chapter thirty one

401 35 8
                                    

✨ *MATANA* ✨

*Mallakar*
       AUTAR MAMA

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Comments*
*Vote &*
*Share fisabilillah*

*031*

          Safiyar ranar asabar Zarah na kitchen tana kokarin sauke girki, wayarta dake kan cabinet ne ta fara ruri cikin ringing tone me daɗin saurare. Hannunta ta ɗauraye sannan ta tsane tana duba me kiran nata, ganin sunan Saude ya sakata ɗauka da sauri tana karawa a kunne. "Hello Aunty" cewar Saude daga ɗayen side ɗin. "Saude ya gida, ya kike? 'lafiya ƙalau wallahi, dama nace bari na kiraki na tambayeki kune likitoci, tun jiya misalin karfe 2 na dare nake ganin fluid yana zuba lafiya dai ko? A ɗan hanzarce Zarah ta ce, " Ai asibiti ya kamata ku tafi, EDD dinki ya cika ne? "A'a fa" Cewar Saude a hankali. "Ok ku tafi asibiti dan wannan ruwan a ciki baby ke rayuwa, be fast Dan Allah, Allah ya saukeki lafiya" "Amma fa Aunty ni bana jin wani ciwo"  Saude ta faɗa harda ɗan murmushi, "za kiji ne anjima, ki dai na ɓata lokaci ki kira mijinki ku tafi stop waisting your time here! Da ok Saude ta amsa tana katse wayar kafin Zarah ta ajiye wayarta taji kukan Hydar da mugun ƙarfin gaske.. da sauri ta fito falo tana raba idanu, a ƙofar ɗakinta ta ganshi kwance a kan tiles yana tsandara kuka ga Raihan a gabansa sai faman rarraba idanu yake yi. Da sauri ta ƙarasa tana ɗaukar yaronta, sosai Haydar yake kuka cikin ƙanƙanin lokaci kansa ya fara swelling, idanun Zarah ne suka ciko da hawaye, Raihan kuwa da gudu ya bar wajen dan yayi tunanin dukansa Zarah zatayi. Kitchen ta koma ta kashe gas ɗin ta fara jijjiga Hydar da kukan yaki tsayawa har yana neman shiɗewa.. ɗakinta ta koma ta kwantar dashi sannan ta fara observing din kan nashi, sosai ya bugu dan har kan ya kumbura, massaging wajen ta fara yi a hankali tana kallon yadda yake tsala kuka wanda take jinsa har apex din zuciyarta. Baccin wahala ne ya daukeshi, ajiyar zuciya ta sauke tana daukar shi ta goya sannan ta koma kitchen ta cigaba da girkinta. Kafin 10am ta kammala girkinta iya cikinta dan Ammar ba'a gida ya kwana ba yana Call a asibiti and baya ma dakinta. Bayan ta ci abinci ta wanke abinda ta ɓata sannan ta dawo dakinta ta gyara ko ina yayi neat, sakko da Hydar tayi tana jin temperature din jikinsa yayi zafi sosai. Ajiyar zuciya tayi tana tashi ta kulle kofar dakinta sannan ta shiga wanka, bata jima ba ta fito tayi wa Hydar ta shiryashi sannan ta shirya kanta. Thermometer ɗinta ta dauko dan duba temperature din jikin Hydar saboda har yanzu yaƙi sauka. Bayan yayi reading ya nuna 39.7°c sosai hankalinta ya tashi ta fara shafa kansa tana jin bugun zuciyarta na ƙaruwa, temperature din yayi high dayawa, ga nunfashinsa daya fara fita da sauri², hawaye ne suka cika idanunta ta fara shafa masa fuska a hankali. Ita sam yanzu bata san me zata yi masa ba, tasan dai buguwar da yayi ce ta janyo masa zafin jiki. Bayan ta idar da sallar azahar tana zaune akan sallaya lokaci² takan kalli direction ɗin da ta kwantar da Hydar. Gani tayi hannunsa na rawa, da sauri ta tashi ta nufi inda yake, sai kuma taga kamar ma zabura yake yi, ɗaukarshi tayi ta fara tofa masa addu'a, after some minutes ya fara convulsing, da sauri ta miƙe tsaye  hawayen da suke zaune a gurbin idanunta suka kwaranyo zuwa