✨ *MATANA* ✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*Comments*
*Vote &*
*Share fisabilillah**037*
Ammar na zaune a driver seat yana jiran Zarah, ya kai 10mins zaune cikin mota amma bata fito ba, har yayi deciding ya koma yaga me take yi sai gatanan ta fito tana gyara zaman hijabinta, murfin front seat ta buɗe sannan ta shigo tana fad'in "Sorry, na rasa me zan kaiwa Aunty Hafsat ne wallahi shine kawai na ɗebo mata turarruka" "Kufa mata kuna da wani hali wanda sai ku din dai, yanzu kema idan zaki taho nasan sai ta baki wani abun, Uhmm this gender have issues wlhy" Ammar ya ƙarashe maganar yana dariya tare da Girgiza kai. Rabi'u ne ya buɗe masa gate suka fito. "Ai dai kyautatawa ce, me aibu? "A'a babu komai hakan na da kyau, zan barki a chan by 5pm zan dawo na daukeki, and zamu je wajen Saude ba sai kin kuma fita gobe ba ko? "Haka ne" Zarah ta amsa tana gyara zamanta. Bayan sun isa gidan Umar yayi horn gateman ya leƙo yaga motar Ammar sannan ya buɗe musu yana ɗagawa Ammar ɗin hannu. Sai da yayi parking ya kashe motar sannan suka fito, hannunta ya rike suka nufi entrance ɗin gidan. Zarah ce ta fara shigowa, Hafsat na zaune a falo da remote a hannunta cikin jikinta yayi girma kuma ya mata kyau sosai, murmushinta ne ya faɗaɗa bayan tayi arba da fuskar Zarah, "Tun safe nake baza idanu, Omar har ya gaji da jiran Ammar ya fita kasuwa" Shigowa Ammar yayi yana fad'in " Haba dai? "Eh mana bai daɗe da fita ba sannunku da zuwa, ku zauna mana" Ta ƙarashe maganar tana tashi tsaye. "No bari na bishi ita dai ta zauna, take care of my wife Kuma" Daga haka Ammar ya tafi. Murmushi Hafsat tayi tana zaunar da Zarah ta ce, "Tun dawowar ku daga America naso zuwa amma bana jin daɗi sam, yakike? "Lafiya lau Aunty Hafsat, ina yini? "Lafiya Alhamdulillah, kinga yadda kika ƙara kyau Masha Allah wallahi, ko dai²? Hafsat ta ƙarashe maganar cikin sigar tsokana. Ita dai Zarah murmushi kawai take. "Bari na kawo miki abin taɓawa kar na cikaki da surutu" Daga haka ta tashi ta tafi kitchen, bata ɗau lokaci ba ta dawo da tray a hannunta, kayan tanɗe² ta kawo mata tana fad'in " Saura kaɗan na gama abinci, seriously Fatima faɗa min menene sirrin, skin dinki so smooth sai glowing kike abunki, ko dai dagaske cikin ne? "A'a fa" Zarah ta faɗa tana sunkuyar da kai. " Wato a chat ki cikani da surutu a fili sai wani sunkuyar da kai kike? C'mon idan ma zaki sake ki sake dan hira nake so muyi sosai, daa Waheeda ma tace zasu zo na hanasu saboda zuwanki inaso muyi hira dan inaso mu ƙara shaƙuwa, shine kike son bani kunya kuma? Dariya Zarah tayi me sauti tana kallon Hafsat. "Eh mana, anyway ya school? Nima fa inaso na yi masters ɗina wallahi amma bansan ta in da zan je wa Omar da maganar nan ba" "Idan kina ganin bazai yarda ba is better ki haƙura tunda har kina da degree ɗinki" cewar Zarah tana kallonta. " Actually inaso nayi karatu me zurfi sosai, amma kinsan Omar fa ya taɓa ce min in his opinion yafi so ya auri wadda iyakacinta secondary school, lokacin