Chapter fourteen

424 35 32
                                    

✨ *MATANA* ✨

*Mallakar*
      AUTAR MAMA

*FREE BOOK*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*

*Comment*
*Vote* &
*Share* Fisabilillah

*Masu nema daga farko kuyi min mgn ta wannan number 08142904255! But bani da pages idan kinsan bakya son document sai dai ki duba Wattpad!*

*014*

     Knocking din ƙofar da akeyi ne yayi waking dinta daga baccin da take, "Shigo! Ta faɗa tana mitsika idanunta.. Mustapha ne, jikinta ta rufe da duvet tana kallonsa. Rufe kofar yayi yana karasowa inda take ya ce " Baki tashi ba kenan? "Uhm! Ta amsa masa. "Ok, ki sameni a falo! Daga haka ya fita. Bacci ta koma sai 11 sannan ta fito.. Ummi ce kawai a falon tana kallo. Karasawa tayi tana fad'in " Ina kwana Ummi? "Lafiya lau, ansha bacci, Mustapha sai jiranki yake wai zakuyi magana har ya gaji ya koma daki" Uhm kawai ta ce tana ɗorawa da faɗin " Ina Zainab da Farida? "Duk suna daki" Da ok ta amsa tana zama. "Baku da wani shiri akan bikin? Kamar dai event haka? Cewar Ummi idanunta akan Zarah. "A'a Ummi amma bansani ba ko shi yayan" "Ok sai kuyi maganar bari na kirashi" daga haka ummi ta tashi ta nufi dakin Mustapha.. bata dade ba ta fito ta wuce dakinta. Ita dai Zarah tasan duk son jan magana ne wannan.. a kujerar da ummi ta tashi ya zauna fuska ba walwala ya ce " Kin tashi kenan" "Eh ina kwana? Ta fada kanta a ƙasa.. Numfashi ya sauke a hankali yana kallonta kafin ya ce, "Haryanzu kuna tare da Ammar ko? Kai ta girgiza alamar a'a. Murmushi yayi kadan yana dawowa kusa da ita tare da miƙa mata wayarsa ya ce, " And this?  Kallon wayar tayi taga picture dinta ne tare da Ammar.. "a ina ka samu wannan? "Bani kadai ba kusan kowa ma yana da wannan a Wayarsa tunda a social media akayi posting dinsa, what is the meaning of all this Zarah? Nifa bana so inyi auren da zanzo ina dana sani, inaso nayi auren kwanciyar hankali, inaso na samu macen da zata kula dani ta bani farinciki, idan kinsan baxaki iya ba just tell me! Zansa yadda zanyi wa su Ummi bayani" Shuru Zarah tayi dan bata san me zata ce masa ba. Numfashi ya sauke yana dago da fuskarta suka fara kallon juna, sauke idanunta tayi zuciyarta na bugawa, tabbas Mustapha ma bashi da wata makusa amma bata sonsa ta yaya kuma zata iya budar baki ta faɗa masa? "Bakya sona ko Zarah? Kai ta girgiza da sauri alamar a'a. "Ok kin yarda zaki aureni? Kai ta daga alamar eh. "Shikenan kiyi min alkhawarin bazaki kara kula Ammar ba! Insha Allah kafin ki koma za'a daura auren" da sauri ta kalleshi.. hannunta ya kamo yana kallon fuskarta ya ce, "Inshallah, bayan hutun 2nd semester dinku sai ki tare, bazan iya jira har nan da wata daya ba" Kai ta gyada masa alamar toh. Da sauri ta tashi ta wuce daki tana jin zuciyarta na zugi. Numfashi ya sauke kafin shima ya tashi ya nufi dakin Ummi. Kansa a ƙasa ya karasa yana zama a kusa da ita.. "Lafiya dai ko? Cewarta. "No Ummi, please if possible a dawo da daurin auren nan next week" "Saboda? Ummi ta fada cike da mamaki. "Kawai so nake a daura kafin su koma makaranta, ina ganin kamar idan ya wuce haka bazan aureta" Ajiyar zuciya Ummi ta sauke tana dafashi ta ce, "Fada min me Zaran tayi? "Babu abinda tayi" Ya fada ba tare da ya kalli ummin ba. "Ok zanyi wa mahaifinka magana, Allah yasa hakane yafi Alkhairi" Da Amin ya amsa sannan ya tashi ya fita.

