Chapter twenty nine

583 48 32
                                    

✨ *MATANA* ✨

*Mallakar*
       AUTAR MAMA

*FREE BOOK*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
                 (E.W.F)

*Comments*
*Vote &*
*Share fisabilillah*

*029*

           Slowly ya tura ƙofar bedroom ɗinta yana bin kan gadonta da kallo, tana kwance ta rufe jikinta da duvet ga Hydar cikin net ɗinsa a gefanta. Ƙarasowa ciki yayi yana nufar inda take ya buɗe duvet ɗin a hankali, four eyes sukayi dashi. Murmushi ya saki yana ɗan shafa kansa ya ce, " Bakiyi bacci ba? "As you can see" Ta faɗa tana gyara kwanciyarta. Numfashi ya sauke a hankali yana kallonta da kyau ya ce, "Yanzu munyi aure shikenan duk soyayyar mu ta gudu ne? Ni ban gane miki ba Zarah! Why are you behaving like this? Ni ba haka na sanki ba, Zaran dana sani daban da wannan" Numfashi ya sake saukewa yana dawowa gefanta ya zauna tare da haɗe hannayensu, cikin tausa-sa murya ya ce, "Ki faɗa min idan laifi nayi miki, ko kuma nayi miki abinda bakya so" za me hannunta tayi tana juya masa baya tare da furta kalmar "Ba komai" "kinsan bazan karbi amsar ba komai a matsayin amsa ba ko? Ni bana son wannan zurfin cikin naki, voice out your mind Zarah I'm ready to listen wlhy, baki san yadda kike hurting ɗina ba ko? Zarah Please ki faɗa min" Ya ƙarashe magana yana dawowa side ɗin data juya harda matsar da net din Hydar. Tashi zaune tayi tana kallon agogon ɗakin 12am har da minti uku, dubanta ta mayar gareshi ta ce, "Dare yayi, bana so ina shiga hakkin matarka, ya kamata ka tafi" "Ko na fita anan dakina zan wuce Zarah! I have no issues with her! No body will understand me ai including you! Nifa if I love something I just love it wholeheartedly, and also If I despise something! "This isn't right Ammar! No matter what Bilkisu is your wife and the mother of your child and you can't change that right? Adalci shine abinda muke buƙata a wajenka! Kuma ka san result na rashin yin adalcin a wajen Allah, Good nite ina jin bacci" Xarah ta ƙarashe maganar tana kwanciya abunta. Lumshe idanunsa yayi na ƴan seconni sannan ya buɗesu a kanta. "I love you Zarah" Ya furta yana shafa Fuskarta. Ko kulashi ba tayi ba dan har ga Allah haushi ma yake bata idan yana cewa i love You ɗinnan. Bulb ɗin ɗakin ya kashe sannan ya fita. Bilkisu na kwance tana chat da Fa'iza taji shigowarsa, kasancewar a blanket take ya saka tayi saurin kife wayar tana rufe idanunta. Bathroom ya shige abunsa, da sauri ta tashi ta nufi ma'ajiyarta, abinda Aunty Sadiya ta bata ta dauko ta shafa sannan tasha na sha, murmushi tayi bayan ta tuno abinda Aunty Sadiya ta ce da ita akan maganin me suna "Lock him! Make him yours only" Shu'umar Humrah ta shafa, tana kokarin kwanciya ya fito daga toilet, kallonsa ta tsaya yi na yan seconds sannan ta ɗauke kanta ta kwanta tare da addu'ar Allah yasa kwana zeyi anan kar ya cuceta ya saka tayi asarar maganinta dan Aunty Sadiya ta ce mata maganin da tsada sosai, tasan idan tayi waisting ɗinsa ubanta zata ci. Nafilfilu yayi sai kusan 3pm sannan ya kwanta, Hajiya bilkisu tuni bacci ɓarawo ya ɗauketa. Ammar can't hold it anymore  and he spends the remaining hours with his uwargida. Washe gari da safe Zarah na zaune a gefan gado tana shirya yaronta, Raihan ya shigo yana kallonta. Murmushi tayi masa kaɗan tana fad'in " Har ka