✨ *MATANA* ✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
*Comment*
*Vote* &
*Share* Fisabilillah*My WhatsApp group link, Dan Allah mata kawai*
https://chat.whatsapp.com/BrUNywiBsPxDJjxclwHfdU'''Assalamualaikum jama a ina sanar daku cewa wanna shaharariyar Mai makeup dinna Wanda akaf maiduguri babu kamarta wato AMMIS GLAM tana sanar daku cewa akwai ingantatun man gyara gashi ga Mai bukata zai iya tutubar number ta kamar haka..... 08030687711 muna bada sari a kowani state kike za a iya aika Miki kedai Yar uwa kiyi Kokarin mallakar naki kamin ya kare 500 ne kachal Amma idan sari zakiyi akwai discount sanna wanna man gyaran gashin Yana Kara tsowon gashi da laushi sanna Yana hana karyewar gashi sanna Yana sa gashinki yayi baki sosai sanna Yana maganin amotsrin gashi Yar uwa karki Bari a baki labarin don wanna man Basu da wani illa domin an hada sune da ingantataun kuma nagartatun mayuka masu aminci da karfi da basu da wata illa sai ma taimakawa da yakeyi karde ku Bari abaku labarin wanna Mai gashi na AMMIS HAIR OIL/CREAM'''
'''sanna pls don Allah idan kinsan ba siya ko sari zakiyi ba pls karkimin magana ko kikirani'''
*023*
"Ina yini? Yame jiki? Cewar Aysha cikin ladabi tana kallon Ummi. "Lafiya lau, jiki alhmdll" Ummi ta amsa idanunta a kanta.. Inna ta gaisar tana maida dubanta ga Zarah da itama kallonta takeyi.. "Sannu" Ta fada a hankali.. Zarah bata iya amsawa ba sai kai kawai data gyaɗa mata. Wajen zama Ummi ta bata.. Zainab ce ta shigo ɗakin tana fad'in "Anje za'a gwada shi, Ni zan wuce makaranta saboda muna da test" "Ok kin dai bada latter dana rubuta a kai student affairs ko? Cewar ummi tana kallonta. "Eh Ummi kuma sunyi accepting, nan da 3weeks suka bata tunda bata da lafiya" "Ok Allah ya bada Sa'a" da Amin Zainab ta amsa kafin ta kalli Zarah ta ce "Allah ya kara sauki" daga haka ta fita. Sai bayan azahar Mustapha ya dawo dakin.. Inna, Aysha dake riƙe da babynsa kawai ya gani a ɗakin, ƙarasawa yayi yana fad'in " Ina Ummi da Zarah? "Basu daɗe da shiga banɗaki ba" Cewar Inna tana kallonsa. Ƙarasowa yayi yaja kujerar roba ya zauna yana fad'in " Inna wannan sunanta Aysha ƴar wajen aikin mu ce" "Ayya, ai tana da kirki itama baturiyar ce? Dariya Aysha da Mustapha sukayi kafin Mustapha ya ce, "Bahaushiya ce kawai dai mahaifiyarta buzuwar Nijar ce shiyasa kika ganta fara tas" murmushi kawai Aysha tayi tana miƙa masa yaron.. cikin tsantsar so da kaunarsa ya karɓeshi yana ƙarewa cute face din yaron kallo, sai bacci yake abunsa... Kallon yaron kawai yake yi har su Zarah suka fito daga toilet.. taimaka mata Ummi tayi ta zauna sannan ta haɗa mata abincin da Inna ta girko... Sai a lokacin ya san sun fito, tasowa yayi ya nufi inda take fuskarsa cike da murmushi... Zarah kuwa sunkuyar da kanta tayi kirjinta na bugawa.. "Ya jikin? "Da sauki" ta amsa a hankali. "Masha Allah, Allah ya kara lafiya, sannu" Kai ta gyada ba tare da tace komai ba... Abinci Ummi ta zubawa Aysha tana fad'in " Kiyi haƙuri an barki ko ruwa babu, Mustapha jeka siyo ruwa a wajen asibiti zaka ga shago, ka siyo cartoon uku mara sanyi" Da ok ya amsa yana miƙa wa Ummi yaron. Be dade ba ya dawo ya ajiye ruwan yana gyara