      Tun daga wannan ranar Zarah bata kara wani lafiya ba, amma a cewar Ummi ai duk wata amarya haka take idan bikinta ya matso, sosai ake gyara Zarah, wani kyau na musanman tayi, ita kanta tafi jin dadin jiki ta yanzu, ko falo bata fitowa kullum tana daki komai sai dai akai mata, cikin one week tayi wani bala'in kyau kamar ba ita ba, ko abu ta rike khamshinta sai ya kama wajen. Yanzu ma ita daya ce a daki fitowar ta daga wanka kenan, me gyaran jiki bata dade da fita ba. A gefan gado ta zauna tana jin kanta na ciwo.. wayarta dake charji ta cire kasancewar ta cika.. kiran Waheeda ta gani har biyu. Zata kirata wani kiran ya shigo, dauka tayi tana fad'in " Anata shan biki" Dariya Waheeda tayi kafin ta ce, "Eh wallahi yau ai za'a fara, yanzu ma muna salon ni da Aunty Hafsat, ya kike an manta dani" murmusawa kawai Zarah tayi. "Toh ya zaki zo ɗin ne? Cewar Waheeda daga dayan side din. " A'a! "Kai Zarah! Waheeda ta fada kamar zatayi kuka.. idanun Zarah na cikowa da kwallah ta ce, " On Sunday fa za'a daura min aure" "Keee Zarah! Waheeda ta fada cike da mamaki. "Ba wasa ba, bana fada miki da saura wata daya ba? Toh yanzu an rage saura 2 days" "Allah sarki, Allah ya bada zaman lafiya Zarah, nidai shawarar da zan baki ki kwantar da hankalinki ki rungumi mijinki Allah ya baku zaman lafiya"  da Amin zarah ta amsa sannan sukayi sallama. Goge hawayenta tayi, inshallah zatayi biyayya duk da cewa tasan hakan abune mai wahala a gareta. Farida ce ta shigo room din tana cewa " Zarah ga abinci, kuma Ummi ta ce kije dakinta kiga lefanki! Yarinya kin chaba su Yaya anyi kokari" Murmushi Zarah ta aro ta dora a lebanta ba tare da tace komai ba.. fita Farida tayi, ko abincin bata ci ba ta saka hijabi ta fito har ta manta rabon data fito falo.. dakin Ummi ta nufa, bakinta dauke da sallama ta shiga.. Mustapha da ummi ne a ciki suna magana.. "Shigo ki zauna! Cewar Ummi ganin zata tafi. Sunkuyar da kanta tayi ta karasa cikin dakin. A gefan gado ta zauna tana kallon akwatunan dake gabansu kusan 12boxes. "Gobe idan Allah ya kaimu sai kaje ka dauko su Innar, sannan ƴaƴan ƙanin mahaifinku ma zasu zo daga England da yamma sai kaje ka daukosu daga airport, dole sai kayi hakuri goben nan, akwai sauran cards a wajena anjima zaka sauke su Farida zasu rabawa wadanda ba'a karasa bawa ba" "Toh insha Allah" Mustapha ya amsa yana satar kallon Xarah. "Toh tashi kaje mana" cewar Ummi tana kallonsa. Shafa kansa yayi kaɗan yana tashi ya ce, "Zarah idan kin gama ki kawo min abinci" "Xansa Farida ta kawo maka" Murmushi yayi yana kallon Ummi dake harararsa. Fita yayi yana murmushi.. dubanta ta mayar ga Zarah ta ce, "Ga kayanki nan sakko ki duba" a sukwane ta sakko tana kallon kayan, ita ta rasa me zatayi farinciki ko bakinciki? A sanyaye ta ce, "Nagode Allah ya saka da Alkhairi ya kara budi ummi" "Amin, amma babu ko sisi na a ciki tashi ki kai masa abinci sai kiyi masa godiya" "Toh" ta amsa tana miƙewa.. ta daɗe a kofar dakinsa rike da tray amma ta kasa shiga, da kyar dai ta tura kofar tana yin sallama.. yana zaune a kan sofa yana kallo a