kuncinta. Kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun ta dinga nanatawa, kamar ma Hydar ɗin ya suma, toilet ta nufa da sauri ta fara shafa masa ruwa a fuska, but still no respond. Da sauri ta fito daga toilet ta nufi wayarta ta shiga neman contact ɗin mijinta, har ta gama ringing bai dauka ba. Bata sake kira ba ta dauki mayafin da tayi sallah dashi ta fito daga ɗakin, kusan karo sukayi da Ammar, wanda kana ganinsa kasan yayi matukar gajiya. "Ke! Lafiya! Ya faɗa yana riƙeta, kai ta girgiza da sauri tana nuna masa Hydar dake hannunta, "Subahanallahi, me ya sameshi? Kasa magana Zarah tayi sai hawaye da take yi.. "Temperature dinshi yayi zafi dayawa, dama yana zazzabi ne? And me ya sameshi a kai naga ya kumbura" "Ammar muje asbiti convulsion ya fara, Please bana son rasa yarona" Ganin duk ta ruɗe ya saka shi kwallawa Bilkisu kira. Kamar jira take sai gata ta fito tana raba idanu. " Ɗauko hijabinki za muje asibiti zaki riƙe Yaron nan Cox Zarah bazata iya ba" "Asibiti kuma? Ka manta na faɗa maka zanje gidanku saboda shirya kayan saukar Maryam gobe ne fa, kuma ka... "Will shut your mouth up! Ina miki zancen asibiti kina min zancen gida? Zaki wuce ki saka hijabi ko sai na tattakaki?! Cewar Ammar cikin tsawa. Da sauri ta bar wajen, bata daɗe ba suka fito tare da Raihan dake kallonsu duk a tsorace yake. "Riƙe Zarah muje! Naga rawar kanki yayi yawa zaki iya yarda yaron! Daga haka yayi gaba, kusa da Zarah ta matso tana fad'in " Muje! Xarah bata ce da ita komai ba saboda jiri data fara gani... Tun daga time din bata sake sanin inda take ba sai ganinta tayi a asibiti, lokacin data farka da sauri ta miƙe tana kallon ɗakin, Bilkisu su kawai a ciki sai faman latsa waya take yi. Pulse oximeter dake hannunta ta cire tana sakkowa daga kan gadon. Bata kula Bilkisu ba ta fito tana jin jikinta duk ba ƙwari, har gari yayi duhu, kallon asibitin take yi, jin kanta ya fara juyawa ya saka ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun da aka tanada domin zaman mutane. Tun daga nesa Ammar dake tahowa ya ganta, da sauri ya karaso yana fad'in "Ya a kayi kika fito daga ɗaki? Ina ita Bilkin? "Ina Yarona? Ta faɗa tana riƙeshi.. "Ki kwantar da hankalinki, yanzu doctors suna kansa and komai zaizo daga  sauki" Kuka ta fashe dashi tana riƙe hannunsa magana take sonyi amma taji ta sarke mata.. "Shiiii, kinsan condition dinki meyasa kike son ƙara stressing kanki? Insha Allah babu abinda zai samu Aliyu, just pray for him" Kai ta fara girgizawa tana kokarin tashi, bai hanata ba sai taimaka mata da yayi ya riƙeta.. "Muje ɗaki ki huta" "Dan Allah zanga yarona" Ta faɗa da kyar. "Zaki ganshi amma ba yanzu ba" bata kara cewa komai ba suka koma ɗaki, da idanu kawai Bilkisu tabisu da kallo, sai da ya zaunar da Zarah sannan ya mai da dubansa ga Bilkisu ya ce, " Cewa nayi ki zauna kina latsa waya or ki kula da ita? "Toh ya zan mata tana son fita? She's mature enough to decide what is right or wrong! Zanje gida saboda bana jin dadi" daga haka ta miƙe ta fice daga ɗakin. Girgiza kai kawai Ammar yayi, be taɓa tunanin Bilkisu bata da tausayi har haka ba. Da kyar Ammar ya kwantar wa Zarah da hankali har ta haƙura, kafin sallar Isha'i aka kai Hydar ward. Ammar na kallon Dr Sadiq ya ce, "Dr me issue din? Sai da yayi discarding safar hannunsa ya ce, " Ga file dinsa a hannun Dr Sa'eed ka