tashi? Shuru yayi dan ba magana yake ba. "Zo" Ta fada tana miƙa masa hannu. Ba musu yazo inda take, a kan gado ta ɗorashi tana fad'in " Anyi maka wanka? Nan ma shuru bai ce komai ba. Murmushi tayi tana tube mesa kayan dake jikinta ta shiga toilet dashi, few minutes suka fito ta naɗeshi a towel sai dariya take yayi wasa da ruwa, mai ta shafa masa ta shirya shi tsaf cikin new clothes na Hydar wanda babansa ya kawo masa daga America yace idan ya ƙara wayo a saka masa. A nan gadon ta barsu bayan ta bashi abin wasa, bathroom ta shiga tayi wanka abunta ta. Cikin few minutes ta shirya dan ba kwalliya tayi ba kwalli kawai ta saka a idanunta sai Vaseline a lebanta. Tsaf ta fita abunta natural kyanta ya ƙara bayyana. Hydar ta ɗauka tana riƙe hannun Raihan suka fito daga ɗakin. Bilkisu na falon tana serving ɗin Ammar breakfast. Ɗagowar da zatayi ta gansu, serving spoon din hannunta ta ajiye ta nufesu da sauri ta kwace hannun ɗanta tana fad'in " Dan Allah bana son fitina da safen nan! Me hadinki da Raihan? And those clothes? Oh so kike ki nuna min kina son ɗana? Shine kika bashi kaya? Kayan ma ƴan gwanjo? Dan Allah Zarah kar mu fara wannan da safiyar na... "Me haka ne bilkisu? Komai sai kinyi magana a kai ne? Itama ai danta ne" "lala-lala! Ga dai danta a kafaɗarta amma wannan ɗana ne! Ba wani ne yayi min rainon cikinsa ba! Yaji min zafin haihuwar! "Toh ki godewa Allah, kinji Bilkisu! I have my own son on my shoulders! Kuma nima cikinsa na ɗauka har na tsawon wata 9 da yan sati! Kuma na sha wahalar labour! Na haifeshi! Zaki iya zuwa ki faɗawa wanda bai san zafin haihuwa ko rainon ciki ba! Cewar Zarah very calm tana kallon bilkisu. "Eh naji dai!  Kar a sake taɓa min yarona, sannan ko dakinki ya shigo ba ruwanki dashi dan gidan babansa ne dole ya wataya! Yo wani ma yayi rawa ballantana ɗan makaɗi! Daga haka ta juya zata wuce amma Zarah tayi saurin dakatar da ita da faɗin " Ni bazan tsayar chachar baki dake ba Bilkisu, Cox ɗa na kowa ne" Zarah ta ƙarashe maganar tana murmushi. "Ni yanzu banga abin magana ba anan Bilkisu, laifi ne dan ta saka masa kaya? "Bana so kawai! Kowa yaji da nashi yaron, ai itama tana da shi ko? "Ok amma kinsan ko da ace yaran sun girma bazaki raba tsakaninsu ba? "Bazai ma kai wannan girman ba zai koma wajen babansa" Zarah ta faɗa tana wucewa kitchen. "Yafi ai! Haka kawai a kawo mana agola cikin gida! "Bilkisu Allah ranki zai ɓaci akan kina yi wa Zarah irin haka! Kin sanni ko? Cewar Ammar ransa a ɓace "Nifa bazan zauna a cutar dani ba wallahi! Tunda ni ba matar so bace toh zan kwatarwa kaina hakkina" "Nifa ba ina nufin wani matar so wani matar ƙi ba! Gaskiya nake faɗa Miki! Kin fiya neman fitina Allah! Indai kina son zaman lafiya dani respect your self please! Kinsan wacece Zarah a wajena tun kafin auremu na fari! Please Bilkisu ki bari mu zauna lafiya a gidan nan dan Allah"  "Ikon Allah! Cewar bilkisu tana wucewa ta barshi a wajen. Tashi yayi yabi bayan Zarah. A jingine ya ganta jikin cabinet ta lumshe idanunta, "Zarah! Ya kirata. A hankali ta buɗe idanunta tana kallonsa. "Ki daina shigowa kitchen da Hydar kinji ko? Bata ce dashi komai ba ta gyara Hydar sannan ta goyashi da towel ɗin data rungumoshi. "Dan Allah ki daina biye mata Please Zarah for my sake kinji" "Ok" Ta amsa don so take ma ya kyaleta. "So, let me help you" Ya fada yana