Chapter Three

703 34 7
                                    

✨ *MATANA*✨
 

*Mallakar*
       AUTAR MAMA

*FREE BOOK*

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

*Wannan labarin ƙirƙirarre ne, banyi shi ɗan cin zarafin wani ko wata ba! Sannan idan yayi shige da labarinka/labarinki coincidence ne Yawwa*

*Comments share and vote dinku yana da matukar mahimmanci idan yayi karanci zan maida abuna ba kudi💃*

*Whatsapp group females only please*

https://chat.whatsapp.com/Ib3gwXORbTB1GxcVr0FdAw


*003*

        Ƙosawa yayi da kukanta dan ta dameshi kidan ma dake tashi a motar bata barinsa yaji dai-dai.. a ɗan hassale ya ce " Ya isa mana! Da sauri ta hadiye kukan da take yi dan kaɗan daga aiki Yaya Musty ya kwadeta. Tsaki yayi kaɗan yana fad'in " Muje gida kicewa Ummi akan saurayi kike wannan kuka ta daka ki! Saurayin naki ma mummuna" Ita dai bata ce komai ba sai goge idanunta da takeyi amma hawayen sunki tsayawa.. "Please ki kwantar da hankalinki, life is full of challenges mostly aure da kika anyi shi toh idan kika bincika zakiji ire-iren wannan, u'r fine enough to find someone better than him! Dan iska dashi, raina miki hankali ma yakeyi da yake cewa auren dole za'a yi masa, ke kin taba ganin inda akayi wa ƙato auren dole? Ai ko a wasan kwaikwayo ban taɓa gani ba, bazai iya budar baki ya ce baya so ba? Uban waye zai zauna masa da ita? Ke! Hmm kyale namiji mugun munafiki ne" Ita dai bata ce masa komai ba amma tana ta juya maganganunsa a zuciyarta, ta wani fanni gaskiya yake faɗa ma ta amma idan haka ne meyasa Ammar zai shigo rayuwarta bayan yasan ba aurenta zaiyi ba? Mustapha be kara ce da ita komai ba. A traffic suka tsaya.. masu tallah sai tallan kayan ciye² suke musu, dubansa ya mayar gareta yana fad'in " Zakici wani abu ne? Kai ta girgiza a hankali alamar a'a. Taba baki yayi ya sauke glass ƙasa ya siyi abinda zai siya.. juyowar da Zara'u zatayi taga motar Ammar, zaro ido tayi tana karewa motar kallo, da sauri ta sauke glass dan ta kara tabbatarwa saboda tinted glass ne is not clear sosai.. four eyes sukayi dashi.. Mustapha be lura ba yana tuki dan an bada hannu.. a sanyaye ta daga glass din sama tana kwanciya a jikin kujera zuciyarta na bugawa da ƙarfi.. Tafiyar 5hrs sukayi maimakon 6 saboda yadda Musty yake zuga gudu.. 8pm suka isa garin Abuja.. Gidan da Musty ya tsaya yana horn gida ne me kyau da tsari duk da cewa ba wani fankacece bane amma ya hadu dan an tsara shi.. gateman ne ya bude gate sannan ya shiga.. har lokacin Zara'u bata daina kallon mirror ba. "Sauka mana! Taji ya fada da karfi. A daburce ta fara cire seatbelt ɗin ganin duk ta rude ya sakashi faɗin " Tsaya! Shi ya cire ma ta seatbelt ɗin da sauri ta bude kofar motar ta fita tana kallon gate din gidan. Gani tayi gate man yaƙi karasa rufe gate ɗin kamar dai magana yake yi da wani, kasa tafiya tayi ta tsaya tana kallon ƙofar.. "What are you staring at? Kallon Musty tayi sai kuma ta juya ta fara tafiya. Shima bin bayanta yayi zuwa cikin gidan.. shi ya fara shigowa falon gidan sannan ita, sai rakuɓewa take kamar wata munafuka.. "Oops akwai kayanki a mota ko? Cewar Musty yana maida dubansa gareta. "Bari na je na dauko! Ta fada da sauri tana fita ba tare da ta jira cewarsa