daya fara ganina kuma zancen ya canza, kinsan maza dayawa suna ganin duk macen da tayi jami'a idanunta sun buɗe kamar tafi karfinsu, which is not right, ilimin fa ƴa mace abu ne mai matuƙar mahimmanci kuma zai amfanar da al'umma, ko da batayi aiki ba zata iya koyar da yaranta, a lokacin na faɗa masa wannan maganar kawai nasan jina yake, a time ɗin ina level 300, ya kwallafa rai sai munyi aure amma Dad ɗina yace sai na gama, ai wallahi nasan da anyi auren kwalin degree ɗin ma bazan samu ba" ta ƙarashe maganar tana dariya. Itama Zarah dariya tayi tana ɗorawa da faɗin " Gwanda da kika ƙarasa abinki gashi yanzu ya zama labari" "Wallahi kam, idan ka biye ta soyayya kai ne a ruwa, ke su auroki sun hanaki karatu idan sun tashi ƙaro aure su ɗauko me PhD ai lamarin maxan nan sai addu'a wallahi" Hafsat ta ƙarashe maganar tana dariya. Itama Zarah dariya tayi tana gyaɗa kai alamar gaskiya ne. "Bari na duba abinda na ɗora" Cewar hafsat tana tashi ta koma kitchen, ta ɗan ɗau lokaci sannan ta fito ɗauke da medium tray ta zubo abinci sai ƙhamshi yake. A gaban Zarah ta ajiye tana sake barin wajen, rike da tray ta dawo wanda ta jero natural drink da medium bowl. "Toh Mrs Ammar sakko muci" Ba musu Zarah ta sakko tana shaƙar khamshin girkin ta ce, "I like the scent" dariya Hafsat tayi tana cewa, "Ai amfanin spices kenan, su ƙarawa abincinki ƙhamshi da kuma ɗan ɗano, idan zaki tafi zan baki ki gwada ki gani, idan kinaso sai na baki number me sai dawa, ko ƙanin mijina yaji sauyi" murmushi Zarah tayi tana kallon Hafsat. "Well, kinsan kuwa yadda Ammar yake kaunarki? Kedai kawai ki cigaba da kula da Mijinki, karki yarda wata kishiya ta dinga saki kina janye jikinki a kan Mijinki, Kema fa aurenki yake yi, ki cire idanunki daga kan kishiya ki sa a ranki ke kaɗai Ammar yake aure ki bashi duk wata kulawa, Nasan is not easy ace family ɗin mijinka basa sonka, dan nima ya faru da elder sister ɗin mu, ƙarshe dai sai raba auren a kayi saboda fitintinu sunyi yawa, so bana miki fatan irin haka, itama sake tayi duk dai da ƙaddara, amma ke kam karki saki fuska da jiki yadda za'a raina ki wallahi, kuma kar kiyi gaba da kowa Lokaci - lokaci ki dinga zuwa gai she da Maminsa, kina ɗanyi abun kwaɗayi kina kai mata, ba ruwanki da duk abinda wasu zasu ce, Mami fa tana da sauƙin kai wallahi, wannan ƙanwar nata ne me kumbura bala'i ta kuma siranta zaman lafiya, ki dage da addu'a sosai in sha Allah zaki ga komai ya wuce wallahi kedai kar ki sake da athkhar, sallar dare, karatun Alkur'ani hmm ki riƙe su kixo ki bani labari" Hafsat ta ƙarashe maganar tana zuba coslow a offal jollof rice ɗin da tayi. "Kin ga wannan sanyi² wallahi ki daina shi, ki sake abunki a gidanki, dan ni rannan da mukaje naga kamar ma tsoran Bilkisu kike ji, and shi kanshi Ammar din kamar baku wani saba ba, ba haka nayi tunanin ganinku ba a yadda nasan love story ɗinku, ki dinga kwantar wa mijinki da hankali kinji ko? "Toh" Zarah ta faɗa tana kai lomar abinci. "Good, mu dai gama cin abincin akwai