buɗe cabinet.. "Na gode, is ok I will manage" Ta faɗa tana karbar tukunyar daya fito da ita. Kwace tunkunyar yayi daga hannunta yana wurgi da ita, runtsa idanunta tayi tana matsawa baya da sauri, Kuka Hydar ya fara yi dan shi kanshi yaji tsoro.. kulle kofar kitchen ɗin Ammar yayi yana nufota ransa duk a ɓace ya ce, "Ki faɗa min me nayi miki Zarah? Kin ƙi sakin jiki dani! Wannan ce duk irin soyayyar da kike iƙirarin kina yi min? Haka zamu cigaba da rayuwar auren mu? Just two days of marriage kin fara batan rai! Me nayi miki? Ta yaya zaman mu zai yi daɗi idan nayi miki laifi zaki kullaceni baxaki sanar dani ba? Ganin ta fara hawaye ya saka shi shafa kansa yana ƙoƙarin ganin ya saita temper dinsa... "Look Xarah! Ya kamata ki sanar dani idan wani abu na miki, wallah Zarah kina bani wahala! From the apex of my heart Zarah wallahi bana jin daɗin yanayin nan, ki bani farincikin da kika min alkhawari mana! Ko dai kin daina sona? Ya karashe maganar yana kallon cikin idanunta. "I don't know either" Ta fada tana goge idanunta. Runtsa idanunsa yayi da ƙarfi yana budesu a kanta zuciyarsa na bugawa da ƙarfi sosai.  "Zarah are you kidding me? Bangane you don't know either ba! Are you hesitating on me? I mean my love? Are you serious? Please Zarah" Ya ƙarashe maganar yana riƙe arm ɗinta. "Nifa bance bana sonka ba, dan Allah mu bar wannan maganar" Numfashi ya sauke yana shafa karan hancinta zuciyarsa na bugawa da ƙarfi. "Banaso" Ta faɗa tana ɗan tureshi" tsayawa yayi yana kallonta kafin ya ce, "Bakyason ina taɓaki? But Why? Ke halal ɗina ce fa! Lokacin da baki zama halal ɗina ba ina taɓaki! Why aren't you complaining then? Is the feeling running away or what? "I'm starving! Daga haka ta nufi tukunyar daya wullar ta ɗauka tana nufar sink. Ƙarasowa yayi ya karbi tukunyar ya wanke yana fad'in " Bari na dafa miki indomie, akwai dubulan da alkaki, idan kina so na dibar miki kafin in gama" "No" Ta fada tana zama a kan kujera. Store ya shiga ya fito da indomie da albasa da eggs. Kwan ya dora a wuta sannan ya fara gyara albasa, lokaci daya idanunsa suka fara hawaye, ita dai idanun kawai ta zuba masa, yankawa ya fara yi lokaci² yakan runtsa idanunsa saboda zafi. Har ya kammala, zai zuba tayi saurin dakatar da shi da faɗin " Bana son albasa a ciki" Ƙuri yayi mata da idanunsa da sukayi jaa kaɗan. "Eh bana so, akwai mini Plastic rubber a cikin fridge ka juyeta a ciki. Da tohm ya amsa yana yin yadda tace sannan ya cigaba da girkinsa.. For almost 30mins suna zauna a kitchen ɗin har lokacin bai sauke indomie ba kuma bata ce dashi ƙala ba. "Zarah bata dahu ba? Cewar shi yana kallonta. Bata ce masa komai ba ta tashi ta nufi tukunyar ta kashe gas ɗin tana fad'in " Tayi" Tasowa yayi yana ɗauko plate, sosai indomie tayi over cooked ga ruwa yayi yawa, "Kamar ta dahu dayawa" Ya faɗa yana miƙa mata. Bata ce komai ba ta karba ta koma kan kujerar ta kai ƙaramar loma bakinta, salam ba komai a ciki. "Ka saka maggi? Ta faɗa tana kallonsa. A hankali ya Girgiza mata kai. "Kawo in tayaki kawo in tayaki! This is all what you can do? Ta ƙarashe maganar tana ajiye plate din hannunta. "Bazaki ci ba? "I'm ok thanks" "Please for the sake of our love zarah, wallahi girki da wahala, Please kici" "Gaskiya i can't! Ta faɗa tana fita daga kitchen ɗin. Ɗandana indomie yayi, kai ya gyada kafin ya saki