TV. Ajiye remote din hannunsa yayi yana tashi tsaye ya karbi tray din hannunta ya ajiye akan table. Durkusawa tayi kanta a sunkuye ta ce, "Nagode Allah ya kara budi"  "Amin Zarah" A sanyaye ta miƙe zata fita yayi saurin tsayar da ita da fadin "Ok kin kawo min abinci bazakiyi serving dina ba? Bata ce komai ba ta juyo ta nufi wajen table din ta zuba masa abincin a plate sannan ta tsiyaya masa ruwa, duk abinda take ko sau daya be dauke idanunsa daga kanta ba. Ita kuma bata yarda ta kalleshi ba. "Gashi nan" "Ok, zauna muci tare ko? Kai ta girgiza tana kokarin tashi ta ce " Naci nawa ai" "Ok musu zaki fara yi dani kenan tun kafin ayi auren? Kai ta girgiza alamar a'a. "Ok just do as I say! Bata ce komai ba ta koma ta zauna tana daukar spoon. Tsakurar abincin kawai take yi, duk abinda takeyi yana kallonta. "Ranar daurin aure kinsan za'ayi dinner ko? Banga kina planning komai ba, Farida ta ce min ko weeding dress baki zaba ba? Ain't you happy? "Ni fa kawai bana son wannan event din, da kayi shawara dani da ba'ayi booking ba" "Ok kiyi hakuri ai ba dadewa za'ayi ba kinji ko? Kai ta gyada alamar toh. "A..am..Amma dai anan gidan zan cigaba da zama ko? Ta faɗa muryarta na dan rawa. Sai da yayi murmushi sannan ya ce, "Of course no! Gidanmu zamu tafi" "kai fa kace baxan tare ba sai mun gama second semester examination" Kai ya girgiza yana faɗin " Kafin ku koma hutu zaki tare ai, ko bakya so? Da sauri ta daga kai alamar eh. "Saboda me? Shuru tayi dan bata da amsar wannan tambayar. "As you wish ma'am, baki da damuwa" Murmushi tayi kaɗan tana tashi tsaye ta ce " Na tafi" Bata jira cewarsa ba ta wuce. Nunfashi yaja me karfi yana jin khamshinta har cikin zuciyarsa.. daki ta koma ta saka key.. online ta hau ko zata debewa kanta kewa... *_Aslm Aunty ya kike ya shirin biki? Inna tace gobe zamuzo ai, ina fatan kin kwantar da hankalinki?_* sakon Saude ya shigo.. budewa tayi ta karanta kafin tayi reply da *_Eh Saude Allah ya kawoku lafiya, ki taho min da gyadar Inna_* kasancewar bata online bata yi mata reply ba. Dm din Ammar ta shiga, just few minutes da yin offline. Sako ta tura masa sannan ta sauka daga online din tana ajiye wayar zuciyarta tayi mata nauyi. Tana fatan hakan shine Alkhairinta. Washe gari da safe suka wuce salon, sai bayan azahar suka dawo, me gyaran jiki tayi aikinta sannan ta tafi, gaba daya zarah ta gaji ga gidan an fara baki, tana kwance har bacci ya fara daukarta ta jiyo Muryar Inna tana fad'in " Ai sai dana tashi da tsayuwar dare wallahi tallahi! Na faɗa miki fa ba haka shegan yaron ya barta ba, ai gwanda ma da aka matso da bikin ayi kowa ma ya huta! Tashi tayi daga kwance tana daukar wayarta ta fito falon. Saude na ganinta ta nufeta ta rungume tana fad'in " Kinga yadda kika yi kyau sai wani khamshi kike? Murmushi tayi tana kallon jan lalle saude ta ce, "Kinsha kyau! Dariya Saude tayi tana cewa " Ya bakiyi lallen ba? Kinga har kitso da nayi, bakiga rigata ba ta dinner! "Saude an samu abinda akeso! Zarah ta faɗa tana karasawa cikin falon... Gaida Inna tayi, itama sai yaba kyan Zarah takeyi.. "Ga