maganganu sosai, kinsan ba kyau ana ci abinci ana surutu" Murmushi Zarah tayi tana gyara zamanta. Sosai Hafsat ta bata shawarwari cikin ƴan awannin da tayi tare da ita, kuma ta ƙaru da abubuwa dayawa da Hafsat, tabbas Hafsat macece me fasaha duk wanda ya zauna da ita ko yaya ne sai ya ƙaru da ita, sosai Zarah taji daɗi kasancewa da ita kuma ta saki jikinta sosai. Bayan sallar la'asar su na kitchen ita da Hafsat, Zarah na fere mata doya, su Ammar suka shigo.. Hafsat ce kawai ta fita Zarah kuma firar doyar ta cigaba da yi. "Aiki kika sakata? Daga zuwa ziyara? Zarah ta jiyo Muryar Ammar.. "Eh dai, idan kuma baka so ta yi sai na sani" Hafsat ta bashi amsa tana cire hular kan mijinta. Lekowa Zarah tayi ta taga tana kallonsu.. "Welcome home sweet mie" Cewar hafsat tana yi wa Umar murmushi me cike da soyayya. "Xarah ki fito ku gaisa da Hubby" Hafsat ta faɗa tana kallon direction ɗin kitchen ɗin. Da Ok Zarah ta amsa tana fitowa kanta a sunkuye. Calmly ta karasa ta ce, "Ina yini? Umar na murmushi ya amsa da "Lafiya lau Zahmar! Ko ba haka bane? Bata ce komai ba ta sai ƙara sunkuyar da kanta da tayi, riƙota Ammar yayi yana kallon Umar ya ce, "Kai fa kasan kunya ce damu" Dariya Umar yayi me sauti yana fad'in " Na sani" "ɗauko mayafinki mu tafi, Hansatu a je a ƙarasawa miji girki a dena bawa matan mutane wahala daga zuwa ziyara" "Kar dai ka shiga tsakanin mu, cewar Hafsat tana janyo hannun Zarah suka wuce ɗaki... Almost 10mins Ammar yana jiranta amma bata fito ba. Zama yayi a kan kujera yana kallon Umar ya ce, "Su fa mata idan suka haɗu sai addu'a" "Ko dai gulmar mu suke? Cewar Umar yana kallonsa. "Zasu aikata, wannan daɗewa da sukayi gulmar ce" Dariya Umar yayi yana fad'in " Kai dai ka sani" Kafin Ammar ya ce wani abu sai gasu sun fito. "Toh Ammar ku gai da gida" "Ok Mom twins" Dariya tayi tana girgiza kai. Zarah ce ta fara yin gaba bayan sunyi sallama da Umar. Tana zaune cikin mota Ammar ya shigo yana dariya. "What's funny? Ta faɗa idanunwanta a kansa. "Umar ne, don't mentioned, za muje gidan Saude ko mu bari sai wataran? Ajiyar zuciya ta sauke, bata son spoiling good mood ɗin da take ciki a yanzu hakan yasa ta bashi da, "Mu bari gobe sai muje, yanzu na gaji" "Na sani ai dama Hafsat ta tula miki aiki" Dariya Zarah tayi tana fad'in " Doya fa kawai na fere mata, me abun aiki? "Na ji dai, ni yunwa nake ji, and i need something spicy" "Ok kwaɗayi dai kawai kake ji" murmushi yayi me sauti yana mai da hankali kan titi sannan ya ce, "Affirmative" "Na sani ai, muje dai gidan" Gyaɗa kai yayi yana ƙara gudun motar, a jikin kujera tayi relaxing tare da lumshe Idanunta. Bayan sun isa gida a kan gado ta kwanta tana kallon Ammar daya shigo mata da jakar data taho dashi daga gidan Umar.. zama yayi yana fad'in " Duk wannan kayan data baki ne? Itama tashi zaune tayi tana kallon jakar ta ce, "Eh mana" "Well done, duk wannan? Toh me a ciki? "Idon ma tambayi " Ta faɗa tana janyo jakar kusa da ita. "Ok, abin na gulma ne kenan? "Babu dai ruwanka" "ok