ɗan murmushi dan baiga laifinta ba.. Ruwan tea ya ɗora kasancewa kaɗan ya ɗora da wuri ya tafasa, shayi me kauri ya haɗa mata sannan ya ɗibar mata dubulan da alkaki ya jera a tray ya nufi ɗakinta. A dan kishingiɗe ya ganta kamar dai waya take. Tray din ya ajiye yana kallonta da kyau ganin yadda take murmushi tana shafa kan Hydar. "Ok, yanzu Dubai zaku koma gaba ɗaya? Yaji ta fada tana kallon screen din wayar tabbacin vd call ne. Bayan second kmr 20 yaji ta sake cewa " Ok Allah ya bada Sa'a ya taimaka" minti kaɗan kuma yaga ta cire earpiece din kunnenta tana gyarawa hydar kwanciyarsa. "Da wa kika gama waya? Ya fada yana kafeta da idanu dan haka kawai yaji wayar bata kwanta masa ba. "Is non of your business Ammar! Wai meyasa kake haka? Ta faɗa tana ajiye wayarta. Ɗaukar wayar yayi yana kunnawa amma da Password, sunan Hydar ya gwada amma bai cire ba, sunanta ya saka nan ma bai fita ba. "Me password din? Ba tare da ta kalleshi ba ta ce, "Innata" bai ce mata komai ba ya saka abinda ta ce aikuwa ya bude.. call logs dinta na Whatsapp ya shiga, banda vds calls na Yaya❤️ babu abinda yake gani.. "Waye Yaya? Ya fada yana kafeta da idanu. "Wai dan Allah Ammar me yake damunka? Zargina kake ko me? "Just tell me! Nunfashi ta sauke tana ɗauke idanunta daga kansa ta ce, "Abban Hydar ne" "What! Cewar Ammar da ƙarfi! "Eh ai ba laifi bane dan nayi waya da ɗan uwa na! Ko ka manta shi din ɗan uwa nane? Kuma so yake yaga dansa zan hanashi ne? "But I'm your husband zarah! Inda right din da zance ki daina waya dashi! Idan ɗansa yake son gani ya dinga kirana zan nuna masa ɗansa but not him calling my wife! How Dear he? "Ammar Please! Mustapha dan uwa nane! Dan munyi aure mun rabu ba shi zaisa na daina kulashi ba kuma ba hakan ne zai baka damar rabamu ko tsanarsa ba! "Amma Zarah me hadinki da shi yanzu? "Au kana so in kara maimaita maka? Ok naw! He's my brother and the father of my child! "But I'm your husband! Na fishi iko da ke! "Dan Allah k daina yimin ihu Ammar! Bai ce komai ba ya zauna a gefan gado yana rike ƙansa da ya fara sarawa. Tashi Zarah tayi ta barshi a dakin.  Ya jima a zaune a ɗakin kafin ya fito, a zaune ya ganta tana kallo. "Kije kici abinci bakici komai ba tun safe! And I'm sorry for what happened earlier" Ko ƙala bata ce masa ba, shima bai ƙara cewa komai ba ya fice. Ɗakinsa ya nufa ya shiga toilet yana sakarwa kansa ruwa me sanyi sosai zuciyarsa ke bugawa  da karfin gaske, hango fuskar Zarah kawai yake daxun da take masa magana, be taɓa tunanin ta iya ɗaga murya haka ba, me yake damunta ne? Ina tarin soyayyar da take masa a baya? Meyasa duk ta canza masa lokaci ɗaya? Numfashi ya sauke yana kashe shower ɗin tare da faɗin " Ba mamaki saboda ban sanar da ita cewa zan mayar da bilkisu tun farko ba! But a yadda ya san Zarah tana da fahimta sosai! Towel ya daura a jikinsa yana fitowa, yana zama a gaban mudubi Bilkisu ta shigo riƙe da waya. "Yaya gashi Mami zatayi maka magana tace ta kira wayarka a kashe" Bai ce komai ba ya karbi wayar yana karawa a kunne.. "Yawwa, Ammaru!  