kaya chan waje guda innarki ta kawo har da engine wanki" Cewar Ummi tana nuna mata compound din gidan.. "Yanzu zansa a shigo dasu sai ki gani" murmushi Zarah tayi tana kallon Inna ta ce, "Nagode innarmu! "Amarya, kinsha kyau, ina shi Mustaphan ne? Tunda ya kawo mu ya shige daki kamar amarya! Dama sai da na miki addu'a Allah ya baki dan Habuja gashinan ya baki Mustapha dan albarka" Inna ta kuma fada tana washe baki. "Inna Abuja fa ba Habuja ba! Cewar Saude tana dariya. "Naji dai! Dariya sukayi gaba daya.. Bayan Zarah ta koma daki ita da Saude 37missed calls ta gani na Ammar.. sai da gabanta ya fadi.. dialing numbersa tayi bugu uku ya dauka yana sauke ajiyar zuciya ya ce, "Ina kika saka wayarki Zarah? "Sorry tana silent ne! "Ok, are you serious abinda kika turo min a Whatsapp? "Eh fa" Tana jinsa yana furta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun.. daga bisani ya ce " Allah ya sanya alkhairi zarah! Bai jira cewarta ba ya kashe kiran. Kallon ta Saude tayi tana fad'in " Ammar ne ko? Zarah bata iya cewa komai ba ta shiga toilet da sauri tana fashewa  da kuka. "Allah yasa hakane yafi Alkhairi Aunty" cewar Saude cike da tausayinta. Bangaren Ammar kuwa ji yayi komai ya tsaya masa, yadda yake jin zuciyarsa tana zafi da radadi yana tunanin komai zai iya faruwa, kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun ya dinga maimaitawa.. kansa wani mugun ciwo ya fara yi masa.. Rike da plate umar ya shigo dan dama abinci yaje siyo musu saboda Ammar yace bazaici abincin gidan biki ba. "Bro lafiya dai? Kai Ammar ya girgiza masa yana tasowa ya iso inda yake ya ce, "Two days to her wedding! Cike da rashin fahimta Umar ya ce, "Wacece? Shuru Ammar yayi yana yi wa kansa mazauni akan gado kansa na wani irin ciwo. Ajiye plate din hannunsa yayi yana zama kusa da Ammar din cike da tsantsar damuwa ya ce, "Kayi min bayani mana meyafaru? "Bikin Zarah! Ajiyar zuciya Umar ya sauke yana dan dukan bayansa ya ce, "Sorry Man, Allah yasa hakanne yafi Alkhairi just pray for the best, ka kwantar da hankalinka, Allah ya tsara hakan tun kafin kuzo duniya, just thank him kaji ko? Damƙe gashin kansa yayi da karfi yana jin zuciyarsa na suya da radadi.. "Ammar me haka? Just calm down mana! "Bazaka gane ba Umar, I really love that girl, I'm madly in love with her, Umar dan Allah ka kaini ABUJA Please! "Ammar ka kwantar da hankalinka, ya kake abu kamar ba namiji ba? Ta ina zan fara tafiya kaika Abuja? Ko ka manta aurena akeyi? Kai Ammar ya Girgiza yana rike hannun dan uwansa ya ce " Alfarma zakai min Umar Please! "Toh wai tsaya idan na kaika ABUJan tsayar da auren zakai ko me? Tashi Ammar yayi yana gyara wuyan rigarsa ya ce, "Is ok I will manage! Daga haka ya fita, da sauri Umar ya bi bayansa, airport Umar ya kaishi yayi masa booking din urgent flights zai tashi nan da 20mins.
