailor anan Abuja so a wajenta na siya nace ta dinka mana, naki milk nawa red, isn't this beautiful? Aysha ta ƙarashe maganar tana daga leshin. "Nagode Aysha, amma inada kayan da zan saka, Yaya ya zaɓa min" "C'mon ai sai ki saka wannan da rana ko da yamma" "Shikenan Nagode" Cewar Zarah ba tare da ta kalleta ba. "Yawwa, bari na tafi da nawa, sai na dawo na dauki Hydar" Kai kawai Zarah ta gyada mata... Tana fita ta dauki danta ta nufi dakin ubansa... Mustapha na aiki da computer ta shigo ranta a haɗe.... "Gashi nan kuma ban yarda ka bawa Kowa ba bllnt wata Aysha" ta faɗa tana miƙa masa Hydar... "Kya haɗani da renon yaro ina aiki? Why not ki kaiwa Ummi ko Inna? "Ai nasan dasu na kawo maka! Aysha ce take son ɗauka ni kuma bana so yarona yana zama da ita, idan na kaiwa Ummi ko Inna zata iya karbar sa a hannunsu bazan iya musu kashedin karsu bata ba, kai kuma zan iya" "Ok kice rowar ɗa kika fara? "Eh shi na fara ai ba wani ya ɗaukar min cikin ya sha min wahalar haihuwa ba! Ta ƙarashe maganar tana ajiye masa Hydar a cinya.. hannunta ya riƙe yana fad'in " baki nuna min retouching ɗin ba" "Tunda kaga na Aysha ae ya wadatar! Ta faɗa tana kwace hannunta.. "Zarah! Ya kirata.. kallonsa tayi ganin how serious he's ya saka ta ce " Lafiya? "Karki sake min maganar Aysha idan muna tare kinji ko? Shiru tayi tana baza masa idanuwa. "Magana fa nake" ya sake faɗa idanunsa cikin nata. "Ai toh gaskiya na faɗa, inda ace Ummi bata ce ka kaini ba nasan ba zaka kuma fita kaini saloon ba! Amma ka iya kai wata Aysha! "Ok yanzu dai kishi kike? "Kai kake ganin hakan amma right dina kawai nake so! Daga haka ta fice ta barshi... "Right? Mustapha ya maimaita yana sakin murmushi.. "Shidai yana fatan abinda yake tunani ya zamana gaskiya, but kafin Zarah ta koma Kano zaiyi proving koma menene, yana fatan ganin abinda yake so ɗin.. wani murmushin ya saki yana pausing din aikin da yake yi sannan ya gyara Hydar dake jikinsa yana bacci... A falo Zarah da Aysha suka hadu.. Aysha na yanƙare haƙora ta ce " Daga dakinki nake yanzu, ina Hydar ɗin? "Yaya ne ya kirani yace na kaishi wajensa" Cewar Zarah tana wucewa bedroom... Da kallo Aysha ta bita sai kuma tayi murmushi tana wucewa kitchen... Maid din Ummi ta gani tana kokarin fito da food preservers saboda dinner time... "Jeki ajiye kizo kiyi min fruit salad! Da toh ta amsa tana fita daga kitchen ɗin.. bayan ta dawo Aysha ta saka ta haɗa mata fruits sannan ta yi fruits salad ɗin da kanta, fita tayi ta nufi dakin Mustapha rike da bowl din data haɗa komai. Mustapha na kwance Hydar akan cikinsa dukansu idanunsu a rufe... kafeshi tayi da idanu, tun daga kan low cut askin dake kansa har zuwa well shaped eye brows dinsa da lumsassun idanunsa zuwa kan hancinsa har lebansa ko wanne kallan ƙurilla take masa... "Bata taɓa tunanin abubuwan zasu juye haka ba! She's falling for me so deeply... Nunfashi taja tana saukewa a hankali... "Buddy! Buɗa idanunsa yayi dan dama tun shigowarta yasan ta shigo Cox ba bacci yake ba, and scent ɗinta ya tabbatar masa da cewa itace ba Zarah ba. "Na kawo maka abun kwadayi, tashi kaci" "Ohk' ya fada yana dauke Hydar dake cikinsa.. a kan gado ya kwantar dashi yana kallonta ya ce " All this? Murmushi tayi tana fad'in " Wato zakayi pretending yayi maka yawa ko? Bayan nasan yanzu zaka cinye tas" Murmushi yayi yana karɓar bowl ɗin.. "Ke kinci? "No I just made it for you" "Thanks alot! Ya faɗa yana sakar mata murmushi.. murmushi