kan maganar Fatima ce da kuma saukar yarinyar nan Maryam! Na saka Umar ya ciro kudi a family account, and sunce an cire 1.5m kusan 2yrs back, Kai ne ka cira? Sai daya dan kalli bilkisu sannan ya ce, "Eh Mami, dashi nayi using na biya kudin event na bikina da bilkisu! I'm sorry" "Ok saboda na takura maka? Ko saboda alert din ba wayata yake shigowa ba? "Ba haka bane ba Mami, banda kudin ne a wannan lokacin shiyasa" "Shikenan kayi kokari ka mayarwa yara kudinsu! Murmushi yayi kaɗan kafin ya ce, "Nifa? Ko bana ciki? "Ban sani ba! Kudin dai marayun Allah ne ba ruwa na" Mami ta faɗa daga ɗayen side ɗin. "Nima ai maraya ne Mami! Kuma nasan siblings ɗina zasu yafe min, after all waye yake juya musu kudin? Ina ce Umar ne? Kuma Umar ai twinny dina ne, ladan juyawar da baya ɗauka shi na ɗauka " "Ni dai ba ruwana, idan bikin yarinya yazo kai zaka yi kayan ɗaki" Murmushi yayi sosai har hakoransa na bayyana sannan ya ce, "Insha Allah Mom, me ya faru a kan Fatimah? Ɗaga ɗayan side din Mami ta ce, "Saurayinta ne yake so manya su shiga maganar, ina ce dai kayi bincike a kansa yadda ya kamata? "Eh Mami, amma zan cigaba insha Allah" "Good, next week saukar Maryam! "Allah ya kaimu" Ya faɗa yana ɗan jan numfashi. Sallama tayi masa tana katse wayar. Miƙa mata wayarta yayi yana fad'in " Get lost! Sim² ta fice dan bata son masifan shi. Kaya mara nauyi ya shirya yana kwanciya akan gado tare da lumshe idanunta, moment din ɗazu ne yake dawo masa! Ya kasa fahimtar meyasa Zarah take yin hakan! Haka suka yini a gidan zuciya duk ba daɗi. Washe gari da safe Zarah da shirin school ta tashi, tsaf ta shirya cikin uniform ɗinta ta ɗauki yaronta tare da jakarta. A compound din gidan ta tarar dashi yana exercise. "Na tafi" Ta faɗa tana kallon direction din da yake. Tsayar da abinda yake yayi yana nufin inda take... "Ok haka kika koma zuwa makarantar babu wani mayafi ko Abaya? "A'a Waheeda da driver suna waje suna jirana kaga ba yawo zanyi ba, sai zan dawo" "Yau ba zuwa makaranta, let's stay together please" Ɓata rai tayi tana kallon sa ta ce, "Mu fa ba'a fashi haka kawai kuma kasan muna posting idan ba'a ganina za'ayi reporting ɗina". "okay muje na baki kudi" "ina da kuɗi idan na dawo ka biyani" Ta faɗa tana kallonsa. " Au bashi kika bani? Bata ce komai ba ta wuce ta barshi. Murmushi yayi yana bin bayanta da kallo wai idan na dawo ka biyani! Murmushi ya sake yi yana fad'in "This girl!  Shima cikin gida ya koma yayi wanka tare da shirin zuwa aiki, Bilkisu ma fita tayi dan zasu fara shirin yadda shagalin sauka zai kasance. Ƙarfe 3 na yamma Zarah ta dawo a matukar gajiye, wanka ta fara yi sannan tayi wa Hydar, takeawaye ɗin da tayo a hanya ta zauna taci sannan ta ɗauki littafin ta ta fara dubawa saboda kwana biyu duk batayi karatu ba, sai kusan 6 sannan ta ajiye littafinta,  kallo ta kunna kafin a kira magariba. Bata daɗe tana kallon ba akayi kiran sallah.  Tana cikin athkar taji shigowar motar Ammar.. zuwa dan lokaci taji Muryar bilkisu tana fad'in " Yaya Maryam ta ce wai tana so ayi mata littafi ba memo ba" "Me marabar memo da littafin? She's not serious! Meyasa bata sameni da maganar ba? Taɓa baki Zarah tayi tana maida hankalinta kan abinda take yi. Bayan ta kammala Hydar ta dauko a bedroom sannan ta dawo falo ta sake kunna kallo. Tana cikin kallonta Ammar ya shigo yana sanye da jallabiya maroon.. kusa da ita ya zauna yana fad'in " Zarah yunwa" "Baka ci abinci ba daga inda kake? "Me kike so naci? Bayan zanzo na tarar da abinci a gida" "Nifa banyi komai ba dan na gaji takeawaye nayo naci, na manta yau zaka dawo nan da kai ma nayi maka" Idanun kawai ya zuba mata