Chapter fifty two

629 42 13
                                    

✨ *MATANA* ✨

*Mallakar*
       AUTAR MAMA

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Comments*
*Vote &*
*Share fisabilillah*

: Assalamu alaikum wa rahmatullah.

Na ce bara in tunasar daku cewar na shirya aji tsaf don ci gaban mata iyayen gida,A wannan lokacin da sanyi yayiwa mata yawa a matsayin ki na mace yaya kike kula da kanki don kariya daga ɗaukar cutar sanyi ko da mai gida ya na ɗauke da shi?
: Shin kinada labarin sai kin isa ake tafiya dake? Aure nawa ke suke mutuwa saboda mazaje sun gaji da rashin damun isashiyar gamsuwa awurin matayensu?
Da yawan mata basuda labari game da kansu ma bare su nemi maganin matsalar su abu ɗaya suka sani sanyi ko dryness
Kina zaune kinashan maganin da ba shine matsalar taki ba
Kiyi ƙoƙarin shiga wannan ajin da naira dubu ɗaya jal, inda zaki mallaki ilimin da babu mai ƙwace miki shi har abada; A wannan ajin namu zamu baki ilimi akan sanin wace kalar macece ke acikin mata, menene matsalar ki a ɓangaren jikinki, yanda zaki kula da kanki a lokacin saduea da bayan saduwa, dabarun samun gamsuwa yayin jima'a musamman da ragon namiji.
Hanyoyi inganta tukunyar gidan ki, zamu kawo daɗaɗan abubuwan da zasj taimakawa mai gida idan kin mishi ya dawo da ƙarfinsa, ga koyar da kayan mata najinna faɗa daga er mutan sokoto 👍🏻👍🏻👍🏻
Duk fa wannan akan kuɗi naira dubu ɗaya kacal!
To me kike jira? Maza hanzarta biyan kuɗinki ta wannan asusun akawunt ɗin
Tallafawa tukunyar azuminki ta hanyar koyar dake ƙayatattun girke girke, shu'umar humrah da kuma kulacham ga turaren tsugono don zama tauraruwa👍🏻👍🏻👍🏻
Duk fa wannan akan kuɗi naira dubu ɗaya kacal!
To me kike jira? Maza hanzarta biyan kuɗinki ta wannan asusun akawunt ɗin Saiki tura shaidar biya ta nan👉🏻 07084161619.
Na gode.
2073065733
UBA BANK
SHA'AWA IBRAHIM