ba. Ummi dake zaune a falo tana kallonsu ta ce " Amma Kunyi sauri! Shafa kansa yayi yana murmushi baya ce " Yeah ba goslow sosai, ina su Farida? "Ai Farida na garden tana zance ita kuma Zainab tana upstairs tana karatu kasan an fara Neco" "Ok, idan Farida ta shigo ta kawo min abinci dakina" Daga haka ya wuce upstairs.. Zara'u na fita ta nufi bakin gate kallon me gadi tayi ta ce " Waye ku ke magana dashi dazu? "Hajiya wani ne wai wajen Oga Mustapha yazo kuma nasan karya ne saboda da ace wajensa yazo ai daya ganshi dan kusan tare suka iso, gashi dai da kamala amma ga dukkan alamu baida gaskiya! Bata ce komai ba ta bude gate din gidan ta leka, tsaye ta ganshi jikin mota yana latsa wayarsa.. karasa fitowa tayi, karar kofan daya ji ya sakashi ɗagowa yana kallon wajen. Kasa karasawa tayi sai kallonsa kawai da takeyi. Ajiyar zuciya ya sauke dan har yayi deciding ya tafi gobe da safe kafin ya wuce Kano sai ya dawo.. shi ya karasa inda take, hannunta ya janyo ta karasa fitowa daga cikin gidan sannan ya rufo kofar gidan.. kwace hannunta tayi tana juya masa baya.. "Zarahhh! Ya kira sunanta yana jan h din ƙarshe Runtsa idanunta tayi kaɗan dan har cikin zuciyarta taji yadda ya kira sunan. "Please ki kalleni we don't have much time nasan yanzu za'a fara kiranki" bata ce dashi komai ba kuma bata yarda ta juyo ba. Shi ya dawo gabanta yana kallon fuskarta ya ce " Meyasa kika zabi tafiya ki barni? "Hmm! Ta fada ba tare da ta ɗora da wata kalmar ba. "Ok bazakiyi magana ba? Shuru tayi dan haushi ma yake bata musanman idan tuna da maganar Yaya Musty ta dazu. "Zarah dan Allah karkiyi negative thinking akaina, wallahi ina kaunarki kuma ban shigo rayuwarki dan na cutar da ke ba, ni bansan da zancen auren nan ba, just 2weeks baya Mami take sanar dani wallahi Zarah bana son Bilkisu! Banda son ƴan uwantaka bana yi ma ta wani son, kece zabina kece wadda zuciyata ta zaba abokiyar rayuwar, dan ta yarda kuma ta amince ki zamto kawa a gareta, meyasa zan cutar dake? Ina da kanne, ga Maryam, Fa'iza da Fatima duk wadda akayi wa a cikinsu bazanji dadi ba, wannan duniyar ka aikata alkhairi ma ya ka kare ballantana ace akasin haka? Hawaye na zuba a idanun ta ta ce " Why not kace baka so? If it was me I will definitely speak my mind Ammar! I won't let anyone steal away my happiness, why won't you do the same? Numfashi yasauke yana kallonta cike da tausayinta, bazata taba gane halin da yake ciki ba, he can't joke with his Mom and he can't choose her happiness over his mother's happiness.. bata tsammani ba taji yayi hugging din ta, hug din da ake kira da tight hug.. Runtsa idanunsa yayi dan baya so kwallar da ke shirin taruwa ta taru ballantana ta zubo.. kuka Zarah ta fashe dashi zuciyarta na zafi, she dearly love him, Kuma tana kishinsa sosai how could she bear it? Ta yaya zata iya jure jin Ammar yayi aure? "Zarah Please! Ya fada whispering in her ears. Hadiye kukan tayi babu shiri.. "I'm sorry Zarah! Umarnin Mami ne bazan iya tsallakewa ba, bawai dan bana kaunarki ba but i will surely come back for you i promise! Hawaye masu zafi ne suka zubo ma ta.. Sakinta yayi yana kallonta, tears din dake fuskarta ya fara whipping yana cewa " Ki daina kuka Dan Allah! "Ok! Ta fada wasu