✨ *MATANA* ✨
*Mallakar*
AUTAR MAMA*FREE BOOK*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
*Comment*
*Vote* &
*Share* Fisabilillah*My WhatsApp group link, Dan Allah mata kawai*
https://chat.whatsapp.com/BrUNywiBsPxDJjxclwHfdU*018*
Satin Saude ɗaya sannan Aunty Sadiya ta dawo tare da Bilkisu har da Maryam.. Saude na kitchen tana breakfast suka shigo.. Murmushi kawai Saude tayi tana cigaba da tsane Irish potatoes dinta. Fitowa tayi falo tana faɗaɗa murmushinta, daga sama har kasa Aunty Sadiya ke kallonta, tasha doguwar riga ta kashe dauri, ga farar fatar nan data sha gyara sai daukar ido take, "Saude! Uban me kuma ya kawoki nan? Cewar Maryam tana kallonta. Kallon² Bilkisu da uwarta suka fara yi.. Saude bata ce komai ba ta maida dubanta kan Aunty Sadiya ta ce " Ina kwana Aunty? "Lafiya! Aunty Sadiya ta amsa ba yabo babu fallasa. " Kutumar ubancan! Saude! Kece amaryar Abba? Maryam ta kuma faɗa tana tashi tsaye. "Eh sai akayi yaya? "Ahayyyyyyeeee! Tabdijan! Aunty Sadiya! Kinsan wacece kuwa? Toh wallahi k'anwar Zara'u ce! "Wace Zara'un? Cewar Bilkisu da karfi.. "Zara'u dai zara'u mayyar yarinyar nan data lashe miki miji! "Wallahi Yayata ba Mayya bace! Akwai mayen daya wuce Ammar? Tayi aure ma bazai kyaleta ba! Jarababbe! Ya bar matarsa tana yawo kwararo² kamar bata da mafadi! Cewar Saude tana zazzare idanuwa bala'i na cinta. " Sai dai idan uwarki ce take yawo kwaro² wallahi badai ni ba! Cewar Bilkisu.. dariya Saude tayi harda tafa hannayenta kafin ta ce, "Ni an koya min tarbiyya, kuma da yake naje islamiyya an koyar dani duk wanda ya zagi uban wani toh idan mutun bai rama ba nashi ya zaga! Daga haka ta koma kitchen. Tana ta jiyo surutansu, sai data kammala breakfast din sannan ta fito tana fad'in "Aunty ga abinci" "ke da yunwa ta kawo ai sai kiyi ta ci gashi nan indai abinci ne sai kin gaji dashi! Bilkisu ta faɗa tana harararta kamar idanunta zasu fado.. "Kinga dakata! Ina magana da wadda ta isa ba dake ba! Nan kuma gidan miji nane ki tafi naki gidan mijinki kiyi gadara da takama! Daga haka ta zauna kan kujera tana cin abincinta.. "Abba! Abba! Bilkisu ta fara kiran sunan daddynta.. " Da zaki hutar da kanki saboda babyna ya dade da fita" Cewar Saude tana sakin wani shegan murmushi.. tsabar bakin ciki da takaici Aunty Sadiya tashi tayi ta wuce daki.. Bilkisu na huci ta kalli Saude ta ce " zaki san kin tako wuta wallahi" "Kyaji dashi dai, matar Shige! Saude ta fada tana kwashewa da dariya. Bilkisu bata ce komai ba ta bi bayan uwarta. "Ke kuma zaman me kike? Cewar Saude tana yi wa Maryam wani shegan kallo. Tsaki Maryam tayi tana tashi ta bi bayansu.. "dai dai nake daku wallahi! Saude ta kuma faɗa tana cigaba da cin abincinta. Da yammacin ranar Saude ta dau wanka ta fito daga daki ta zauna a falo dan tasan girki y bar hannunta, shiyasa bata shiga kitchen ba. Bilkisu ce ta fito daga dakin uwarta tana wani baza hanci.. "Wannan kujerar da nake zama ce Malama zaki iya tashi ki ban waje? Banza Saude tayi mata tana kallon TV hankali kwance. " Bakiji bane? Bilkisu ta kuma maimaitawa. Sai a lokacin Saude ta kalleta kafin ta kwashe da dariya ta juya ta cigaba da kallo abinta. "Eh lallai samun waje, ai babu a hawus dole ayi dane² kan kujera! Banza Saude tayi mata tana cigaba da kallon series Film din da ake a starlife. Tsaki Bilkisu tayi tana daukar remote ta fara searching din channel.. "Ke dallah bana son shiririta, ya za'ayi ina kallo ki wani canza min tasha? "Sai ki bari idan ubanki ya siyo miki TV kyayi kallon dashi ba dai wannan ba! Tashi Saude tayi ta wafce remote din a hannun Bilki tana fad'in "Tafi gidan Mijinki kiyi takama! Aikin banza! Daga haka ta zauna ta mayar da starlife dinta ta cigaba da kallo. Kashe TVn Bilkisu tayi tana kallonta ta ce " Sai inga ta yadda xakiyi kallon ai, dangin tsiya kawai! "Dan Allah Bilkisu a koma gidan miji! Saude ta fada tana dariyar wulakanci.. Cikin hayagaga Bilkisu ta ce " Idan ubanki yake aurena dai kisaka ya mayar dani! "Shiiiiiii! Ya kike haushi kamar wata sabuwar karya? Nifa shawara na baki, Kodai sakinki yayi tun kafin ku rufe shekara? Ashaaaa ashaaaaaa... Hannu Bilkisu ta daga