✨ *MATANA* ✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
*Comment*
*Vote* &
*Share* Fisabilillah*Masu nema daga farko kuyi min mgn ta wannan number 08142904255! But bani da pages idan kinsan bakya son document sai dai ki duba Wattpad!*
*012*
Yau ta kama Saturday Zarah bata da school, tun asuba data tashi bata koma ba saboda karatun da take, duk da cewa jikinta ba dadi kuma ba wani gane karatun take ba amma bata son abinda zai saka ta fara tunanin wani abun da zai dameta. Saude ce ta shigo dakin nasu ta ajiye plate din dake hannunta ta ce, "Ga abinci ki tashi kici tara ta wuce fa, kuma Inna ta ce ki fadi abinda za'ayi wa bako dan ba'a san lokacin da zaizo b" Nunfashi taja tana saukewa a hankali kafin ta ce, " Basai an masa komai ba kawai a siyo ruwa da lemo ya isa" Gyada kai Saude tayi tana fita daga dakin.. bata dade da fita ba Inna ta shigo tana gyara daurin zani ta ce, "Saboda wulakanci irin naki Xarah? Mutumin ya taho tun daga Habuja dan kuturin wulakanci kice babu abinda zaki bashi? "Inna dan Allah ki kyaleni bana jin dadi wallahi, bazan iya masa komai ba" cewar Zarah kamar zatayi kuka. "Ai dama bance kiyi ba, Ni da saude zamuyi, sai ki fadi abinda za'ayi! "Kuyi komai ma" Zarah ta fada tana kwanciya. "Idan ma zaki saki jiki ki saki jiki Kinji ko? Allah yayi Mustapha ne mijin naki, wallahi dan arziki abinsa, babu abinda Ammaru zai nuna masa banda hasken fata, hasken fatar Ammarun ma kamar wani zabiya! Daga haka ta fice. Murmushi Zarah tayi kaɗan tana kwanciya tare da lumshe idanunta. Kaji biyu inna ta fita ta siyo sannan saude ta gyara sukayi lafiyayyan stew da white rice sai leman abarba da kwakwa aka saka cikin kankara a kula. Ana kiran sallar azahar Mustapha ya iso. Sallama yayi daga kofar gida.. Inna najin muryarsa ta tashi tana fad'in " Shigo mana Mustapha ka tsaya kamar wani bako? Shigowa yayi kansa a ƙasa yana sakin murmushi me kyau.. sallaya Saude ta shimfida masa sannan ta gaida shi. Gaisawa sukayi da Inna dake ta jera masa sannu kamar wani mara lafiya. Tashi ka shiga daki mana kaga rana ta kwalle nan inuwar bata zo ba tukun" Cewar Inna tana kallonsa. Tashi yayi Saude ta masa rakiya har dakin inna. Zarah na kwance tana bacci abunta dan tunda Inna ta sakata tayi wanka ko mai bata shafa ba ta kwanta saboda baccin dake damunta. "Ya jikin nata? Ya fada idanunsa akanta. "Taji sauki Alhmdll, bari na kawo maka ruwa" Daga haka Saude ta fita. Tun da suka fara magana Zarah ta tashi amma taki bude idanunta. Tare da Saude suka dinga hira har yaci abincin da aka kawo masa. Bayan ya dawo daga sallar la'asar ya tarar da Zarah zaune a tsakar gida. Duk ta rame ta kara duhu, tasha kyau cikin jalbab. Murmushi yayi yana karasawa yayi wa kansa mazauni a kusa da ita. "Ya jikin? "Naji sauki, ya hanya? Ya Farida, Daddy da kuma Ummi? "Duk suna nan kalau suna gaida ke, ya karatun? Da alhmdll ta amsa masa. "Toh Masha Allah, ki dage kinji ko? Kai ta gyada alamar toh.. kafin yayi magana suka jiyo sallama.. ɗagowa Xarah tayi dan the voice is so familiar.. cike da mamaki take kallon Hajiya Babba... Murmushi Hajiya Babba tayi dan ta gane Zarah, duk da cewa a hoto kawai Ammar ya taɓa nuna mata ita. Tashi tsaye Xarah tayi tana Kallonta bakinta ya kasa furta komai.. Inna ce ta fito daga daki dan taji sallamar... Kallon rashin sani take mata.. "Sannunku" Cewar Hajiya babba.. da kyar Zarah ta iya gathering courage dinta ta ce, "Ina yini Hajiya? "Lafiya kau Zara'u! Hajiya babba ta amsa cikin fara'a.. "Shigo mana" Cewar Inna tana kallonta. Saude dai na daga bakin taga tana hango komai. Sallaya Inna ta dauko a daki ta shinfida mata ta zauna. Ruwa ta saka Saude ta kawo mata sannan ta zauna a bakin kofar dakinta tana Kallonta ta ce, "Ban shaidaki ba" Sai da Hajiya babba tayi murmushi sannan ta ce, "Baki Sanni ba ai, ni kamar uwa nake wajen Ammaru, da mahaifinsa da ni jini daya ne" Shuru wajen ya dauka. Hajiya babba ce ta katse shurun da cewa " Karki wani damu, Ni kam da Alkhairi nazo wallahi" "Toh madallah! Inna ta fada tana gyara dankwali.. "Toh bamu gaisa ba ko? Cewar Hajiya babba.. murmushi Inna tayi sannan suka gaisa, Mustapha ma ya gaida ita haka