naji, tashi kije dai kiyi min abinda nace" Da ok ta amsa tana miƙewa ta ɗauki jakar ta saka a closet tare da yi masa gargaɗin kar ya taɓa mata. Bai kulata ba har ta fice, tana fita ya sawa ɗakin key ya dauki jakar, komai sai daya fito dashi yana yi yana dariya, shi sha'anin mata dariya yake bashi, ita ta kai mata modern perfume ita kuma ta haɗota da natives ones ai kuwa sai khamshi suke, harda lemo ya fada a fili yana bude jakar maltinar daya gani, khamshi zuma yaji haka ya sashi faɗin " Oh zuma ce, let me have some" sha yayi dan sosai ta masa daɗi yaji har da dabino a ciki. Rufewa yayi ya ajiye yana ajiye spices ɗin daya gani a leda daban a cikin jakar, knocking Zarah ta fara yi tana fad'in "Ka buɗe zan ɗauki abu" tasowa yayi ya buɗe yana kallonta, ta gefansa ta wuce tana kallon yadda yayi dai² da kayanta. Haɗe fuska tayi tana mai da dubanta gareshi ta ce, "Na ce fa kar ka taɓa min kayana" "Sorry" bata kulashi ba ta dauki spices ɗin da Hafsat ta bata sannan ta fita ta barshi. Zama yayi ya haɗe kayan waje guda, sai da ya kuma shan zumar sannan ya ajiye mata ragowar da niyyar idan sunyi waya da Umar zai ce a kawo masa dayawa dan tayi masa daɗi. Pepper meat zarah tayi masa tare da white couscous ta ɗauki lokacin sannan ta dawo ɗakin tana ajiye tray ɗin hannunta a bedside drawer ta ce, "gashi nan" Tashi zaune yayi yana kallon abincin ya ce, " I don't feel like eating right now, cikina ya fara ciwo" "Ciwo kuma? Cewar Zarah tana zama kusa dashi. "Yeah, ko zumar dana sha ce" "A ina ka sha zumar? Cewar Zarah idanunta a kansa. "Wadda matar Umar ta baki, i think nayi overdosing ɗinta, but as far as I know zuma bata saka ciwan ciki, anyway akwai maganin ciwan ciki cikin drawer dakina ɗauko min" Kasa tashi Zarah tayi sai kallonsa ta ke, ita kanta da Hafsat ta bata tace murfi biyu zata dinga haɗawa da madara tana sha, after 3-4 days ta kuma sha. "Baki ji ba? A hankali ta tashi ta fita, bata daɗe ba ta dawo da maganin, karɓa yayi ya sha yana komowa ya kwanta, Zarah kuwa rufe abincin tayi tana zuba masa idanu. Yau kam taga karshen kwaɗayi a wajen Ammar. Ganin ya rufa da duvet, ta ɗauki wayarta ta fita daga ɗakin, number Hafsat ta fara dialing, bugu biyu ta ɗauka tana fadin " Ya kuka je gida? "Lafiya ba lafiya ba, ina zumar matar nan da kika bani? Toh Ammar ya sha! Ga shi nan dai kwance wai cikinsa yana ciwo" "ke garin yaya? Ai kuwa idan besha da madara ba zai ta zawo, kuma Kema kin shiga uku, hmm ba ruwana! Irin wannan ai ɓoye wa ake inda ba zasu gani ba! Ya shanye ko kuwa? "Ban sani ba dan ban duba ba" Zarah ta faɗa kamar zatayi kuka" "Ni bansan wani taimako zan baki ba Zarah, but is better ki bashi flagly ya sha" da toh Zarah ta amsa tana nufar ɗakinsa direct. Da flagly ta dawo, bata tarar da Ammar a kan gado ba, zama tayi tana jiran fitowarsa, ai kuwa a wahala ce ya fito yana zama a kan gado idanunsa a kan Zarah ya ce, " Dauko min flagly, da sauri ta miƙa masa tana ɗauko ruwa, karɓa yayi yasha yana riƙe kansa, "sannu" ta faɗa tana