yana mamakin kalamanta. "Sorry" Ta furta tana cigaba da kallonta. "Ok ba damuwa" Ya amsa yana kallon TV. Few moments later ya karɓi Hydar dake hannunta ya wuce bedroom. Bai daɗe ba ya dawo yana zama a kusa da ita tare da janyota jikinsa.. "Ka matseni! Ta faɗa tana son raba jikinsu" "Ok kiyi hakuri! Ya fada yana kara matseta a jikinsa. Ji tayi kamar ta rusa kuka dan har ga Allah ita bata son yana taɓa ta. "Zarah dan Allah ki yafe min duk da bansan laifi na ba, dan Allah! "Nifa baka min komai ba kawai ka cikani"  "I can't" Ya fada yana sumbatar goshinta. "Dan Allah ka cikani zanyi sallah" "Lokaci be karasa ba Zarah, idan kina so na sakeki sai kin fada min laifi n" Tana kokarin yin magana ya haɗe bakinsu! Numfashin ta ne ya ɗauke na ƴan seconni sosai ta zaro idanunta! Lokacin data dawo senses ɗinta ta fara kokarin sauke numfashi tana son tureshi but Ammar doesn't give her that chance. Americans kiss yake bata, he never knew the thing sweet like this! Komai dama idan kana zeal ɗin yinsa yafi maka daɗi, daɗin daɗawa he's together with the love of his life, his joy giver, his Noor Aiyn...hular kanta ya cire yana shafa kanta cikin salonsa, a hankali Zarah ta rufe idanunta tana jin tsikar jikinta na tashi, Zuciyarta na bugawa da karfi, respiration rate dinta na raising and falling very fast. Kallonta ya tsaya yi na ƴan dakiku kafin ya rungumeta yana shafa kanta, gaba ɗaya jikinta yayi laƙwas, hakan yasa ta sakar masa jikinta tana sauke numfashi a hankali.  Zip ɗin jikin rigarta ya fara zugewa, a kasalance ta riƙe hannunsa tana buɗe idanunta a hankali. "Few minutes then I'm done Zarah please ²" Numfashi ta ja me nauyi tana saukewa a hankali ba tare da ta iya ce mishi komai ba. Shima bai cigaba da abinda yake ba yayi hugging din ta kawai! Ya daɗe yana jiran rana irin ta yau! Amma meyasa zata tsayar dashi? Or isn't she ready to accept him? Ajiyar zuciya ya sauke dan bashi da amsa. Sai kusan 9pm sannan Ammar ya tasheta ta wuce bedroom. Fita yayi daga dakin sai daya kullo ko ina sannan ya tafi ɗakinsa, daga nan kitchen ya nufa ya haɗa ruwan tea yasha da bread sannan ya nufi ɗakin Zarah! Yasan idan ya tafi ɗakinsa Xarah bazata biyoshi ba kamar yadda Bilkisu take Sometimes! A kan sallaya ya ganta har ta fara bacci. "Zarah! Tashi ki hau gado" Da kyar ta iya buɗe idanunta sannan ta mike tana cire hijabin jikinta ta hau kan gado. Shi ya ɗauke abun sallar. Gadon Hydar ya dawo dashi ƙasa bayan ya ciro blanket guda biyu na shimfida a kasan tiles din. "Meyasa zaka sauke min yaro? Yaji ta faɗa a kasalance. "Kin fi kowa sani Zarah, insha Allah gobe zan siyo masa crib ki dinga saka shi a ciki" Bata ce komai ba ta ja duvet. A gabanta ya kwanta yana buɗe duvet din tare da kafe fuskarta da idanu. "Zarah! Ya kira ta sigar magiya. "Bata kulashi ba dan bata so yayi distracting baccinta. Hannunsa ya dora akan cikinta ya shafo a hankali yana kallon fuskarta. Kasancewar bata kulashi ba ya bashi daman cigabawa, within some minutes Ammar losses his control, rough and hot romance yake yi wa Zarah, tun bata feeling any sensation har jikinta ya fara ɗaukar sakonnin da Ammar yake aika mata. He left her with nothing sai duvet daya rufeta dashi... Zuwa ɗan wani lokaci Ammar feels like he can't do anything, runtsa idanunsa yayi yana jin gabansa ya fad'uwa sosai, he tries so many time