Ammar ji yake kamar 20mins din bata lokaci ne, gashi ya kira wayar Zarah bata dauka ba.. sai da jirginsu ya tashi sannan Umar ya koma gida, shi baisan wani irin so Ammar keyi wa Zarah ba! Bayan saukarsu da kyar ya iya kawo kansa gidansu Mustapha saboda ciwan kai.. banda hasken wutar lantarki babu komai a layin. Knocking din kofar gidan ya fara yi, gate man ne yayi saurin budewa.. shigowa Ammar yayi, a bencin me  gadi ya zauna yana dafe kansa.. "Lafiya malam? Cewar gateman yana kallonsa.. Ammar be iya amsa masa ba sai lumshe idanunsa da yayi yana sauke ajiyar zuciya a hankali.  Ruwa me gadi ya dauko masa a daki yana fad'in " Sannu" kadan yasha ruwan yana kallon gateman da jajayen idanunsa ya ce, "Inason ganin Mustapha" Sai yanzu gate man ya ganeshi, aikuwa da sauri ya nufi cikin gida, bai daɗe ba ya fito yana fad'in "Gsshinan zuwa! Tunda Zarah taji an ambaci abokin Mustapha wanda yazo kwanaki ta kasa samun peace of mind.. mayafin Zainab ta karba ta faki idanun jama'ar falon ta fito ko takalmi babu.. kafin ta karasa inda yake taji Mustapha ya kira sunanta. Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba, shi ya karaso inda take yana cewa "Ina zakije? Kinganki kuwa? What's this? Have you seen your outfit? Kuma kike roaming a compound? Koma ciki! Ya ƙarashe maganar ransa a dan bace, dan silky dress ce a jikinta tayi kyau sosai. Kasa motsi tayi ta zuba masa idanu. Tunda Mustapha ya kira sunan Zarah hankalin Ammar ya kai kansu.. kasa dauke kansa yayi daga kallonsu wani irin kishi na damun zuciyarsa.. da kyar ya taso ya nufo inda suke, with cracking voice ya ce, "Zarah! Kirjinta na bugawa ta juyo tana Kallonsa hawaye na zubowa akan kuncinta.. rai Mustapha ya haɗe yana kallon Zarah ya ce, "Koma cikin gida! Kai ta shiga Girgizawa a hankali tana jin kamar tabi Ammar su tafi. "Ki wuce nace! Ya sake faɗa cikin tsawa. Nan ma ko motsi batayi ba, idanunta cikin na Ammar. Riƙo hannunta Mustapha yayi yana fad'in " Are You deaf? Kuka ta fashe dashi tana kokarin kwace hannunta daga na Mustapha.. wani abu me daci Ammar ya hadiya yana kallonta ya ce " I told you already, but gonna repeat my self again! I love you, but i wish the best for you, i can't stop loving you till my last breath Zarah' Karfin kukanta ne ya karu tana kallonsa tana jin kuma tsanar Mustapha a zuciyarta dan yanzu gani take shine silar rabuwarta da Ammar. Janta yayi har  garden, ya bude kofar garden din da zata sadaka da verandah din dakinsa ya turata ciki ya kulle. Haryanzu Ammar yana tsaye inda ya barshi.. "Wallahi idan na ƙara ganinka kusa da gidan nan yan sanda ne zasu rabani da kai! Kayi aure ai? Kaje ka rayu da matarka! Yanzu Zarah ta maka nisa! Tunda baka da bakin da zaka iya kwatarwa kanka farinciki lokacin da ake shirin rabaka dashi toh yanzu ma kana ji kana gani zan aureta! Ammar baice komai ba ya sauke wata iriyar ajiyar zuciya yana kallon Mustapha. "Get out! Mustapha ya faɗa da ƙarfi. "Thanks! Itace kalmar da Ammar ya furta sannan ya juya ya tafi. Yana fita Mustapha ya karasa wajen me gadi yana kallonsa ya ce, "Duk ranar daka kara barin wannan mutumin ya shigo a bakin aikinka! Daga haka ya tafi ya bar wajen. Daki ya koma ya buɗe verandah ta ciki, a durkushe ya ganta tana kuka.. karasawa yayi inda take ya durkusa yana fad'in " Zarah wai baki da zuciya ne? Kin manta