Chapter six

672 37 6
                                    

✨ *MATANA*✨
 

*Mallakar*
       AUTAR MAMA

*FREE BOOK*

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

*Wannan labarin ƙirƙirarre ne, banyi shi ɗan cin zarafin wani ko wata ba! Sannan idan yayi shige da labarinka/labarinki coincidence ne Yawwa*

*Comments share and vote dinku yana da matukar mahimmanci idan yayi karanci zan maida abuna ba kudi💃*

*Whatsapp group females only please*

https://chat.whatsapp.com/Ib3gwXORbTB1GxcVr0FdAw


*006*

       Washe gari da misalin ƙarfe huɗu na yamma aka fara shirin tafiya kai amarya. Tsaf ta shirya cikin lafaya me kyau da tsada, sai khamshi kawai take zubawa, Aunty Khadija na kallonta ta ce, "Tabarkalla Masha Allah" "Aikuwa dai Bilkisu ta kai duk inda ake so Khadijah! Mace iya mace, kyau iya kyau jinin labarawa" ita dai Bilkisu sai murmushi takeyi.. jin uwar mijinta na yabonta. Ni kuwa nace zaki gane.. lol.. Fa'iza ce ta shigo tana fad'in " Wai su baffan na jira" "Je kice tana zuwa" Cewar Aunty Khadija. Kallonta Mami tayi tana fad'in " Duk abinda yayi miki karkiji ɗar kirani ki fada min kinji ko? Karki yarda ki bashi space din da zai dinga samun lokacin waccan mayyar dan nasan ba rabuwa dashi tayi ba, karki yarda ki bashi wani space, kuma ki rike abubuwan da muka gaya miki kinji dai ko? A hankali ta ce, "Insha Allah Mami" "Yawwa, girkin nan dai me dadi zaki dinga daurewa kina masa naji uwarki tace ganda ce dake, toh ki cire wannan gandar dan ubanki, Ammar yana son cin abinci me daɗi ki kula da cikinsa yadda ya kamata kin jini ko? Murmushi tayi ta ce " Toh Mami! Mami bata kara cewa komai ba ta rufe mata fuska ta rikota har wajen su Baffah.. Nasiha me ratsa jini da jiki sukayi mata kafin a dauketa zuwa gidan mijinta.. sai a lokacin gabanta ya fara faduwa, ita ko da chan basu da wani good time da Yaya Ammar. Duk hirar da su Fatima sukeyi jinsu kawai takeyi sai yanzu ta fara tunanin yadda rayuwar aure zai kasance tsakaninsu, ita kanta sheda ce akan yarinyar da yake so kullum bashi da zance sai na Zarah, karamin tsaki tayi aranta.. tunani dai kala² a haka har suka isa gidan. Fatima, Fa'iza da kuma Maryam kaɗai aka bari duk an hada kan yara an tafi.. har 10:30pm shuru kake ji kamar an shuka dusa.. Ammar kam yana dakin Umar sai trying number Zarah yake Amma bata shiga. Umar dake tsaye kansa ya ce, "Kasan Allah ranka zai ɓaci? Are you out of your mind zaka zauna anan har 11 saura? Shima cikin faɗa ya ce, "Can't you see I'm busy? Or are you blind? Fita Umar yayi daga ɗakin ransa duk a ɓace.. tare da Hajiya babba suka dawo.. itama fuska atsuke take kallon Ammar da yayi saurin tashi tsaye bayan ya ganta. "Raina mutane kayi da zan fada maka magana tun dazu kuma kaki bi? Narkar da fuska yayi yana matsowa inda take ya ce " Hajiyaaaa! "Bana son shiririta Ammar, ka shirya ina jiranka a falo" Daga haka ta fita. Closet Umar ya nufa ya ciro masa kaya yana fad'in " Kayi sauri" Shima fita yayi daga dakin.. Fuska a murtuke ya fito bayan ya shirya.. kallonsa Hajiya babba tayi tana sakin fuskarta ta ce, "Ko kaifa, Dan Allah karka shigar mata da wannan fuskar kaji ko? Kuma bana son jin matsala daga ɓangaren ka! "Insha Allah" Ya fada yana nufar hanyar fita. Biyoshi Umar yayi sai da ya bari suka fito compound din gidan ya ce " Bance ina bukatar dan rakiya ba ai, nasan hanya  ina kuma da kafa da ido" Murmushi Umar yayi yana kallon sa har ya shiga mota mai gadi ya bude masa gate ya bar gidan. 