karba ka karanta" " Bani da wannnan time din just tell me" Cewar Ammar yana kallonsa. Sai da Dr Sadiq ya ɗan ja nunfashi sannan ya ce, "Dr Ammar, yaronka yana under oxygen, kuma ba mamaki convulsion din da ya samu ya taba kansa and after that ya bugu sosai a kansa, dole gobe zakuje kuyi hoto! But a shawarce in dai muka samu daya daga cikin complications na Convulsion ko kuma wani head injury sakamakon buguwar da yayi toh yafi ku tafi Cleveland Clinic, Ohio, united state, asibitin yana ɗaya daga cikin best hospital for neurosurgery, a shawarce fa, fatan dai Allah ya bashi lafiya, akwai alluran da xan rubuta yanzu, idan ka duba file dinsa zaka ga dose din da ya kamata ka bashi nayi inserting cannula, so no wahala" "Ok Na gode, muje ka rubuta min" Office ya bishi yayi masa rubutu sannan ya karbi prescription din ya fita, be daɗe ba ya dawo da Medications ɗin, shi da kanshi yayi masa komai, yayi chatting sannan yazauna a kusa da gadonsa yana kallon cute face dinsa cike da tsantsar tausayinsa ga NG tube an saka masa ga oxygen. Runtsa idanunsa yayi yana tunanin yadda Zarah zata ji idan ta ganshi cikin wannan condition ɗin, and gashi ranar Monday zata fara exams. Nunfashi ya sauke a hankali yana tashi ya bar wajen, wajen Zarah ya nufa, a zaune ya ganta da alama sallar ta idar, da idanu kawai ta bishi ganin duk jikinsa a sanyaye ya saka zuciyarta ƙara karaya. " An bamu gado, gobe insha Allah zan kawo miki Maryam ta tayaki zama, cox you can't cope alone, ki kwantar da hankalinki kinji ko? Kai kawai ta gyada a hankali. "Good, sister ɗinki ta sauka ta samu baby boy" "Masha Allah, Allah ya raya kira min ita" Ta faɗa cikin karfin hali. "No ki bari sai da safe, by the way faɗa min ta yadda Hydar yayi wannan faduwar? "Bansani ba, na barshi a ɗaki na taho kitchen girki sai ihunsa naji, kawai dai ina tunanin Raihan yayi kokarin daukarsa ne sai ya fadi saboda na zo na tarar da Raihan a kofar dakina tare da Hydar dake kuka" Kai Ammar ya riƙe yana jin ba daɗi sam, dan tabbas hasashen Zarah gaskiya ne, tunda yasan a kan gado zata bar Hydar shi kuma Raihan zaiyi karambanin daukoshi, so cikin Sa'a har suka fito kofar ɗaki kafin ya faɗi" Numfashi ya sauke yana duban Zarah ya ce "Sorry Please" "No it's ok, why are you apologizing? Nasan ƙaddara ce kuma Raihan ai yaro ne, zan iya zuwa yanzu na ganshi? Kai ya gyada mata alamar eh. Shi yayi mata jagora har zuwa VIP room din da aka kai Hydar, tun kafin ta ƙarasa gaban gadonsa hawaye suka fara sintiri a kumatunta. Riƙeta Ammar yayi yana rarrashinta cikin tausa-sa murya ya ce, "Addu'a zakiyi masa wannan kukan bai da amfani, idan kin kalli conditions ɗin yaran dake kwance zaki ga naki ba komai bane" "Me likita yace? Cikin karfin halin bata amsa Ammar ya ce, "Gobe zamu kaishi ayi masa hotan ƙwaƙwalwa, if there is any problem insha Allah cikin week dinnan zamu tafi UK insha Allah" Kuka ta saki me karfi tana ƙoƙarin sulalewa a wajen, riketa Ammar yayi yana fad'in " Me haka Zarah? Baki yarda da ƙaddara bane? Wannan kukan da kike yi bazai canza komai ba, kiyi haƙuri dan Allah, ganinki cikin wannan condition din ba ƙaramin tayar min da hankali yake ba wallahi, Hydar zai samu lafiya insha Allah, idan anyi hotan gobe insha Allah zan sanar dasu Inna da Ummi dan su san halin da ake ciki, and also Mustapha. Kai ta girgiza tana rike