rigar jikinsa idanunsa akan Zarah dake pretending bacci takeyi... Nurse ce ta shigo riƙe da tray, kallon Zarah tayi ta ce "Sannu ya jikin? "Da sauki" ta amsa tana buɗe idanunta. "Allah ya kara sauki, yanzu zan sa miki jini kinji ko? "Toh" ta amsa tana gyara kwanciyarta.. cikin ƙanƙanin lokaci akayi fixing din jinin, kwanciya tayi tana lumshe idanunta.. fita Nurse ɗin tayi bayan tayi musu godiya.. "Bari naje gida Aminatu, na samu nayi wanka ko? Cewar Ummi tana kallon Inna. "Eh toh nima bari na biki sai in girka abincin dare na tafi da wannan ragowar tunda Allah yasa Mustapha yana nan" Gyaɗa kai Ummi tayi sannan suka fara haɗa kaya, sallama sukayi musu sannan suka fita.. sai a lokacin Aysha ta taso ta iso gaban gadon Zarah tana ƙare mata kallo kusan minti ɗaya kafin ta ce " Tasha wahala sosai, i pity her! Mustapha bai ce komai ba ya karaso inda Zarah take yana zama a jefan gadon.. " Zarah! Ya kira sunanta.. tana jinsa amma tayi shiru.. "Bacci ya dauketa fa " Aysha ta faɗa tana kallonsa. "Ba bacci take ba! Zarah Please just open your eyes magana zamuyi" nan ma ƙin buɗa idanunta tayi.. "Bari na ɗan fita " cewar Aysha tana barin wajen da sauri zuciyarta na bugawa... Zarah najin fitarta ta buɗe idanunta akansa.. "Nasani dama ba bacci kike ba" Shuru tayi tare da kawar da idanunta akansa. Hannunta da babu cannula ya riƙo a hankali yana ɗan murzawa ya ce " Sannu Zarah, Allah yayi miki albarka" Hawaye taji sun taru a idanunta zuciyarta tayi mata nauyi.. "kukan fa? Kamar jira take ta fashe da kukan da bazata ce ga dalilin yinsa ba. "Ya isa mana! So kike su Ummi su dawo suce na saki kuka? Please mana! Sai da tayi me isarta sannan ta tsayar da kukan tana goge fuskarta.. "Bakya son ganina? Shuru tayi tana lumshe idanunta. Nunfashi ya sauke yana tashi daga kan gadon yaja kujera ya zauna, kafeta da idanu yayi zuciyarsa na bugawa da karfi yana jin wata iriyar sabuwar soyayyar ex wife dinsa na shigarsa.. lumshe idanunsa yayi a hankali yana riƙe kansa.. kusan minti biyu sannan ya buɗesu yana tashi tsaye ya ce " Zan fita yanzu zan dawo anyi la'asar" "Amma akwai toilet a nan ko? Ta faɗa tana buɗe idanunta.. shafa kansa yayi kaɗan kafin ya ce " Zan kira Aysha ta shigo, maybe bata jin daɗin zaman wajen" "Wacece ita? Yaji ta faɗa unexpected. Shuru yayi yana kallon ta, ganin baice komai ba ya saka ta ɗauke kanta daga kallonsa tana fad'in " Is okay" matsowa yayi inda take yana kallonta ya ce " Just a friend, ita tace zata rakoni saboda ta ganki that's all" "Ok bata da iyaye ne? "Kamarya? Ya fada cike da rashin fahimtar maganar ta. "Ina nufin bata da iyayene da zasu barta ta biyo stranger tun daga America zuwa Nigeria? Just the two of them? Murmushi yayi kaɗan yana kallonta... "Shikenan, Ni zanyi bacci" "Zarah! Ya kirata zuciyarsa na ɗan bugawa da karfi.. is she jealous or what? Cikin son tabbatar da zarginsa ya ce " Na fada miki friend ɗina ce, kuma da consent ɗin iyayenta muka zo nan, don't think too much ki huta bari na kirata" bata ce komai ba.. shima be ƙara cewa komai ba ya fita yana kawar da tunanin abinda zuciyarsa take bashi dan yasan is impossible. A zaune ya ganta a kan kujera tana latsa waya.. "Aysha