amma the pn is not given any sensation! Rumgumeta yayi yana sauke numfashi me karfi, hawaye Zarah ta fara yi tana jin bugun Zuciyarta na ƙaruwa, ya kaita matakin da ta kasa jure condition din da take ciki, ji take if nothing happens she can die! Shi kanshi ya lura da halin da take ciki. Kansa yaji ya fara ciwo, he never experienced such kind of thing before, numfashi ya sauke yana buɗe idanunsa akan Zarah, bashi da choice sai dai ya cigaba da trying! He just can't believe this is happening! Duk trying ɗin da yayi beyi aiki ba, sai kara tabo Zarah kawai yake yi! Ta yaya zai yu ace iya wajen ne baya jin sensation? Daga lower abdomen do sa zuwa karshen long bones dinsa? "I'm sorry Zarah! Ya faɗa yana rumgumeta sosai. Kuka ta fashe dashi tana riƙeshi jikinta na rawa kamar wata me jin sanyi. Da kyar Ammar ya samu yayi calming ɗinta, har asuba Ammar kasa bacci yayi saboda tunanin condition ɗinsa, sam be taba fuskantar wani abu makamancin hakan ba. Kiran sallar asuba da akayi ne ya saka ya bar gadon ya nufi ɗakinsa. After like 30mins ya dawo ɗakin Zarah, cikin rashin kwarin gwiwa ya ce, "Zarah lokacin sallah yayi" Tana jinsa amma tayi shuru, even though Jiya she isn't on her Senses but tana recalling wasu abubuwa.. "lokaci n ƙurewa shida ta kusa" "ok" Ta amsa a hankali. Fita yayi daga bedroom ɗin ya koma falo. Wanka tayi sannan ta dauro alwala tayi sallah.  Komawa tayi ta kwanta tana rufe idanunta dan bacci take ji.. sai 7 da rabi ta tashi, hakan ma baccin be isheta ba, shirin makaranta tayi, sannan ta shirya ɗanta, saƙon Ammar ta karanta a waya, ajiyar zuciya ta sauke tana daukar Hydar sannan ta fito. A falo taga Bilkisu tana breakfast. "Barka da safiya" Cewar Zarah ba tare da ta tsaya ba. "UHM! Bokoko! Soon makarantar zata gagareki wallahi! Ita dai Zarah bata ce komai ba ta fice dan tasan babu wanda ya isa a cikinsu ya tsayar mata da karatun ta.

      Ammar kuwa cike da damuwa ya kammala yi wa likitan bayani yana jiran yaji mai zai ce. "Toh Dr. Ammar, baxan iya cewa komai ba a condition dinka, kaga har haihuwa ka taɓa yi suddenly abun ya faru jiya, kuma baka taɓa experiencing rashin karfi a da ba ko? "Yes! Ya bashi amsa. ' Akwai tests da zakayi da kuma x ray idan da akwai abu matsala duk zamu gani, if possible kaje kayi yau saboda matsalar nan babbar matsala ce ka sani ba sai na faɗa maka ba" "Na sa ni Dr. Insha Allah anjima zaka ganni Na gode" Handshake sukayi sannan Ammar ya baro office ɗin. Kafin yamma yayi duk abinda zaiyi, a nuste ya zauna ya duba duk wani sakamakon da aka bashi, komai ya nuna normal ba matsala, amma ya akayi hakan ta faru? Ajiye sakamakon yayi a mota da niyyar gobe zai koma wani asibitin ayi masa wani, but first zai fara kaiwa DR din daya ganshi dazu ya gani tunda abinda wancan doctor din ya karanta kenan. Ya ɗan jima a cikin mota yana tunanin yadda zai yi confronting din Zarah. Daga karshe dai dole ya fito yana shiga cikin falo. Zarah na kitchen tana girki dan yau bata dawo da wuri ba sun tsaya group discussion. Ganin kitchen ɗin nata a buɗe ya saka shi nufar kitchen ɗin bayan ya ajiye jakar hannunsa a kan kujera. Daga bakin kofa ya tsaya yana kallonta, Zarah bata yarda ta juyo ba ta cigaba da aikinta cikin nutsuwa. Ajiyar zuciya ya sauke dan ya gane avoiding din eye contact take yi dashi. Ƙarasa shigowa yayi yana dan