ma Zarah ta kara wata gaisuwar.. "Zara'u ya jikin naki? Kanta a sunkuye ta ce, "Naji sauki Hajiya" "Toh Allah ya kara sauki" Da Amin suka amsa gaba ɗaya. Nunfashi Hajiya babba ta sauke a hankali tana maida dubanta kan Inna ta ce, "Toh ni bazan tsaya jan zance ba kamar wata kankanuwar yarinya, dama akan maganar yaron nan Ammar da kuma Zarah ne, inaso ta bashi dama zai turo magabatansa insha Allah zuwa nan da wata ko daya ne idan angama bincike sai a daura dan babu zancen jan lokaci saboda sun rigada sun gama fahimtar junansu, abinda yasa nazo da kaina shine inaso naji tabakin ita Zaran idan tana ganin zata aureshi? Wani murmushi Mustapha baya saki yana tashi ya fita daga gidan gaba ɗaya.... A tsaye yaga Umar jikin motarsa yana waya, da farko ya dauka Ammar ne amma daga baya ya lura ba shi bane amma duk yadda akayi sun hada dangantaka da juna. Sallama Mustapha ya masa yana miƙa masa hannu, ɗagowa Umar yayi yana kare masa kallo sannan ya mika nashi hannun tare da amsa sallamar. Shuru Mustapha yayi yana kallonsa, yanzu ya gane tare suke da matar dake cikin gida yanzu kuma daga gani yayan Ammaru ne. Murmushi ya saki yana kallon Umar daya cigaba da latsa wayarsa. Shafa kansa yayi ya koma gefe ya zauna.yana zaune yaga matar ta fito jikinta duk a sanyaye. Shafa sajensa yayi yana dan Murmushi ya bisu da ido har suka bar wajen.. Cikin gidan ya koma, be tarar da Zarah a tsakar gidan ba sai Inna dake faɗin " Ai kuma Zarah ta muku nisa wallahi! Zama yayi yana kallonta, tun kafin yayi magana ta ce, "Ai ko da ace Zarah bazata aureka ba ni bazan iya yarda da aurenta da wannan mutumin ba, itama wannan matar bana tunanin da Allah a zuciyarta, ita kuma munafukar daga anyi zancensa sai ta fara kuka, ja'ira kawai kyayi dai kya gama wallahi! Shidai Mustapha baice komai ba. Ganin yamma na ƙara yi ya saka shi tashi ya ce, "Ina zuwa Inna" Da toh ta amsa masa sannan ya fita. Be dade ba ya dawo rike da leda yana ajiyewa a gabanta ya ce, "Ke da Saude Inji Ummi" "Toh Masha Allahu, kace muna godiya Allah ya saka da Alkhairi" "Amin Inna, ni zan tafi" "Toh shikenan kace angode wallahi, Allah sarki kace mata muna Godiya... Kallon daki tayi kasancewar labulan a dage yake ta maida dubanta ga Zarah dake goge hawaye ta ce, "Sai ki tashi ki taka masa zai koma" a sanyaye ta tashi tana daukar hijabinta ta fito, A jikin mota ta tarar dashi ya zuba mata ido, sunkuyar da kanta tayi tana karasowa. Ajiyar zuciya ya sauke me karfi yana kallonta da kyau ya ce, " Zarah karki bari damuwa ta samu gurbi a zuciyarki kiyi kokarin cireta, na miki alkhawarin zama best husband a gareki insha Allah, kuma inhar zaki bani damar hakan domin damar daga gareki ne Zarah, inaso ki cire Ammar daga zuciyarki ki amsheni na miki alkhawarin bazan taba saki kuka ba inshallah, na miki alkhawarin farinciki na har abada" Shuru Zarah tayi kanta a ƙasa tana jin duk jikinta ba kwari.. "Zarah ina kaunarki kuma insha Allah zanzamo silar haske a cikin rayuwarki, nayi alkhawarin mantar dake Ammar indai zaki bani damar hakan" nan ma bata ce komai ba.. nunfashi ya ja da karfi yana saukewa a hankali.. mota ya buɗe ya ciro gift din daya siyo mata.. a kwali yake medium. Miƙa mata yayi, hannu biyu ta saka ta amsa muryarta na cracking ta ce, "Nagode.. "U'r welcome dear, zan tafi idan naje zan miki transfer na kuɗin makaranta, dazu naje wajen Zainab tace min kinyi ƙawa ko? Murmushi tayi kaɗan tana ɗagowa ta kalleshi ta ce, "Eh" "Ok ki kula sosai da irin wadanda zaki dinga ƙawance kinga soon zamuyi aure ko? Shuru tayi tana yin kasa da kanta. Murmushi yayi kadan ba tare da yace komai ba. Itace ta ɗago da kanta ta dan kalleshi ta ce, " Ka gaida Daddy, Farida da kuma Ummi. kwana biyu wayar Farida bata shiga" "She's ok, a kitchen ta barta ruwa ya shiga amma naji tana fad'in fiance dinta zai kawo mata wata, kinsan anso a hade auren amma Ummi ta ce a'a" Murmushi kawai Zarah tayi. "Ok toh ina kara yin dare, ga yanayi na garin kidnapper's kar a sace ni bari na wuce" Murmusawa tayi tana Kallonsa ta ce " Allah ya kiyaye, Allah ya kaika lafiya" Da Amin ya amsa. Juyawa tayi ta shige cikin gida sannan Mustapha ya bar kofar gidan.....