hannunsa ta ce, "Idan ka fadawa Mustapha da Ummi bazasu taba yafe min ba, dan Allah kar ka faɗa" "Babu abinda zasuyi miki, kuma ai baki da laifi, kinsan wannan condition din bazai yu a boye musu ba, dole su sani, especially his father, infact ma US zamuje kuma kince a chan yake aiki right? Kai kawai ta gyada alamar eh. Kwanan zaune sukayi daga shi har ita. Washe gari da safe da kyar ta yarda suka koma gida tayi wanka ko ruwan tea taki sha, idanunta duk sun kumbura saboda kuka, be sanar wa kowa a gidansu ba banda Hajiya Babba da Umar dan yasan su Mami sun shiga hidimar saukar Maryam. Anan gidansu Umar suka tarar dasu har da Hafsat, sannan suka wuce Asibitin. Hajiya Babba da Hafsat sai kwantar mata da hankali sukeyi... Ammar ne ya kai shi scanning ɗin sai kusan 1pm suka dawo, anjima da yamma zai koma ya karbi result ɗin. A nan asibitin Hajiya babba ta zauna tare da Zarah da sam hankalinta baya jikinta, su Umar kuma suka wuce gida. Tun rana da Ammar ya bar ward din bai dawo ba sai bayan Isha'i... A yadda result din ya nuna akwai Brain Bleed Hemorrhage (Intracranial Hemorrhage) bleeding between the brain tissue and skull Kuma zai iya causing  brain damage and be life-threatening, though dai akwai possibility na warkewa amma dole za'a samu complications daga baya, kuma is an emergency case da ya kamata ayi aiki da wuri, ba Zarah ba har Ammar hankalinsa yayi mugun tashi duba da yanayin ƙanƙantar yaron. Kuka kuwa babu irin wanda Zarah bata yi ba, dan ta fitar da rai ga Hydar tasan mutuwa zaiyi.. riƙeta Ammar  yayi yana kokarin zaunar da ita amma taki zaman. "Kyaleta Ammaru, dole taji ba daɗi ai ɗan fari ne, ya kamata kuma ka sanar da danginta ko? Da kuma uban yaron" "Eh na sanar dasu, innarta ce dai ban fadawa ba saboda jibi zata tafi Saudiyya, ƙanwar mahaifiyarta kuma insha Allah gobe zata iso, shi kuma mahaifin yaron  nace sai munje chan kasar wajen sai a sanar masa tunda dama a chan din yake da zama"  "Shikenan toh, yaushe zaku tafin? Cewar Hajiya babba. "Gobe nake so mu tafi saboda ana bukatar yin aikin cikin gaggawa, nasan bamuyi wani shiri ba amma insha Allah zan biya urgent flight, Allah zai hore, yanzu ma zanje chan ɗin, kafin gobe zanyi contacting din likitar da zamu gani a chan din *DOCTOR AMINATU*" "Ayya toh Allah ya kaimu ya bada nasara, dama chan ka san likitar ne? Hajiya babba ta kuma faɗa tana kallonsa. "A'a, DR Sadiq ne ya haɗani da ita, ta kware sosai a fannin, yar Sudan ce amma a chan ƙasar tayi karatunta kuma take musu aiki" "Toh, Allah Ubangiji ya bada nasara" da Amin ya amsa yana kallon Zarah. Bai daɗe ba a ward din ya fita, Ammar be dawo asibitin ba sai 12am, gobe da safe zai koma airport ɗin ya kammala komai, yana so ko zuwa dare ne jirginsu ya tashi zuwa  United State of America. Yadda Zarah taga rana haka taga dare, Ammar was very supportive! Ko da wasa be bar gefanta ba har wayewar gari. Kafin 8am Hafsat da Umar suka zo, hakan yasa Ammar da Umar barin Asibitin dan zuwa airport daga nan kuma Umar ya saukeshi a gidnsu ya sanar dasu Mami halin da ake ciki, duk da yasan by now farfesa Bilkisu ta sanar dasu halin da ake ciki tunda ya sanar da ita dan yayi zaton zata zo amma ta nuna bata da lafiya. Sai 3 sannan  suka baro airport ɗin komai kuma yayi ready, gidansa Umar ya fara kaishi, a cikin mota Umar ya zauna Ammar kuma