kije ciki" "But buddy kana ganin is ok idan na zauna da ita? "Don't worry, jeki kawai" tashi tayi tana kallonsa ta ce " Nasan baxataji daɗin ganina tare da kai ba, bana son causing any trouble Ina tunanin zan wuce hotel zaifi"... "Na ce miki ba komai! Nayi mata bayani, kije kinga ba kowa a dakin" Gyada kai tayi tana kallonsa sannan ya fara tafiya... Dan juyowa tayi ta kalleshi ganin har yayi nisa ya sakata yin murmushi kaɗan tana wucewa itama. Bayan ta idar da sallar la'asar ta ɗauki babynsu jin ya fara kuka, a time din bacci ya ɗauke Zarah.. kusa da ita ta nufa tana kallonta.. taɓa baki tayi tana kallon jinin dake shiga jikinta, a hankali ta jaa robar da ake saita yadda amount of jinin da zai dinga shiga.. rageshi tayi jinin ya daina diga, sannan ta cire shi daga bakin cannular.. a hankali ta buɗe bakin cannular jini ya fara flowing yana fitowa.. da sauri ta bar ɗakin.. tana zaune a wajen dazu Mustapha ya dawo, da sauri ta tareshi tana fadin " Buddy ina jin yunwa" "Ok, bari na duba Zarah sai na rakaki ki siyo" "She's ok, yanzu na fito" "Ok muje ba nisa ae" murmushi tayi tana ƙara rufe yaron sannan suka fita... Packaging ya saka akayi mata sannan suka koma sai janshi take da hira... Suna shiga dakin suka tarar da Zarah tana mimmiƙewa.. sakin packaging din daya riko yayi ya karasa da sauri, jini ne sosai ya zuba a kasan tiles din wajen, gashi an cire jinin da ake kara mata gana jikinta yana ta zuba kasancewar cannular a buɗe take.. da sauri ya kalli Aysha ya ce " What is this? Bance ki kula da ita ba kafin na tafi?! Me haka? Me kika ce min kafin mu tafi siyan abinci? Cikin faɗa da tsawa yake magana kamar zai daki Aysha... Sai kuma ya fita da sauri, tare suka dawo da Nurse.. da sauri ta karasa tana fadin "Garin yaya hakan ta faru? Jinin da ake lallabawa? What's all this? Waya ce muku ana fita abar patient din da aka sakawa jini? Nurse ɗin na masifa tana gyarawa, bayan ta gyara ta kalli Mustapha ta ce " Lallai kana wasa da rayuwar matarka! Daga haka ta fice. Bata dade da fita ba cleaner yaxo ya gyara inda jinin ya ɓata.. kusa da Zarah ya nufa yana rike hannunta a hankali ya fara tofa mata addu'o'i... Shafa hannunta yake zuciyarsa na zafi.. kissing din hannun yayi yana jin tsantsar tausayinta dan yasan ita kaɗai tasan me take ji a jikinta.. Aysha kuwa kallonsu take tana haɗe rai.. "Allah zai baki lafiya, kiyi hakuri da barinki da nayi" Tasowa A'isha tayi tana marairaice fuska ta ce " Kayi hakuri Buddy, lafiya lau na fita na barta fa" "meyasa zaki fita? Meyasa? Da bamu dawowa ba wani hali kenan zata shiga? Na kusa fa rasata? Can you imagine?! Hawaye ta fara yi, da sauri ta fita a dakin. Nunfashi ya sauke a hankali yana shafa hannun Zarah.. slowly ta fara buɗe idanunta da sukayi mata nauyi... Idanu ta zuba masa kasancewar ya sunkuyar da kansa bega tashinta ba.. " Ina yarona? Ta faɗa muryarta na rawa.. "Ya wajen Aysha" shuru tayi ba tare da tace komai ba.. "I'm so sorry" "For what? Bai ce komai ba ya riƙe hannunta sosai.. itama bata kara ce masa komai ba ta rufe idanunta.. kusan 10mins sannan ya tashi yana kallonta, ganin tayi bacci ya sashi sauke ajiyar zuciya.. light kiss yayi mata