Ramin karya 40

158 3 0
                                        

RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha
🆓book
WhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 40

Bayan wata uku da rasuwar alhaji sambo kuma fa sai wata mastala ta bulowa huda dan yanzu gaba daya kudin data samu gurin alhajin ya kare gashi jummai sai Kira take Akan tana bukatar kudi dan watarana ma idan ta share wayar jummai bata Hakura saita dinga Kira har sai hudar ta dauka kuma magana daya ce dai kudi take da bukata dan haka huda ta shiga Damuwa ga karatu ya dau Zafi ta Abincinta ma duk ya kare kwaki take ta hada da kwana biyu tana sha ko biscuit zee kuwa Ido ta saka mata tana ganin gudin ruwanta dan tasan dole idan huda taji uwar bari ta kuma dawowa hanya

Rahama ce ta lura da halin da hudar take ciki dan haka take mata tayi idan tayi girki saidai nauyin rahama yake hanata ci duk da tanason cin abimcin rahama yarinya ce niststsiya shiyasa take son halin hudar dan ta fuskanci kamar zee da sadiya babu abunda suka saka gaba sai yawo karatun ma bai Dame su ba dan sadiya sau biyu tana step down duk waenda suka shigo makarantar tare sun dade da gamawa aman ita tana nan tana shiririta

Yau huda bata samu zuwa lecture ba dan malamin yayi warning Akan duk wanda bashida handout karda ma ya shigo masa aji dan haka ta hakura da zuwa tayi kwanciyarta gashi jummai takirata yafi sau 10 Akan tajita shiru tun wacan satin ba aike dan huda wayarta da alhaji ya siya mata tayi gwanjonsa ta siyar da tura ma jummai kudin sanan ta siyi karama , shine ta daina kira toh gashi kuma yanzu ko sati ba a rufa ba ta kuma kira wai tana bukatar kudi dan haka huda ta rasa abunda yake mata dadi

Zee ce ta shigo dakin tana taunar chewing gum abunta tana waka ganin huda tayi tagumi ya ska ta tafa hanayanta tayi dariyar bakiga komai ba sanan tace ke wai huda kuma bani mama ki wlh

Ace da kyaun ki anan ki zauna rayuwa na gara ki mai makon ke ki gara sa yanzu why kike zaune bayan ana lectures , huda kallonta tayi sanan tace hmm zee kenan nafada miki irin wacan rayuwar ta daina Bani sha awa wlh Kema Kamata yayi ki nustu wlh

Dakata malama ya isa karki bata mun rai ni zee bani da ranar daina bin maza dan haka idan bazaki iya joining ba ki daina mun wani wa azi nagaji zan kwanta ta fada tana kwanciya a gadonta tana dana latest wayarta da wani inyamuri ya bata bayan ta kwana a hotel dashi jiya

Huda kallon wayar tayi tace zee iPhone 14 fa nake gani , zee tsaki taja sanan tace ke tunda kin tsaya playing good girl saiki karata wanan somin tabi kenan yarinya ta fada tana mata gwalo

Huda girgiza kai tayi sanan ta tashi dan tayi wanki da safe zataje ta dauko kayan daga shanya dan haka tafiya tayi kamar wace kwai ya fashewa a ciki

Sadiya ce ta shigo dakin bayan huda ta fita ganin zee a kwance tana danna sabuwar iPhone 14 ya saka sadiya yin birki sanan ta ce wow iPhone 14 zee na dade dan sanin ke babar yarinya ce wlh kalli iPhone 14 fa omo

Zee mamaki ne ya cikata yau shine rana ta farko data ga fara ar sadiya haka hasalima ko muemushi bata Musu kallon arziki ma bai Taba shiga tsakanin su ba zata iya yin wata daya bata ko kula wani cikin su ba gwanda ma rahama Aman huda da zee basu isa ta kula su ba

Sadiya babbar yarinya ce mai mutane kala kala masu halaye iri iri maza da mata wanna yasa ta zama kamar kawaliya mai hada mata da maxa haka ta hada maza da mata shine aikinta wanan kenan

Zee kuwa murnushi tayi cikin farin ciki yau sadiya ta kulata tace eh shine , wow na dade da sanin ke babar yarinya ce kawai bana baki face ne saboda kawar ki I don't like her wlh tanayi kamar tafi kowa tsoran Allah bayan ha haka bane ba kinga irin su sunfi kowa tsula tsiya aman su dinga nunawa mutane su na Allah ne

Zee ce tace hmm kin Taba mun Inda yake mun kaikaiyi wlh sadiya banasın huda haka take da wanan fake personality din tun Muna school aman barta wlh saina sake mayarda da ita ruwa

Sadiya ce tace oo daman kawar kicw tun da nadauka a school fa kuka hadu , zee tace aa nan ta bata labarin huda komai data sanı har tsanar da tayi mata da ingizata kula alhaji sambo datayi

Sadiya dariya tayi sanan tace kice itama mini karuwa ce ta taba karuwancin nan aman take haka kamar wata ta Allah

Zee ce ta tabe baki sanan tace tab ae yadda na fada miki wlh haka komai ya faru dan haka daidai muke da ita Tama daina baki wani tsoro

Yanzu hannu da hannu zamu hada dan mu samu mu sake tsunduma ta cikin wanna rayuwar dan kuwa wlh banson yarinyar nan tafiye Girman Kai imagine behaving like bata Taba wani abu da namiji ba aikin banza sadiya ta fada tana yastine baki

Ae hakan za a yi alhamdulilah bani kadai bace yanzu nake so na hukunta huda dan haka ina bayan ki dari bisa dari har sai mun çıka burin mu nan suka tafa suna shewa

Rahama ce tayi gyaran murya sanan ta shigo ta kallesu kallon tsana da mamaki sanan tace wlh sadiya da zainab kuji tsoran Allah daman ke ta nuna zee na dade ina zargin kina bakin ciki da huda sai gashi yau na tabbatar da hakan kekuma sadiya wlh kiji tsoran Allah babu abunda bAiwar Allahn nan tayi miki aman kin dauki tsana kin dora mata wlh ki daina hakan wanna ba rayuwa bace ba

Toh munafuka labe kika koma Kenan toh bara kiji abunda mukayi niya ke kinyi kadan ki şaka mu fasa Ehe sadiya ta fada tana hararar rahama

Huda ce tayi salama ta shigo nan rahama tayi saurin kwanciya ta rufe İdonta kamar mai jin bacci dan kuwa kanta ya kule da al amarin sadiya da zee

Huda kayanta ta shiga linkewa daga nan ba wanda ya sake magana kowa ya shiga hargar gabansa

Kwana 2 da faruwar hakan suna zaune gaba daya aman ba rahama zee da sadiya ne ke hira jifa jifa dan kuwa yanzu sun zama kawaye watarana ma har party suke fita tare

Wayar huda ce ta yi kara ganin bakuwar number ya saka ta dauka saidai tsinuwar da taji ana mata ne ya bata amsar sanin wanda yake kiranta....

Mrs abba

Ramin karya (Hausa novel )completedStories to obsess over. Discover now