ya sauka ya shiga ciki. Bilkisu na zaune a main falo tana shan leman fata ga TV na aiki. Kallo ɗaya yayi mata ya wuce ɗakinsa, bai ɗau lokaci ba ya fito ya shiga na Zarah, kayanta ya diba cikin akwati ya haɗa dana Hydar sannan ya debi nashi duk ya zuba cikin trolley, duk abinda yasa zata bukata sai daya dibar mata duk da beyi wani lodi ba, takardar hutun daya dauka a asibiti ya saka a ciki sannan ya fito yana kallonta da kyau ya ce, "In sha Allah by 6pm zamu wuce US saboda za'ayi wa Hydar aiki, zaki iya komawa gidanku or wajen Mami har mu dawo " da sauri ta miƙe tana kallonsa bakinta har rawa yake dan  magana na cinta.. "Tab! America? Ai wallahi bazan yarda ba! Sai dai a tafi dani! Kaine ubansa da zaka dinga dawainiya da shi har haka? "Kinga bana son rashin hankali! Na dai faɗa miki! Daga haka ya ja trolley ya barta a nan wajen tana jin wani bakincikin mara misaltuwa. Ko da suka isa gidansu Ammar, Umar bai shiga ba nan ma a kofar gidan ya parker. Mami na zaune tana raba memo din sauka da sukayi ragowa saboda a samu a rabawa wadanda suke zuwa Allah ya sanya alkhairi. kansa a ƙasa ya ƙaraso, gaisawa sukayi sannan ya dora da faɗin " Naso muyi maganar tun shekaran jiya amma ban samu zama ba, Hydar ne ya samu head injury kuma yana bukatar surgery cikin gaggawa, in sha Allah by 6pm zamu tafi US ni da Zarah da kuma yaron" "Eh ai Bilkisu ta sanar dani cewa yaron ba lafiya, ashe abun har ya kai ga haka? Toh Allah ya kiyaye hanya, ya kuma bashi lafiya" Kallonta ya tsaya yi jin yadda tayi maganar very soft, bai taɓa tunanin abun zaizo da sauki haka ba, nunfashi ya sauke yana matsowa kusa da ita ya ce, "I know u'r soft hearted Mom, kawai ana kokarin ganin an sauya ki ne! Please don't change" Banza ta masa tana hada kan aikinta. "Bye Mom" Ya faɗa yana miƙewa. "Toh Allah ya tsare" Da Amin ya amsa sannan ya fita. Asibiti suka koma, Zarah ce kawai a gaban gadon Hydar ta kafeshi da idanu, kafadarta Ammar ya shafa very slowly yana fadin " Bazaki daina kuka ba? Sababbin hawayene suka zubo mata tana juyowa ta kalleshi. Yatsa ya saka ya share mata su yana girgiza mata kai ya ce, "In dai baxaki daina kuka ba, zan yi fushi, kukan fa bashi da amfani, addu'a kawai zakiyi masa" Kai ta gyada tana maida dubanta kan Hydar dake kwance yana nunfashi tare da taimakon Oxygen.  Hajiya babba ce ta shigo bakinta dauke da sallama. Ammar ne ya amsa yana fad'in " Ina kika je ne? "Dakta Sadiq ne ya kirani ya ce gida zai wuce ya bani wannan takardar yace idan kazo na baka, ita zaka nuna idan kaje chan ɗin" Karɓar takardar hannunta yayi yana fad'in " Shikenan, muje chan gida na sauke ki tunda yamma tayi" "A'a ai ba'a bar Zarah ita ɗaya ba, na dauka ma k'anwar mamanta ai da safe kace zata zo ko? "Eh, munyi waya dazu zata samemu a chan US ɗin shiyasa bata zo ba"   Kai Hajiya babba ta gyada tana neman waje ta zauna. Shima Ammar zama yayi kusa da Zarah yana haɗa hannayensu waje ɗaya. "Kun fara exams ko? Ya fada ba tare da ya kalleta ba. "Eh, zanyi repeating din semester" Ta fada tana goge hawayenta da dayan hannun" "Bazakiyi repeating ɗin komai ba insha Allah, zan saka aje ayi reporting kuma zan tura evidence a nuna musu, nasan insha Allah zasu bari kiyi daga baya" bata ce komai ba sai kai kawai data gyaɗa tana kallon ɗanta cike da tausayi. 

MATANA ✓Where stories live. Discover now