ita tayi tana zama a gefan gado ta ɗauki Hydar.. "Yaron nan da kai yake kama, sai dai ya dauko duhun Zarah" Mustapha na murmushi ya juyo yana kallon Hydar dake ta bacci abunsa.. "Ka gani ko? Ina imagine ace kun haifi mace yadda zata zama so beautiful, Buddy kasan me? Ta faɗa tana kallonsa. "Inajinki" Sai data hadiye yawu sannan ta ce, " Be kamata ace ka saki Zarah ba, duk da Bansan me ya kawo sanadin sakin ba amma ku biyun kun dace da junanku sosai, kuma kuna son junanku meyasa zaku bar zukatanku cikin ƙunci? Dan Allah ku zauna ku gyara tsakaninku ko dan Hydar! Saboda ku samu damar ƙulla bond me ƙarfi a tsakanin ahalinku, yanzu idan ka koma UK Hydar zai taso wajen Zarah, ba zai wani sanka ba! Idan ma karɓar ɗanka zakayi kaga ka raba uwa da ɗanta, yaron zai taso ba tare da kulawar uwa da soyayyar uwa ba, kuma babu abinda zai iya replacing din wannan kaima ka sani, so dan Allah kuyi haƙuri ku gyara tsakaninku" Murmushi yayi kaɗan yana kallon Aysha ya ce, "Naji daɗin shawararki, tabbas kedin ta dabance Aysha, amma Ni da Zarah mun zaɓi hakanne, saboda she needs some time kuma a shirye nake na bata duk lokacin da ta buƙata.. i think she's not ready for being a married woman, kinga rabuwar yafi ko? "But buddy wannan ba dalili bane! Wannan dalilin ba shine zai sa ka saketa ba! Aure ai ba abun wasa bane" "Na sani Aysha amma bazanso nayi rayuwar aure mara farinciki ba" Ajiyar zuciya Aysha taja tana kallonsa ta ce, "Yanzu kana nufin sai lokacin data shirya zaman aure sai a mayar muku da auren? "Yeah! Ya bata amsa batare da ya kalleta ba. " Are you kidding me? Please Buddy just find another excuse! Wannan zancen naka hankali ma bazai dauka b! Zarah bata chanchanci abinda kayi mata ba! Aure ko shekara beyi ba? Ka bani kunya Buddy! Daga haka ta tashi ta fita tana jijjiga Hydar dake son fara rigima. Da kallo kawai ya bi bayanta. Ɗakin Zarah ta wuce, fitowar Zarah kenan daga toilet tayi wanka tana son kwantawa saboda ta huta.. kallon² suka tsaya yi, daga bisani Aysha ta ce " Magana nazo muyi Zarah" "I'm not in the mood please" cewar Zarah tana ƙarasowa inda take ta karɓi ɗanta. "Ohk badamuwa insha Allah gobe ko Bayan taron suna ne sai muyi" "Idan ma akan Mustapha ne dan Allah Aysha stay away from this! Tsakanina dashi u have no right to interfere please! Ajiyar zuciya Aysha ta sauke tana ɗan sakin murmushi ta ce " Kina sonsa? "Wannan be shefeki ba! Zarah ta fada tana ɓalla mata harara. " Ok then, idan har Dagaske bakya sonsa inason maye gurbin ki! "Wannan ne baki isa ba kuma! Dan Allah ki fice min a ɗaki! "Basai kin koreni ba Zarah, zan fita da kaina, inason Mustapha, kuma nasan kin san menene so tunda har kika kashe aurenki saboda soyayyar Ammar! Yanzu You are free zakije ki auri wanda kike so, dan haka Nima inason na auri wanda zuciyarta take muradi, kuma kece wadda zata taimaka mun tunda ba sonsa kike ba! Kinsan wani abu? Ni bana sharing abu a arayuwata, tunda na taso a gidanmu Ni kadai, komai nawa Ni kadai ne ba tare da kowa ba! Wannan dalilin yana ɗaya daga cikin dalilan da yasaka Mustapha ya sakeki saboda ni da shi ɗin mun shirya rayuwa tare ba tare da kowa ba! I'm not his friend rather than his girlfriend Kuma har magana yayi da iyayena akaina, Mustapha be taɓa sonki ba, kedin matar shige ce ni kuma zaɓinsa... Amma karki wani damu yanzu komai yazo karshe ai, na barki lafiya" Daga haka ta fita ta bar Zarah tana jin wani nauyi a zuciyarta...