gathering din courage ɗin da ya rage masa ya ce, " Ya School ɗin? "Lafiya lau sannu da dawowa' Bai amsa ba sai ƙarasa inda take  yana karɓar wuƙar hannunta ya ce, "Bari na tayaki me zan yanka? " Yanzu fa ka dawo kaje ka huta na kusa kammalawa" Ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba. Hugging dinta yayi backward yana sauke numfashi a hankali, kamar me rada ya ce, "Forgive me Zarah" Zarah ji tayi kamar ta ruga da gudu, ita sam bata son ana dawo da hannun agogo baya. "Are you angry? Ya sake faɗa yana kallonta. "Ammar dan Allah ka bari! Meyasa kake son dawo da abinda ya wuce? Please leave! Ta faɗa a ɗan zafafe. "Na san fushi kike yi, but I'm not at fault Zarah, Bansan me ya sameni ba all of a sudden! Ni na san I'm n... "Dan Allah ya wuce! Ta faɗa tana dakatar dashi tare da kokarin kwace jikinta. Sakinta yayi yana sauke ajiyar zuciya a hankali. Fita yayi ya barta da jan tsakin da bata san dalilin yin sa ba. Bayan ta kammala girkinta ta zuba masa a plate ta haɗa komai a tray ta fito. Bilkisu ta gani a falo tana kallo, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Har ta kusa isa door dinta taji Bilkisu ta ce, "Ansha amarci! Sai kuma ta kyal-kyale da dariya. Zarah bata kulata ba ta wuce dakinta. Bata tarar da Ammar a ciki ba. Sake fitowa tayi ta shiga bedroom dinsa, yana kwance har ya sauya kaya zuwa jallabiya. "Ga abinci" ta furta tana ajiye tray ɗin a ƙasan rug. "Ok na gode" kai kawai ta gyada tana fita abunta. Bayan Isha'i tana zaune tana karatu saboda nan da one week zasu fara second semester second year examination. Shigowar Ammar ya saka ta kalli kofar ɗakin. Shafa kansa yayi yana ƙarasowa inda take ya zauna, calmly ya ce "Gobe idan kin dawo daga school zamu je gidanmu ki gaida Mami" Gaban Zarah ne ya fadi, shi kanshi ya lura da sauyin yanayinta. Hannunta ya riko yana ɗan murzawa a hankali ya ce, "Don't be afraid mana, Mamina fa nace ba Aunty Sadiya ba" Kamar zatayi kuka ta ce, "Seriously I'm afraid of what might happen" "babu abinda zai faru, ba daɗewa zamuyi ba, sai bayan Isha'i ma zamu je Kinga ba zancen daɗewa" Kai kawai ta gyada masa. Murmushi yayi yana fad'in " Good girl, next tomorrow idan Allah ya kaimu sai muje gidan Hajiya Babba" "Tohmm" ta amsa tana za me hannunta daga cikin nashi. "Exams zaku fara ne? Though dai naga kina da nacin karatu amma this is different" "eh shi zamu fara" Kai ya gyada yana karɓar handout din hannunta ya fara dubawa, bayan ya kammala dubawa ya shiga yi mata bayani hakan ba ƙaramin taimaka mata yayi ba dan dama ba wani gane Pharmacology take sosai ba, cikin ƙanƙanin lokaci ta fara ɗauka dan sosai Ammar ya san simplest way da zai koyar da mutum ya gane, around 11pm suka kammala sai hamma take dan ita bata taɓa daukar wanann awannin tana karatu ba.  " Yanzu faɗa min, idan kikayi graduation zaki cigaba? "A'a bazan iya ba na gaji kuma" Murmushi yayi kaɗan yana ɗorawa da faɗin " ina ganin idan kika cigaba zaifi, sai kiyi degree ki zabi course ɗin da zaki karanta, kinga idan kikayi zurfi sosai sai ki nemi lecturing is better akan aikin asibiti" a hankali ta gyada masa kai amma sam bata ɗauki abinda ya faɗa ba. "Good nite" ta fada tana barinsa a wajen. Ammar bai kwanta ba sai 2am, ko yunkurin taɓa Zarah beyi ba Cox now he's even afraid.....

Autarmama ce

MATANA ✓Where stories live. Discover now