zata mareta,Saude ta rike hannun batayi wata² ba ta ɗauke Bilkisu da mari me zafin gaske dan dama haushinta take ji tun ba yanzu ba. Ihu Bilkisu ta kwada me ƙarfi, da sauri Aunty Sadiya ta fito daga daki tana kallonsu. "Ke me haka? Cewar Aunty Sadiya tana kallon Saude. "Hankali na koya mata! Next time zata gane cewa Ni ba sa'ar yinta bace! "Umma mari na fa tayi! "Mari? Aunty Sadiya ta maimaita cike da mamaki. " Eh marinta nayi! Ko yanzu ta kara kokarin sake marina sai na mareta! Yadda take takama mahaifiyarta na zaman aure nima zaman aure nake yi ba dadiro ba! Daga haka ta wuce ta barsu a wajen. Aunty Sadiya batayi tunanin gogaggiyar yar duniya Alhaji zai auro ba ashe duk zatonta abun ya wuce haka, lallai sai ta sake ɗamara. "Wuce muje! Shikenan ta mari banza? Cewar Bilkisu tana hawaye.. kafin Aunty Sadiya tayi magana Alhaji ya shigo.. Bilkisu na ganinsa ta kara sautin kukanta.. "To.. toh lafiya dai? Ya fada yana karasowa. "Abba dama haka amaryarka take? Daga magana wai ta dalla min mari" "Saudah? Ya fada cike da mamaki dan yasan ba ƴar sa ba ko me gadin gidansa baya tunanin Saude zata iya mara, domin tana daraja duk abinda ya fito daga ɓangarensa. "Fada min gaskiya! Ya fada yana riƙo hannunta. "Gaskiyar me kuma kake son sani Alhaji? Cewar Aunty Sadiya tana kallonsa. Hannu ya daga mata alamar ya isa.. cikin rarrashi ya ce, "Fada min me ya hadaku? "Abba ita ce kawai dan na dau remote zan canza tasha wai in tafi gidan mijina mana in canza tasha, na bata hakuri shine ta min tsaki shine... "Ya isa, yi hakuri, kira min ita" da toh ta amsa tana tashi ta nufi dakin data ga Saude ta shiga dazun. "Kizo! Daga haka ta fice. Taɓa baki Saude tayi tana tashi ta biyo bayanta. Kusa da kafafunsa ta tsugunna tana fad'in "Sannu da zuwa Abban Bilki" Barin wajen Aunty Sadiya tayi dan bakin ciki da takaici ne ya isheta. "Yawwa, me ya hadaku da Bilkisu har ta kai ga mari? "Laifi ta min" Saude ta faɗa tana tsuje fuska. "Wani irin laifi kuma? Ya kuma faɗa.. ɗagowa Saude tayi tana kallon sa ta ce, "Marina zatayi shine ban bari ta aikata hakan ba ni na aikata mata, Abban Bilki ni bana son tashin hankali shiyasa ban so shiga harkar ta ba, bazai yu ace kullum ya zama ana cikin rabani faɗa da ita ba kamar sa'ata, tunda har tayi tsaurin idon gwada marina gaba kuma duka zata ce zata min wanda gaskiya bazan dauka ba" "Karya take yi wallahi ni banyi ko .. "Ya isa! Abba ya tsayar da ita. "Tashi ki wuce daki! Ya fada yana kallon Saude. Tashi tayi ta wuce dakin abinta ranta fes.. Dadaddare Bayan sallar Isha'i suna zaune a falo har Saude dan Abba ne ya tara su zai musu magana, nasiha yayi sosai ya kuma ja kunnen Bilkisu sannan itama sauden yaja kunnenta akan girmama Aunty Sadiya kowa yayi na'am a lebansa amma kam ta ciki na ciki. Sallamar da Ammar yayi ce ya saka Bilkisu saurin juyawa, dama Ummanta tace zaizo amma batayi tunanin so soon haka ba. Sunkuyar da kansa yayi ya ƙaraso cikin falon, Abba ya fara gaidarwa sannan Aunty Sadiya data amsa kamar bata so. "Saudah ga Ammaru mijin Bilkisu, Ammar ga Amarya" cewar Abba yana kallon Saude. Murmushi Saude tayi tana kallonsa.. "Barka da dare amaryar Abba" Ammar ya fada yana kallon Saude. "Yawwa, ya aiki? "Alhamdulillah" Ammar ya amsa. Ita dai Aunty Sadiya kallonsu kawai takeyi tana girgiza kafa. "Jeki dauko hijabi ku tafi! Aunty Sadiya ta fada tana kallon Bilkisu. Daki ta wuce bata daɗe ba ta dawo sanye da hijabi, sallama sukayi sannan suka fita. Sai da Ammar ya bari suka isa gida sannan ya saka ta zauna ya fara faɗin, "Billah Bilkisu duk ranar da kika kara haɗani da mahaifiyata ranki sai ya ɓaci, wallahi Allah zaki fuskanci hukunci me zafi Allah! Wani irin iskanci ne wannan da kullum zaki dinga saka mahaifiyata cikin bacin rai kuma nima nawa ran na ɓaci? Kinfi kowa sanin matsayin aurenmu! Kinfi kowa sanin bake nake so ba tilasta min akayi na aureki! Ki sake ki gani! Daga haka ya tafi daki ya barta. Kuka ta fashe dashi zuciyarta na zafi sosai, ita gaba daya auren Ammar ya fara fice mata a kai, data sani bata biye ta Ummanta ba, ita ba manema ta rasa ba, sai dataci kuka me isarta sannan ta tashi ta nufi dakinta.