✨ *MATANA*✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*EXQUISITE WRITERS FORUM*
*Wannan labarin ƙirƙirarre ne, banyi shi ɗan cin zarafin wani ko wata ba! Sannan idan yayi shige da labarinka/labarinki coincidence ne Yawwa*
*Comments share and vote dinku yana da matukar mahimmanci idan yayi karanci zan maida abuna ba kudi💃*
*009*
A kan dressing mirror ta ajiye abinda ya bata, sannan ta fara rage kayan jikinta, Farida ce ta dauki ledar tana tana fad'in "Wannan fa? Zara'u bata iya bata amsa ba saboda yadda take jin jikinta. Budewa tayi ta ciro mxry box din dake ciki, fashion necklace ce me kyau da tsari. "Woooow! Ta wace? Ta fada with so much excitement. "Oh if I guess correctly ke ya siyawa? Ta karashe maganar cikin sigar tambaya. Lumshe ido Zarah tayi dan jin kanta take kamar zai fashe. "Wai jikinne? Farida ta kuma fadi tana kallonta. Nan ma Zarah bata iya amsawa ba. "Allah ya baki lafiya" Daga haka Farida bata kara cewa komai ba. Washe gari karfe 7am suka kammala shirin tafiya Kano dan karfe 2pm zasu shiga exam. Karfin hali kawai Zarah takeyi dan jin jikinta take kamar ba nata ba yayi wani iri, ƙafafuwanta sunyi nauyi haka ma hannayenta ga matsanancin ciwon kai. Har suka isa Kano bata sani ba, saboda idanunta a rufe suke ko sun tsaya a checking point bata bude ido saboda nauyin da yayi mata. Bayan sun iso makarantar Mustapha ya maida dubansa gareta yana fadin "Zaki iya exam din? "Eh" Ta fada da kyar. Shi ya taimaka mata ta fito har wajen da ake saka hannu da duba reciet duk shi ya taimaka mata saboda bata iya rike biron da kyau, basu wani dau lokaci ba suka shiga dakin jarabawar. Da kyar Zarah ta iya login a computer ta saka duk abinda ake bukata sannan ta fara amsa questions ɗin, cikin kankanin lokaci ta kammala, taje tayi attendance sannan ta fito, Mustapha ne ya riketa ganin tana dafe bango, cikin mota ya kaita, cikin tsananin tausayinta ya ce, "Zarah me kike son maida kanki akan soyayya? Are You out of your mind? Kinga yadda kika koma? Duk saboda Ammar? Please Zarah karki lalata future dinki akan past dinki, Ammar is your past, now concentrate on your future! Kuka ta fashe dashi tana rikeshi jikinta duk rawa yake yi.. "Bazaka gane ba Mustapha, i have no other choice! Ina kaunar Ammar! Ji nake kamar zan mutu, zuciyata zafi take! Zuciyata ciwo da radadi take min, meyasa hakan zata faru dani? Meyasa Ammar zai yaudareni? Me na taba yi masa? "Shiiiiiiiiii! Ya fada yana kwanto da ita jikinsa. "Ya isa haka Xarah, inaso ki manta da Ammar, face your study, ki dage kiyi abinda ya kamaceki! Show him u can do without him if he thinks you can't, so prove him wrong! Keep your self busy, karki bar duk wani gurbi da zaisa ki dinga tunaninsa ko kuma old memory dinku, he's your past! Sannan karki yarda yasan kina Kano yanzu, ba ruwanki dashi, kiyi abinda ya kawoki banda wannan makarantar ma da babu abinda zai kuma hadaki da Kano sai dai ko kina son zuwa kiga su Inna, ki daina damuwa Please Zarah" Shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya. Zainab ce ta shigo motar tana kallonsu sai kuma ta ɗauke kanta tana fad'in " Allah dai ya bamu Sa'a" "Amin, Hope dai batayi wuya ba? Ya fada yana kallon bayanta kasancewar a front seat take, shi da Zarah kuma a back. "Eh" "Allah ya bada sa'a, bari mu tafi kar yamma ta kara yi" Sakin Zarah yayi ta koma kujera ta kwanta wani zazzafan zazzaɓi na rufeta. 11pm saura suka dawo Abuja, Dukansu a gajiye suke musanman ma Zarah da takeji kamar bazata kai anjima ba zata rasu saboda ciwan dake cinta. Tana idar da sallah ta kwanta ko abincin da Ummi ta kawo mata kasa ci tayi.. Washe gari da asuba da amai Zarah ta tashi, kwata² bata da wani kuzari, yanzu ma zaune take a kofar toilet ta gama amai amma ta kasa tashi, sunan Farida ta fara kira a sanyaye, sam Farida bata san tana yi ba saboda bacci take. Locker dake kusa da ita ta fara bugawa da kyar, cikin bacci Farida ta buɗe idanunta. "Farida dan Allah kira Ummi" Cewar Zarah tana maida nunfashi. Tashi Farida tayi tana buɗe idanuwanta akan Zarah, sakkowa tayi daga kan gado tana karasowa inda take da sauri ta ce, "Subahanallahi lafiya? Kasa magana tayi dan karfinta duk ya kare. Da sauri Farida ta fita daga dakin, kusan karo sukayi da Daddy dan dawowarsu kenan daga masjid. "Ke me haka? Cewar Mustapha yana kallonta. "Dama Ummi zan kira Zarah ce ba lafiya" "Zarah kuma? Haryanzu jikinne? Cewar Daddy yana kallonta. "Eh daddy" Ta bashi amsa. "Toh ta shirya ku tafi asibiti kafin Mustapha ya wuce office ko? Da toh ta amsa tana komawa cikin daki, ita ta taimakawa Zarah ta shirya, da kyar ta iya shan ruwan tea mara madara sannan suka wuce asibiti. Magunguna da allurai aka rubuta bayan likita ya dubata sannan Mustapha yaje ya siyo, yana dawowa aka saka mata drip bata daɗe ba bacci ya dauketa. Ummi dake gefanta ta sauke ajiyar zuciya tana kallon yaran nata ta ce "Anya kuwa wannan yaron hakannan ya bar yarinyar nan? Ace abu yaki gaba yaki baya? Wannan wani irin so ne haka take masa? "Ummi kawai cutace daga Allah sai kuma damuwa shine abun ya hadar mata, amma shidin banza! Ni wallahi dama hakura tayi da karatun health dinnan kawai ayi aurensu ita da Yaya" Cewar Farida ranta duk a ɓace. Wani banzan kallo Ummi ta jefeta dashi, tashi tayi ta fita a ward din. Mustapha ne ya biyota, yana zama a gefanta cikin cool voice ya ce, "Nayi tunanin baki sani ba" "Uhm, na sani rannan naji Daddy na zancen" Sai daya shafa kansa sannan ya ce, "Nima jiya Daddy yake faɗa min" Kallonsa tayi ta kuma faɗin " Allah yasa Zarah ta yarda dannaga bata ganin kowa sai wannan Ammar din kamar shi kadai ne namiji wlhy haushi ma ta fara bani, tana abu kamar ba mace ba" shidai Mustapha baice komai ba. Karfe 8am Zarah ta farka, Ummi ce kawai a dakin. "Ya jikin Zarah? "Dasauki" Ta amsa a hankali. Tashi Ummi tayi ta fita, tare suka dawo da Nurse, duba Zarah yayi kuma ya tabbatar she's ok, Ummi ya nunawa yadda zata sha drugs da kuma allurar da za'ayi mata. Kafin axahara suka dawo gida.