11 ta wuce lokacin daya isa gidan. A zaune ya tarar dasu a falo kowacce tayi jugum². "Uban menene ya zaunar dauku har 11? Ya fada yana kallon su Maryam. "Dama kai muke ta jira, Mami tace kar mu taho sai kazo" cewar Fa'iza a dan tsorace. Karamin tsaki yayi yana cillawa Fa'iza makullin motarsa ya ce, "Idan kinga dama ki goga min mota a jikin wani wajen" Daukar makullin tayi bayan ta gama kallonsa kuma ta tabbatar be shigo da komai ba. Tashi tsaye tayi tana fad'in " Sai da safe Bilki" Kai kawai ta gyada musu. Ammar kuwa wucewarsa yayi ya barta a wajen kamar hoto. Bayan ya shiga bedroom kayan jikinsa ya cire ya kwanta akan gado yana lumshe idanunsa.. har 2 na dare beyi bacci ba, har lokacin kuma Bilki na falo. Tana son zuwa ta kwanta but they must share the same room, Mami tana sane tasaka aka yi mata jere adakinsa duk da cewa yaware nashi dakin amma Mami tace sam! Da kyar ta iya tashi ta nufi dakin dan bacci takeji sosai.. rike da waya ta ganshi yana latsawa.. a kan sofa ta zauna tana yaye lafayar jikinta tare da kwance dogon gashinta saboda tasha iska da kyau. Kashe wayarsa yayi yana gyara kwanciyarsa tare da rufe jikinsa duk da cewa garin da zafi. Bai daɗe ba bacci ya daukeshi. Kallonsa kawai takeyi daga inda take, ko wace mace daren aurenta na farko yana zuwa da tarihi amma banda ita, angon ma kamar baisan da wanzuwar ta a wajen ba. Tashi tayi ta fara warware lafayar jikinta.. closet ta nufa ta dauko gown na bacci ta sakka ta daure kanta ta saka hula sannan ta kwanta a gefansa, juya mata baya yayi dan kamshin da takeyi shi ya tasheshi.. itama baya ta juya masa tana dan turo bakinta.. gaba daya turarenta ya hanashi sukuni, wani irin khamshi take me sanyi da tsayawa a rai. Buɗe idanunsa yayi yana tashi zaune idanunsa akanta ya ce, "Kar ki kara saka wannan turaren! Tana jinsa amma tayi kunnan uwar shegu dashi.. "Are you deaf?! Ya fada da dan ƙarfi.. "naji! Ta amsa masa ba tare da ɗago ba, ita kam tasan turaren a jikinta yake ya kamata sosai and Me gyaran jiki ma ta bata ta cigaba da turarawa kuma bazata fasa ba. Gyara kwanciyarta tayi tana kara sauke ajiyar zuciya. "He can't sleep here besides her, tabbas he will ended up doing something that he won't forgive him self. Ni kuwa nace kayi dai ka gama ai. Tashi yayi daga kan gadon yana yaye duvet din data rufa dashi tana jinsa amma bata kulashi ba. Ficewa yayi daga dakin ya nufi spare room ya kwanta. Yana rufa da bargon yaji khamshin turaren bargon yake yi, Runtsa idanunsa yayi yana wurgi da bargo a tsakar dakin sannan ya kwanta yana lumshe idanunsa. "Don't let that night watse for nothing Bilkis! Make sure you try your best, make him your's! Maganganun mahaifiyar ya dawo mata kunnenta. Tashi tayi zaune tana tunanin yadda zata bullowa lamarin " She just can met him like a fool, she must come up with an idea" Ta kai kusan minti biyar tana tunani kafin idea tazo mata. Murmushi tayi ta tashi ta nufi bandaki, bata dade ba ta fito.. falo ta fito ta fara ihu tana kokarin shigowa dakin da yake tayi dan bai rufe kofa ba hakan yasa tasan ciki ya shiga. Already ya tashi dan da karfi tayi ihun farko.. "Me haka? Ya fada yana ji kamar ya kifa mata mari dan  takaici.. kukan shagwaba ta saki tana fad'in " Wallahi akwai aljanu a gidan nan! Murmushi yayi kadan kafin kuma ya hade rai ya ce " I'm not a kid Bilkisu! Malama jeki ki kwanta i have no time for your drama! Dakewa tayi tana hawowa kan gadon tace "Ba wasa nake ba, i heard some voices laughing, gaskiya i can't sleep alone" wani murmushin ya sake sakin yana kallonta ya ce, "Who taught you this? I'm 100% sure this is not your idea! "Wallahi idea tace! Ta fada tana kallonsa. Real definition of subutul Kalam kenan.. sam sai yanzu ta tuna katobarar da tayi. "Ina nufin ba wa.. Shiiiiiiiiii ya fada yana kafeta da manyan idanunsa. Hadiye yawu tayi ba shiri.. Fuska ya tamke sosai yana nuna mata hanyar fita ba tare da yace komai ba. Sim sim ta tashi ta fice duk takaici ya isheta. Nunfashi ya sauke ya komawa ta kwanta. He wish it was Zarah, ya Dade yana tsara rayuwarsa da ita, ya dade yana imagine yadda first night dinsu zai kasance but Allah knows the Best.. tashi yayi ya dauro alwala. Ammar bai yi bacci ba sai bayan sallar asuba bacci me dadi ya daukeshi...

MATANA ✓Where stories live. Discover now