a goshi a hankali ya furta " Allah ya baki lafiya" kan sofa ya koma yana zama tare da dauko Wayarsa a aljihu.. yana cikin danne² Su Ummi suka shigo... " Ya ka bar baƙuwar taka a waje? Me ya faru ne? Naga Kamar kuka tayi" shafa kansa yayi kaɗan yana tashi tsaye ya ce " Sannunku da zuwa" "Yawwa, meyafaru? "Bakomai Ummi" ya amsa yana kallonta.. "Ya zaka ce bakomai bayan ga yarinya chan kamar tayi kuka idanunta duk sun kumbura? Ya zaka dauko yarinyar mutane kuma ka barta haka Mustapha? Cewar Inna tana kallonsa... "Bansan me akayi mata ba, amma bari naje" daga haka ya fita.. a chan compound din asibitin ya ganta a zaune tana rike da yaronsa.. kusa da ita ya zauna.. calmly ya ce " Kiyi haƙuri" "Bakomai buddy, ni ya kamata na baka hakuri" ta karashe maganar tana goge hawayen da suka zubo mata.. ajiyar zuciya ya sauke yana ganin kamar be kyauta mata ba.. "shikenan tashi mu koma ciki" "No, zan wuce gobe zan dawo insha Allah" ta faɗa tana miƙa masa yaron.. karɓar babyn yayi yana kallon ta ya ce " Fushi kike? Amma ai na baki haƙuri, na kasa controlling anger dina ne a time ɗin, but I'm sorry" "karka damu! Ta faɗa hawaye na biyo kuncinta, kuma tana ƙoƙarin tafiya. Riƙo arms dinta yayi yana fad'in " Bazaki hakura ba kenan? Kuka ta fashe dashi tana kokarin kwace hannunta. "Aysha me haka? Zaki saka mutane suyi ta kallanmu! "Ban taba tunanin haka daga gare ka ba! Nima kasan bazan so wani abu ya sami Zarah ba, kafin kowa sanin yadda nake sonta saboda nasan kana sonta, amma kayi min bahaguwar fahimta, kana ganin kamar ina sane na bar komai ya faru, meyasa zanyi haka Buddy? Calmly ya ce " Shiyasa na baki haƙuri nasan ban kyauta ba, yanzu dai mu koma ciki kiyi wa su Ummi sallama Nima tafiya xanyi ai" goge idanunta tayi kalleshi ta ce "Ok muje" ajiyar zuciya yayi yana bin bayanta... Sallama sukayi wa su Ummi sannan suka fito... Kusan karo sukayi da Ammar! Da sauri Mustapha ya matsa baya yana kallon sa da kyau kafin idanunsa su sauka akan Zainab da wata wadda bazata wuce sa'ar Zainab din ba... "Yaya dama Waheeda ce tace zan rakota wajen Aunty Zarah shine kuma ashe da shi zasu zo" Zainab ta faɗa a hankali kirjinta na bugawa. "Ok, muje" "but Buddy na dauka tafiya zamuyi" cewar Aysha tana kallonsu.. " Eh mu bari sai anjima" daga haka yabi bayansu su Ammar.. a ciki suka tarar da Nurse tana cire wa zarah ledar farko za'a saka ta biyu... "Ummi kawar Zarah ce da Ammar suka zo! Cewar Zainab tana karasowa inda Ummi take... "Kice su shigo mana" da ok ta amsa tana fita, tare suka shigo har Mustapha da Aysha... Tunda ya dora idanunsa akanta ya kasa saukewa, duk ta rame sai haske data yi... No wonder kwanakin nan yake jinsa duk wani iri... "Zarah ya jikin? Ya fada still idanunsa a kanta.. "da sauki " ta amsa tana sunkuyar da kai. Numfashi ya sauke yana tsugunnawa ya gaida su Ummi. Kusa da ita Mustapha yaje ya zauna yana bin Ammar da kallo. Ita dai Ummi kallonsu take dan tayi tunanin ma su Mustapha sun tafi. "Yaya Ammar ga Babyn" cewar Waheeda tana mika masa babyn.. karba yayi yana kallon fuskar yaron, murmushi yayi kafin ya ce "Allah ya raya" da Amin suka amsa gaba ɗaya... "Jinin zai iya karewa by 12am so ku kula yana