kunshe dariya, bai amsa ba ya tashi ya koma toilet.. falo Zarah ta fita tana zama a kan kujera, sosai take dariya, a fili ta ce, "Gobe ma idan kaga abinda ba naka ba ka sake ɗauka ka sha" Jin alamar fitowar shi ya saka ta koma ɗakin, be kai ga zama ba ya kuma komawa banɗaki, Zarah na kokarin saita kanta ta nufi kofar toilet ɗin ta ce " Is better ka zauna a ciki har gudawan ya tsaya" Komawa kan gado tayi ta zauna, Shuru tayi tana kallon kofar banɗaki, tausayinsa ne ya kamata, ORS ta ɗauka a drawer ɗinta, Allah yaso tana da ragowar kwalin daya siyo tun lokacin da tayi rashin lafiya, haɗawa tayi tana fad'in " Ka fito kasha ORS, sai ka kara shan flagly ɗin" har ta fitar da ran zai fito sai gashi ya fito yana riƙe ciki, taimaka masa tayi ya zauna sannan ta bashi flagly ɗin ya sha da ORS. "Sannu" kai ya Gyaɗa yana jin jikinsa yayi week, baya tunanin ko laxatives ka sha zai emptying bowel ɗinka kamar yadda wanann zumar take ɗauke masa aiki, "Xarah kar kisha zumar nan, ita ta sani cikin wannan halin" ya faɗa yana kallonta. "Toh" ta amsa tana kallonsa. Haka dai Ammar ya kai har dare yana gudawaa, sai kusan 9 sannan ya samu ta tsaya, sosai yayi weak, drip Zarah ta haɗa tana kallonsa ta ce " Ko roba ɗaya ce ya kamata a saka maka, kayi week sosai" da Ok ya amsa yana miƙa mata hannunsa, daurewa tayi ya dunkule hannunsa ta saka spirited swab ta goge hannun nasa sosai veins suka fito hakan ya saka ta samu damar introducing ɗin butterfly niddle a ciki, kwance hannunsa tayi tana cire iska a cikin ruwan sannan tayi connecting da butterfly niddle din ta saka plaster, ta fara jero masa sannu. Wa she gari da safe ya ɗan ji daɗin jikinsa, amma tunda yayi wanka ya koma ya kwanta kasancewar bai da wani kwari sosai, bayan Zarah ta kammala ayyukanta kusa dashi ta dawo tana fad'in " Ya jikin? Buɗe Idanuwansa yayi yana kallon ta ya amsa da " I'm better Alhamdulillah" Tashi zaune yayi yana sauke numfashi a hankali.. "In kawo abinci? "Me kika dafa? "Your favorite" "Really? Ya faɗa yana ɗan murmushi. "Eh mana, har yajin tafarnuwa na daka maka" tana ƙoƙarin sauka daga kan gadon ya janyo jikinsa yana manna kiss a kumatu ya ce "Allah yayi miki albarka" dariya tayi tana ɗorawa da faɗin " duka wannan murnar ta ɗan wake ce? "Eh amma har da ta soyayyarki" Bata ce komai ba ta bar jikinsa tana murmushi, sosai yaci ɗan waken, bayan ya kammala ta cinye ragowar sannan ta kai kayan kitchen. Ranar ko kofar falo Ammar bai je ba yana ɗakin Zarah, kafin dare yaji daɗin jikinsa sosai, bayan sun idar da sallar magriba wayar Xarah dake kan dressing mirror ta fara ruri, Ammar ne ya ɗauko mata yana fad'in " Hafsat ce" Karɓar wayar tayi da sauri tana katsewa, short SMS ta tura ma ta sannan ta kunna data ɗinta, bata daɗe a kai ba Hafsat ta hau... *_Ya Ammar ɗin?_* message din Hafsat ya shigo. _*Yaji sauki Alhmdll, ya kike*_ Zarah ta tura mata da reply.