*052*

        Haka suka wuni a gidan, gaba ɗaya Maryam taƙi sakin jikinta banda kudunduna cikin bargo babu abinda take tun isowar su. Bayan sallar Isha'i tana kwance har bacci ya fara ɗaukarta taji shigowar shi. Da sauri ta buɗe idanunta tana tashi zaune. Murmushi ya ɗanyi yana fad'in "Meyasa baki ci abinci ba? "Bana jin yunwa" Ta amsa ba tare da ta kalle shi ba. " Okz tashi kiyi alwala" "Nayi sallah' Ta amsa da sauri. "Na sani   wata zakiyi ina jiranki"  bata ce komai ta miƙe ta wuce toilet bata ɗau lokaci ba ta dawo. Hijabi ta saka sannan ta kalleshi ta ce , "Nayi" da ok ya amsa yana ajiye wayarshi. Shima alwalar ya shiga yayi sanann ya fito ya jasu sallah. Bayan sun idar yayi musu addu'o'i sosai, duk abubuwan da yayi mata tambayoyi a kan su ta amsa su tas kuma sosai yaji daɗin hakan. Ta shi tayi bayan ya umarce ta da tashin. Fita yayi be daɗe ba ya dawo da plate. Kaza ce an yayyanka ta sai khamshi take. Ajiye mata yayi yana fadin "Kici ki kwanta" da toh ta amsa. Fita yayi ya bata waje. Sosai taci kazar dan dama rabonta da abinci tun safe.  Lokacin daya dawo ɗakin tayi bacci. Kashe wutar ɗakin yayi ya shiga toilet be ɗau lokaci ba ya fito ya shirya cikin night wears sannan ya kwanta a gefanta. Rabon daya samu nustuwa irin wannan tun lokacin daya auri Zarah kafin ta fara masa rashin m. Lumshe idanun shi yayi, komai da sanadin shi, a lokacin da suka rabu da Zarah gani yake bazai ƙara samun macen da zai so ba gani yake babu wani gurbi da wata zata iya samu a zuciyarshi. Buɗe idanunshi yayi a kanta, duk ta takure waje daya. Cire duvet ɗin yayi yana janyota jikinshi. Ajiyar zuciya ya sauke me karfi. Ita kuwa Maryam wani irin faduwa gabanta yayi dan dama baccin duk a tsorace take yi, ita duk Fatima ce tabi ta ruɗa ta, da ta sani ma bata saurareta ba. Ganin yana murza hannunta ya saka ta buɗe idanunta tana kallon shi ta ce, "Bana iya bacci da mutun a kan gado" ɗauke idanunta tayi ganin ya kafeta da nashi idanun. Murmushi yayi yana fad'in "Dole zaki koya, ko so kike mijinki ya  dinga tafiya wani ɗakin ya kwana? Da sauri ta ɗaga kai alamar eh..gaba ɗaya ya fahimceta tun ba yanzu ba. Gently yayi wrapping hannayen shi a ƙugunta  yana kallon Fuskarta ya ce, "Don't be afraid Hun? Kamar zatayi kuka ta ce, "Dan Allah ka sakeni" "I won't, ki kwantar da hankalinki ko wace mace da kika gani da haka ta saba" "Ta saba da me? Maryam tayi subutul kalam. Dariya yayi me sauti kafin ya kalleta ya ce, "Kwana da mijinta" Rufe idanunta tayi dan kunya ce ta rufeta, ji take kamar ta ruga a guje. Hira ya fara yi mata, a hankali ta fara sakin jikinta dan ta ɗauka babu abinda zai mata a yau ɗin dai. Zance ne ya fara sauyawa tun tana karbar sakonnin daya ke aikata mata har ta shiga kiran su Zarah! Kaf danginsu wanda ta sani babu wanda bata kira ba, tun tana yi da zazzaƙar murya har muryarta ta dashe. Gaba ɗaya ta rikita kanta.. ko da komai ya zama steady bata ji irin mugun ciwon da Fatima take faɗa mata ba, tabbas ta ji zafi but ba kamar yadda Fatima ta shirga mata karya ba. Abinda yake bata tsoro bata ga wani stain na jini ba kamar yadda Fatima ta faɗa mata. Sosai hankalinta ya tashi saboda ita har ga Allah Mustapha ne namijin daya fara sanin ta a ƴa mace, kuma meyasa bata ga stain din jini ba? Tun fitowarta daga bathroom take wannan tunanin, tsoro duk ya kamata kar Mustapha yayi mata wata fassarar. PCM taga ya miƙo mata yana fad'in "Kisha" hannunta na rawa ta karba tana sha sam ta kasa nustuwa. Gefenta ya dawo yana rungumota jikin shi ya ce, "Allah yayi miki albarka Maryam, na gode sosai da wanna babbar kyautar" Shuru tayi tana jin zuciyarta na bugawa ko dai bak'ar magana yake fada mata? Hawaye taji ta fara yi, ita dai a iya saninta bata taɓa aikata wani abu makamancin abinda ya faru tsakaninta da mijinta ba yau, toh meyasa bata ga jini ba? "Kukan me kike? Ya faɗa yana juyo da ita suka fara facing ɗin juna" kasa cewa komai tayi duk a tsorace take dashi, dan bata san kallon da yake mata ba a yanzun. "Sorry a hankali zaki saba kinji ko? Cewar Mustapha dan yayi tunanin pain ɗin take wa kuka. Bata ce komai ba ta lamo a jikinshi. Sam kasa bacci tayi har asuba. Bayan ya ja su sallah komawa bacci yayi. Ita kuwa cikin ƙarfin hali ta sakko daga kan gadon ta ɗauki wayarta dake charji ta fita falo. Number Fatima ta fara kira. Kamar jira take aikuwa ta ɗauka tana fad'in "Yanzu nake son kwanciya bacci nace gobe da rana na kiraki" " Yanzu na tashi, Fatima wallahi ina cikin tashin hankali" Cewar Maryam cike da damuwa. "Lafiya? Fatima ta faɗa gabanta na fad'uwa. "Wallahi bangaa jini ba kamar yadda kika faɗa min ina jin tsoro kan yadda zai ɗaukeni" "Eh ance wasu matan ba'a ganin jini ki kwantar da hankalinki ai shima bazai rasa sanin hakan ba tunda wayayye ne" "Amma Fatima ta yaya zai sani? Wallahi ina jin tsoro" "Ki kwantar da hankalin ki babu komai kinji ko? Maryam bata gamsu ba ta kashe wayar. "Menene? A tsorace ta juya tana kallonshi. "Fatima ce" Ta faɗa muryarta na rawa. "Tsoron me kike ji? Sunkuyar da kanta tayi ta kasa cewa komai. "Kar kiji tsoro, duk da bansan a kan me kuke magana ba, I'm here for you kinji ko?  Kai ta gyaɗa alamar toh. "Taso ki kwanta kina bukatar Hutu" hannunta ya riko zuwa ɗaki. Kwanciya tayi shima ya kwanta. WiFi ta kunna taga da password. Ɗan kallonshi tayi ta ce, "Menene password ɗin WiFi? Murmushi yayi yana fad'in "Bazakiyi bacci ba? Da Eh ta amsa masa. Password ɗin ya faɗa mata tayi connecting sannan ta shiga Google. Sosai ta dinga research akan rashin ganin jini a first night, kuma ta samu gamshasshiyar amsa akan lamarin. Yanzu dai tana fatan ace shima ya sani amma ga dukkan alamu zai iya sani tunda dai bai canza mata ba. Sai a lokacin ta samu ɗan relief ta fara jin bacci. Bata tashi ba sai azahar. Bata ganshi a ɗakin ba hakan ya bata damar sakewa tayi wanka sanna ta shirya cikin doguwar riga. A falo ta same shi yana kallo. Zama tayi a gefan kujerar da yake tana fad'in "Yunwa nake ji" "Sorry, bari na kawo miki abinci" daga haka ya mike ya shiga kitchen. Bai ɗau lokaci ba ya dawo. Shayi kawai ta sha ta bar kazar. Suna zaune anan bacci ya sake ɗauketa. Rungumota yayi jikinshi yana cigaba da kallon shi...

MATANA ✓Where stories live. Discover now