ƙarewa ku kirani" da toh inna ta amsa sannan nurse ɗin ta fita. Ɗaya gefan nata Ammar ya dawo, Ummi kuwa fita tayi daga ɗakin kar ma ta ɓaci da ita yadda taga Mustapha yana hura hanci! "Ka wani je gaban gado ka nanike! Zaka fito ka barta tasha iska ko kuwa? "Mustapha ana magana! Cewar Ammar yana nunawa Mustapha Inna dake magana.. "Ai kaima kasan kanka! So don't let me loss my temper Ammar! Just get lost mungode! "I'm not leaving! Kai daga shirya tafiya tun dazu sai ka tafi! " Are You mad? Kai har kana da right din da zaka fada min na tafi? "Maybe! Saboda baka da wani iko akanta yanzun! Baka isa kuma ka hanani zama ba! "Ammarrrrrrr! Cewar Zarah tana buɗe idanunta... "Dan Allah bana son shiririta kamar ƙananan yara! Cewar Inna tana kallonsu... "Dan Allah ya isa, can't you both see we have a lot of guests? Why can't you both behave your selves? Cewar Zarah idanunta akan Ammar... "Ok Ni kaɗai zakiyi blaming! "Ba ina blaming dinka bane duka ku biyun nake wa magana" "But ni kaɗai kike kallo why? Aysha dai kallonsu take dan gaba daya sun daure mata kai, Zainab kuwa fita tayi, haka ma Waheeda.. Inna ma tashi tayi tana fad'in " ku fito ku wuce ku duka! "Haba Inna yanzu fa nazo! "Nidai na faɗa muku ku zo ku wuce! Tashi sukayi suna kallon Zarah duk su biyun.. "Get well soon Zarah" cewar Ammar yana kallonta. Mustapha kuwa light kiss yayi mata a hannu yana fad'in " Stay blessed Zarah" ita dai babu wanda ta kula a cikinsu. Korasu Inna tayi... A waje suka tarar da su Ummi suna hira.. "Ummi mun wuce Allah ya kara mata lafiya" cewar Aysha tana kallonta. A gaida gida tayi wa su Ammar sannan suka nufi ciki.. suna cikin tafiya Aysha taja Zainab zuwa baya, a hankali ta ce " Waye wannan Ammar din? Taɓa baki tayi tana fad'in " Tsohon saurayin Aunty Zarah ne fa! Kuma naji Waheeda tace wai zai aureta yanzu" "aure kuma? Wani irin aure? "Zainab ki taho kar dare ya kara yi su hanamu shiga hostel! Cewar Waheeda tana kallonta. Da sauri ta bar Aysha ta nufi motar Ammar.. a bakin titi Mustapha ya tsaya dan tsarar musu Napep. Gaba daya ta faɗa duniyar tunani.. bayan sun isa Hotel din da suka sauka har ya shiga daki yayi wanka ya kwanta ta kirashi... Jallabiya ya saka ya fito, kallonta yayi daga sama har ƙasa ya ce " Ina hijabinki? "Ba fita zamuyi ba, magana zamuyi" "Ok ina jinki" "mu shiga ciki" da ok ya amsa yana bata hanya.. akan gado ta zauna tana kallon sa ta ce, " Zauna mana" kan sofa y zauna yana kallonta ya ce " Meyafaru ne? " Kai da Zarah kun rabu ne? Shuru yayi yana kallonta kafin ya ce "Waye ya fada miki? "No one! Nayi amfani da tunani na ne! "Ok wannan maganar ce ta saka kika taso cikin daren nan? "Eh abun ya dameni ne! Me ya faru har haka Buddy? Auren ko shekara bana tunanin yayi a yadda ka faɗa min! Baka tausayinta ne? I'm really really disappointed wallahi, be kamata ba! Baka kyauta ba! "Amma ai bani da zaɓi! Just let it be, kije ki kwanta sai da safe... Batayi musu ba ta tashi ta fita... Kasa bacci Mustapha yayi, sosai yake ji yayi wauta da ya biyewa Zarah! Anya kuwa zai iya jurewa? Duk da Zarah bata kasance zabin mahaifiyarsa a farko amma yanzu ita din farincikinsa ce! Sai kusan asuba ya kwanta...