_*Ma sha Allah, sai ki kiyaye gaba kuma ko da ya miki maganar zumar kice normal zuma ce kawai dabino aka saka*_ da ok tohm Zarah tayi ma ta reply sannan tayi offline tana clearing din chat din. Kallon Ammar tayi da tun ɗazu Ita yake kallah. Murmushi tayi masa tana cewa " Yau ana ɗan sanyi²" "Ba sai kin wayance ba, kawai kice inzo mu kwanta kiji dumin Mijinki" Dariya ya bata hakan yasa ta dara kaɗan tana kallonsa ta ce, "Kai dai kawai zaka min wayo" Bai ce da ita uffan ba ya dawo kusa da ita yana kallonta ya ce, "Yi min waƙa" Cike da mamaki ta ce, "Waƙa? "Yes! Ya bata amsa yana shafa kansa. "For heaven sake kawai sai na fara waka? "Ok bazakiyi ba? "Ni dai ban iya ba" ta faɗa tana juya masa baya. "Its okay,ni bari nayi Miki" Juyowa tayi tana kallonsa ta ce, "Really? Kai ya Gyaɗa alamar eh. Gyara zama tayi tana fad'in " Ina jinka" Gyaran murya yayi yana faɗi " Fati, Fatima autar mata, a raina babu yake har kullum" Dariya Zarah tayi tana kallon sa da kyau ta ce, "A ina ka iya waka? "Sa wasa, bari na sake miki wata" vd ta fara yi masa Ammar be fasa ba ya fara yi mata waka wanda yawanci ma ba dai² yake yi ba, sosai kam ya bawa Zarah nishadi... Wayar hannunta ya karɓa yana ajiyewa ya ce, "tunda baki iya waƙa ba yi min karatun Alkur'ani" Murmushi tayi me kyau tana kallonsa tare da yin gyaran murya, very soft and calm ta yi a'uzu da Bismillah, sannan ta fara karanta cikin baƙara shafin wattaba'u, rabin shafi tayi sannan ta buɗe idanunta data lumshe saboda shauƙin karatun Alkur'ani mai girma, waya ta gani a hannunsa yana mata vd. Murmushi tayi me kyau tana fad'in " Baka ce min zaka min vd ba" "Kuma kinyi kyau, ƙirar'ar tayi min daɗi Malama Fatima" "Tnx" ta faɗa tana kallon vdn da yayi mata. A masallaci yayi sallar Isha'i. Bayan ya dawo ya tarar har ta kwanta ta kashe fitilar ɗakin. Sleeping wears ya saka yana kwanciya a gefenta. Buɗe idanunta tayi tana fad'in " Naga ka daɗe" "Na tsaya wajen Rabi'u ne" Ya bata amsa yana Janyota jikinsa. Jin Yadda ya riketa ya saka ta kallon fuskarsa gently ta ce, "What's wrong? " Nothing, i just love you" ɗauke idanunta tayi daga cikin nashi tana sauke numfashi a hankali, tare da juya masa baya, hannunsa ya saka cikin rigarta yana shafata, shuru Zarah tayi tana jin tsikar jikinta na tashi, heartbeat ɗinta na ƙaruwa, juyowa tayi tana kallonsa, shima kallonta yake, launin Idanuwansa har sun fara sauyawa, veins din dake kansa sun kara girma. Lumshe idanu tayi tana jin fargaba a zuciyarta, tun kafin aje ko ina Ammar yayi observing changing a tattare dashi, he feels so happy and blessed, that night is unforgettable for the both of them, especially ma Ammar da yake ji kamar mafarki yake yi, he almost fainted, he never experienced such kind of enjoyment before, abinda yaji is undescribable, lokacin da ya daɗe yana mafarkin ya tarar dashi, even though this is not his first time but this feel so different, maybe dan Zarah is the love of his life, kuma the only woman he wants to be with... Tun da ta fito daga bathroom take avoiding haɗa idanu da shi. Wardrobe ta nufa ta ɗauki night gown ta saka, gefan gado ta dawo ta zauna