✨ *MATANA* ✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*Comments*
*Vote &*
*Share fisabilillah**033*
*Two days later*
Zarah na kwance a kan gado tana latsa wayarta lokaci² takan ɗago ta kalli ball ɗin da Ammar yake kallah a TV. "Ina so zanje wajen Ummi" Ta faɗa tana mai da dubanta kan shi. "Ummin da kullum sai kun haɗu a asibiti? "Ai dai ya kamata naje in da take, yau kwananmu nawa amma ban taɓa zuwa ba" banza yayi mata ya cigaba da kallonsa hankalin kwance. "Magana fa nake" cewar Zarah cike da jin haushi. "Babu inda zakije" Ɓata rai tayi tana ajiye wayar hannunta takaici duk ya cikata. Ɗan juyowa yayi ya kalleta, bai ce komai ba ya juya ya cigaba da kallonsa. Itama bata kara kulashi ba ta koma ta gyara kwanciyarta tana jan duvet. Ya daɗe yana kallo sannan ya kashe, toilet ya shiga yayi wanka kafin ya dawo gefanta ya kwanta, so yake yayi bacci kafin la'asar. Tashi Zarah tayi tana ƙoƙarin sauka daga gadon, "Ina zakije? "Zan kwanta a kan couch" "Couch? Matsarki nayi akan gadon? Menene matsalarki ne Zarah? Tun shekara jiya nake lura dake? Me nayi miki? "Nifa bance kayimin wani abu ba, kawai kwana biyu nafi son kwanciya ni kadai" Numfashi ya sauke yana tashi zaune tare da yaye duvet ɗin ya ce " Shikenan kwanta ni zan kwanta a kan Couch din" Daga haka ya miƙe yana nufar kan couch.. kallonsa ta tsaya yi daga bisani ta koma ta kwanta tana lumshe Idanunta, ita bata san ta inda zata bullowa lamarin nan ba! Idan tace bata bukatar mijinta to tayi karya! Amma ya zatayi? Tashi zaune tayi tana sauke numfashi, ta daɗe a zaunen Ammar kuwa har bacci ya daukeshi dan dama beyi wani bacci jiya dadaddare ba. By 4 ya tashi, a kwace ya ga Xarah ta takure waje ɗaya bacci ya ɗauketa. Daf da ita ya matso yana kallon ta, shi baisan me yake damunsa ba! Meyasa sai a kan abar kaunarsa? Why not Bilkisu? Dole ya nemi mafita, idan sun koma Nigeria zai samu Umar ko zai samar masa mafita, bazai yu ya cigaba da rayuwa da yar mutane cikin wannan yanayin ba yasan yana cutar da ita, kuma ya hallata raba auren which he can't take bazai taba iya rabuwa da Zarah ba, shi kadai yasan yadda take a wajensa. Slowly ta fara buɗe Idanunta, a kansa ta sauke, gaba ɗaya taga kamar hankalinsa baya kanta yayi nisa a cikin tunani, Ƙoƙarin tashi zaune take hakan ya dawo da Ammar daga cikin duniyar tunanin daya tafi. "Barka da tashi" Ya fada dan ya rasa abun cewa. "Uhmm" Zarah ta amsa tana gyara hular kanta. Nunfashi ya sauke yana zama gefan gadon, ita kuwa tashi tayi ta wuce bathroom, bata daɗe ba ta fito, cikin simple dress ta shirya tana pinning din veil ɗinta Idanuwanta a kansa ta ce, "Mu tafi" "Ok, but kafin nan zauna muyi magana" "wace magana kuma? Ta faɗa zuciyarta na ɗan bugawa. "Idan kin zauna zaki ji. Bata sake yin musu ba ta nemi waje ta zauna. Hannunta Ammar ya riƙo yana kallon cikin Idanunta tare da kiran sunanta. Bata iya amsa masa ba sai sauke Idanunta da tayi daga kallon nashi idanun.. "Nasan abune mai wahala a wajenki kuma da wahala ki iya fitowa kiyi min ƙorafi, ba mamaki kina wani tunanin chan daban a kaina wanda sam ba haka bane, amma kuma banga laifinki ba but inaso ki sani bana yin komai dan na cutar dake, nima bansan me yake damuna ba, ban taba fuskantar irin wannan ba, kuma naje likitoci sun dubani an tabbatar da lafiya lau nake, bansan da wani bakin zan miki bayani ba, amma ina fatan ace zaki fah... Bata barshi ya ƙarasa ba ta miƙe tsaye tana fad'in "Bakomai" Shima miƙewar yayi yana kallon ta da kyau ya ce, "Akwai komai Zarah! Rayuwarmu ba zai yu a haka ba, Ni bazan iya rabuwa dake ba kuma bazan iya zuba miki idanu naga kina cutuwa ba" "Dan Allah maganar ya wuce, mu tafi" Kai ya girgiza mata yana sake kamo hannayenta ya rike, Idanuwan shi a kan fuskarta. "Bata wuce ba, kuma bazata taɓa wucewa ba, nifa mijinki ne, idan bamu zauna muyi resolving issue ɗin nan ba waye zai mana resolving ɗinsa? Naga kamar bakya son zancen, it seems like na fiki damuwa ko? "Ammar ya zamuyi? Nifa banda wata Idea a kan wannan issue ɗin, is better kawai ka fara shan maganin sanyi" Murmushi yayi kaɗan ganin ita fa dagaske take, amma shi yasan ba wani sanyi, tunda he's not week indai a wajen Bilkisu ne! Ajiyar zuciya ya sauke yana Gyaɗa mata kai alamar shikenan. "Ki nemo min" Ya faɗa yana jan hannunta suka fito daga ɗakin. Da ok kawai ta amsa zuciyarta fal tambayoyin da bazata iya furtasu ga Ammar ba.