hawayen na zubowa. Sake hugging dinta yayi yana ji kamar kar arabasu, shi kadai yasan yadda yake ji akan Zarah, no body would never ever understand his pain, Amma Allah na gani kuma yasan He won't leave him like this.. "i love you! Ya rada ma ta a kunne yana sakinta. Bata iya kallonsa ba dan jikinta duk yayi sanyi.... "Saude ta ce min an siyar da wayarki kuma inaso mu dinga magana, ga wannan wayar akwai layi me and u a ciki" Kallon Samsung ultra20 din tayi ta ce " Wannan ba wayarka ba ce? "Yes tawa ce, zan siyo wata banda wata wayar da zan baki a yanzu kuma nasan lil Mom ɗinkin bazata bari kina fitowa ba, takecare Please kuma promise me bazaki kula kowa ba? Shuru tayi tana kallon wayar yake miko ma ta har lokacin bata karba ba. "Please Zarah! "Ok! Ta fada a sanyaye.. "kinyi alkhawari? Yasake faɗa. "Eh" murmushi yayi sannan ya saka ma ta wayar a hannunta ya ce " Zan dinga kiranki take care please" Kai kawai ta gyada masa.. gida ta shiga shi kuma ya nufi motarsa. and da daddaren nan zai dauki hanyar Kano! Ko karasawa wajen motar Musty batayi ba taga Ummi ta fito tana fad'in " Wai ko guduwa tayi ne? Goge idanunta tayi ta karasa wajenta tana fad'in " A'a, kasa buɗe motar nayi" daga sama har ƙasa Ummi ke kallonta kafin kuma ta ce " Shine kika dauki wannan uban mintina haka saboda sakarci? Me wannan a hannunki yake kyalli? Ta ƙarashe maganar tana kallon hannunta inda bayan wayar da Ammar ya bata ne yake da shining kasancewar babu cover.... "Cover waya ce" Ta fada tana ƙoƙarin miƙa ma ta. 'Aa rike kayarki, muje na buɗe miki motar yar ƙauye! Zara'u bata ce komai ba tabi bayanta. Ummi tayi tunanin ya kulle motar amma tajita a buɗe, karamin tsaki tayi tana fad'in " Ashe ko key besa b? Ita dai Zara'u bata ce komai ba. Booth Ummi ta buɗe ita kuma ta ciro kayayyakinta.. a falo ta tarar da Farida, Zainab harda Ummi.. "Thank God zamu huta da wanke² cewar Farida harda tafa hannuwa.. "Sarki aiki tazo! Ai Zara'u bata gajiya yar albarka"  Ummi ta fada tana murmushi.. itama Zara'u murmushi tayi kaɗan tana tsugunnawa ta gaida Ummi.. bayan sun gaisa ta kalli Zainab ta ce " Kai mata kayanta chan dakin" Ta fada tana nuna dakin dake ƙasa gaban kofar kitchen kaɗan. Tashi Zara'u tayi tabi bayanta tare da Kayanta dan babu wanda Zainab din ta dauka a ciki.. katifa ce kawai a dakin, godiya tayi ma ta sannan ta ajiye kayanta daga gefe.. tana kallon dakin da sanyi ya kama tiles din ƙasa har bango duk da cewa fenti ne.. bata daɗe a ciki ba Zainab ta shigo tana ajiye ma ta pillow da bedsheet da duvet.. godiya tayi ma ta bata amsa ba ta fice.. tana cikin shimfida zanin gado wayar da Ammar ya bata ta fara ringing, da sauri ta dauka dan karar ringing din tayi yawa.. "Kin kwanta ne? Taji ya fada daga dayan bangaren.. "a'a yanzu dai zan kwanta! "Ok karki manta idan kin tashi sallar dare kiyi mana addu'a kinji ko? A hankali ta ce " Toh" "ok good nite! "Amma kace baka zo dawata wayarba? Tana ji yayi murmushi me sauti kafin ya ce " Wannan karama ce kuma inaso mu dinga chat da vd call"  Da Uhm ta amsa tana kashe wayar sannan ta sakata a silent......

*Ayi haƙuri update ba kullum b saboda school, Allah y bamu Sa'a Amin*

08142904255

Autarmama ce

MATANA ✓Where stories live. Discover now