tana tsane ruwan kanta da towel ɗin data nannada a kanta. Hugging ɗinta yayi yana murmushi ba tare da yace komai ba. "Zan kwanta" Ta faɗa tana ƙoƙarin raba jikinsu. Juyo da ita yayi yana kallon cute face ɗinta ya ce, "Allah yayi miki albarka Zarah" kasa amsawa tayi. Light kiss yayi mata a lips ɗinta sannan yaja duvet ya rufesu. Wa she gari da safe around 11 Zarah ta farka, dubanta ta mayar kan shi, bacci yake abinsa, bathrobe din jikinta ta gyara tana sakkowa daga daga kan gado. "Jiya komai ya faru kamar a mafarki! Toh what's wrong with him? Ko dai yana da iska? Kai ta girgiza da sauri tana fad'in " Ba haka bane, amma kuma idan ba haka bane meyasa tun farkon aurensu komai baya tafiya dai²? Bata da amsoshin tambayoyinta hakan ya saka ta wuce banɗaki.....Ƙarar wayarsa ce ta farkar dashi daga daddaɗan baccin da yake yi, ɗauka yayi ba tare da ya duba me kiran ba. "Ammar" Ya ji Muryar Maminsa. "Mami, ina kwana" Ya faɗa yana tashi zaune. "Lafiya lau, lafiya dai kwana biyu baka zo ba? Kuma yarinyar nan Bilkisu tana complaining a kan bleeding ɗin da take yi da ciwan ciki is better kazo ka ɗauketa kaje ka dubata da kyau, gynecologist ne kai ban ga amfanin cewa matarka tana wahala ba ka banzatar da ita haka ba" "Sorry Mami, zanzo anjima bana jin daɗi ne" "Me ya sameka? Ta tambaye shi with so much of concern. "Diarrhoea" ya bata amsa. "Eyya, sannu, ya jikin yanzu? "Naji sauki Alhmdll in sha Allah anjima zanzo" Da ok Mami ta amsa tana nasa addu'ar Allah ya kara lafiya. Da Amin ya amsa sannan su kayi sallama. Zarah ce ta shigo tana ajiye tray ɗin hannunta a kan gado ta ce, " Ga abinci" Ba tare da ta kalleshi ba. "Ok, I'm coming" Ya faɗa yana tashi, toilet ya shiga bai daɗe ba ya fito, zama yayi a gefanta yana fad'in " Thanks" bata ce komai ba ta dawo masa da abincin kusa dashi. Tea ta haɗa sannan debo masa faten dankalin turawa da yaji kifi da alayyahu sai ƙhamshi yake, loma ɗaya yayi ya lumshe idanusa sannan ya buɗesu a kanta ya ce, "jiya kin bani daɗi yau ma ga wani ko? "Ammar! Ta kira sunansa kunya duk ya kamata" "Yes! Ai ba karya nayi ba, i really enjoyed yesterday night, and I'm not yet tired" "Nifa bana so just keep shut" "No way, dole nayi magana, duk wannan kunyar ma ki ajiyeta! Anjima ki shirya zamu je gida" "Toh" ta amsa ba dan ranta ya so ba amma bata nuna a fuska ba.
"Good, meyasa bakya cin abinci? "Oh sai yanzu zaka tuna bana ci? "Sorry, let's eat" "Naci bread and tea na ƙoshi, bari na je na gyara gidan kafin ka gama" "Ok" Ya amsa yana bin ta da kallo har ta fice. By 2pm suka fito cikin shirin fita, basu ɗau lokaci ba suka isa gidansu Ammar, shi ya fara sakkowa sannan ita, ko da suka shiga falon gidan basu tarar da kowa ba sai TV dake ta aiki ita ɗaya, Maryam ce ta fito daga ɗakin Mami tana sanye da uniform na islamiyya.. "Ban hana ku barin TV a kunne ba idan ba kallo ake ba? Cewar Ammar yana kallonta. "Aunty Fa'iza ce wallahi" Maryam ta amsa. Bai ƙara cewa komai ba hakan ya saka ta bar wajen da sauri. Kwafa yayi dan