bak'ar wahalar da kika sha akansa? Anyway tashi ki fita karsu Ummi su nemeki" Tashi tayi zata fita ya rikota yana kallon cute face dinta ya ce "Dan Allah ki bani gurbi me girma a zuciyarki na gwada miki kalar tawa soyayyar" Wani shegan kallo ta masa tana son kwace jikinta. "Relax Zarah, daga gobe fa Shikanan u'r all mine, kuma Nima I'm all yours insha Allah, but inaso ki cire duk wani past dinki ki karbeni kinji ko? "Naji! Ta faɗa a ƙufule. Sakinta yayi da sauri ta fita ta barshi ranta duk a bace.. dakinta ta koma, taci Sa'a ba kowa, wayarta ta cire a charji ta shiga call logs ta danna kiran layin Ammar.. har ta tsinke be dauka ba. Sake kira tayi, sai data kusa tsinkewa sannan ya dauka. Shuru tayi zuciyarta na tsananta bugu. " Zarah! Ya kirata da wata iriyar murya kamar me bacci.. "ka tafi? Ta faɗa a sanyaye.. "No, Ina kofar gidanku I'm not feeling ok zan huta kafin na tafi zan kama hotel kafin gobe" "Ok wait for me! Daga haka ta katse wayar. Cikin drawer ta dauka PCM da ruwa ta fito tana rarraba idanu.. "Zarah ina zuwa? Ta jiyo Muryar Inna.. juyowa tayi tana dan yin yake ta ce, "Yaya zan kaiwa magani" "toh karki zauna! Bata amsa ba ta nufi hanyar dakin Mustapha, tana ganin inna ta wuce ta fito da sauri ta fice.. ko kula gate man batayi ba ta fice, kalle² ta fara yi, chan ta hangoshi tsaye yana gyara wuyan rigarsa.. karasawa tayi da sauri tana fad'in " Ammar! Juyowa yayi ya kalleta dan beyi tunanin dgsk zuwan zatayi ba.. maganin hannunta ta miƙa masa da ruwa, karba yayi yasha yana ajiye ragowar ruwa idanunsa cikin nata.. sosai ta tausaya masa ganin yadda yayi.. "Kayi hakuri! Ta faɗa tana sauke idanunta daga nashi. Janyota yayi yana rungumeta tsam, bugun zuciyarsa na kara karfi sosai.. "Ammar sakeni a waje ne fa! Ta faɗa tana kokarin raba jikinsu.. "I can't Zarah! Zarah i love You Please don't leave me Dan Allah! "Bani da zabi Ammar, amma kaine ka fara barina, You could have say no to them maybe da duk wannan baya faruwa yanzu" "Na sani Zarah, amma a lokacin Mami na ta dau fushi sosai babu yadda na iya dole na amsa mata" "Shikenan, Allah yasa hakane yafi Alkhairi" Zarah ta fada a sanyaye. Dago da fuskarta yayi yana kallon ta ya ce, "Do something mana! Zarah Dan Allah kiyi wani abun" "Babu abinda zan iya! Ta amsa masa tana kuka. "Zaki iya indai son da kike min gaskiya ne, Zarah karki bari kiyi auren nan, ina miki son da bazan iya misalta miki ba! Banaso kiyi aure kuma ya zamana na kasa rabuwa dake, yazo kuma muna haramtacciyar mu'amala" Raba jikinta tayi da nashi tana kallonsa ta ce, " Baxan iya komai ba Ammar, idan nayi wani abun Ummi zatayi fushi dani, haka ma Daddy, kowa ma zai yi fushi nasan kuma zan bata zumuncin dake tsakanina da yan uwan mamana, bazan iya ba! Jiki ba kwari Ammar ya durkusa bisa gwiwowinsa yana riƙo hannunta ya ce, "Dan Allah Zarah! Itama durkusowar tayi tana kallonsa hawaye na zubowa kan kuncinta zuciyarta na zafi da radadi.. hasken fitilar mota ce ta dallaro su.....

Sorry for the late update yau na Dan shiga busy ne

Autarmama ce

MATANA ✓Where stories live. Discover now