yaga alamau sai ya saita yaran akan rashin kirkin da suke gwadawa matarsa abun har da Maryam itama sun fara kitsa mata ba gaisuwa ba sannu. Sakin hannun Zarah yayi yana kallon ta ya ce, "Zauna ina zuwa" Da ok ta amsa tana zama a kan kujera. Ammar be wani daɗe ba suka fito tare da Bilkisu dake sanye da uban hijabi, duk ta rame ta ƙara haske, "Zarah ki shiga ku gaisa da Mami sai ki fito mu tafi" "Toh" Zarah ta amsa tana miƙewa.. a zaune taga Mami ita da ƙanwar Umar kamar dai lissafi ma suke yi ganin biro da takarda a hannun Fa'iza. Har ƙasa ta tsugunna ta gaishe da Mami. Babu yabo babu fallasa ta amsa tana tmbyrt y gdn. Da Alhamdulillah tana ɗorawa da faɗin "Allah ya sanya alkhairi bikin Fatima ya matso Allah ya basu zaman lafiya" Da Amin Mami ta amsa. Dubanta ta mayar kan Fa'iza ta ce, "Sannu" Da yawwa Fa'iza ta amsa ko minti ɗaya Zarah bata ƙara ba ta fito, bata ga Ammar da Bilki a falon ba hakan ya saka ta fita waje, a cikin mota ta gansu da alama magana sukeyi ganin idanun Bilkisu da hawaye kuma tana ɗaga hannu kamar dai rantsuwa ma take, ƙarasawa tayi ta buɗe Back seat zata shiga amma Bilkisu tayi saurin juyowa tana fad'in "Wai dama da ita zamu tafi? "Eh, me aibun haka? Cewar Ammar yana kallonta. Goge hawayenta tayi tana fad'in "Babu dama kenan ni nayi sirri da mijina asibitin ma da za'a kaini dan gulma sai kin biyo mu? Ganin Ammar bai ce uffan ba ya saka Zarah haɗiyar yawu me daci ta rufe murfin motar ba tare da ta shiga ba, kallon Bilki ta yi ta ce, "Aje ayi sirri da miji, Allah ya kara sauƙi" daga haka ta nufi bakin gate. Sakkowa Ammar yayi yana kiran sunanta, tsayawa tayi tana aro murmushi ta ɗora a kan fuskarta.. "Dr Ammar kar ka wani damu, zan wuce wajen Saude kawai" "Ok muje sai na sauke ki" "No need! "Ok da shekarunki zaki hau napep ɗin? Ya faɗa yana kamo hannunta. Kwace hannunta tayi da karfi tana ɓalla masa wata uwar harara sannan ta ɗora da faɗin " Maybe zan biya da shekarun nawa" Daga haka ta wuce ta barshi. Tsakin takaici yayi yana komawa mota, gate me gadi ya buɗe masa, kallon Bilkisu yayi ya ce, "Ke baki da lafiya ma bazaki iya hakuri ba? "Ai gaskiya na faɗa! Ta tafi duk inda zata je! Duk wannan kwanakin da take tare da kai basu isheta ba sai ɗan lokacin nan da zan kasance da mijina sai ta wani biyoka kamar ƴar yaye?! "is okay, don't say alot! Cewar Ammar yana danna giyar motar ya gurza taya dai² inda Zarah ta tsaya. Nunfashi kawai ta sauke dan ta ɗauka take ta zeyi. Fitowa yayi yana haɗe rai ya ce, "Shiga mota" "nifa babu inda Zanje, wai na baku guri ne kuje kuyi sirri" Daga haka ta barshi a wajen. "Dan Allah kazo mu tafi bana jin daɗin jikina fa! Cewar Bilkisu daga cikin mota. Bin bayan Zarah yayi yana riƙo hannunta ya saka mata kuɗin mota ya ce, " Kar ki zauna Please kafin magariba ki koma gida, take care" Gyaɗa kai kawai tayi, shi kuma ya koma mota, bin ta yayi tayi a baya har sai daya ga ta tsari Napep sannan ya ɗau hanyar asibiti Bilki kuwa ji tayi kamar ta shaƙe shi dan haushi......Autarmama ce.