Ramin karya 24

18 0 0
                                    

📕RAMIN KARYA
✍️Written by Khadija mustapha

WhatsApp 08022242200
Watpad khadijatmustapha25
Page 2️⃣4️⃣

Da hüda ta bar shagon wani lungu ta samu ta kirga kudin mamaki ne yakamata dan bata taba rike irin wanan kudin ba a zuwan nata , kirga kudin jummai tayi sanan ta cusa sauran kudin a rigarta tayi hanyar rumfar jummai

Tana zuwa ta tarar da jummai na rumfar tana zaune tana ganin hüda ta fara washe baki ke har kin dawo bani kudina nasan alhaji garzali bazai barkı haka ba

Lankwasar da Kai hüda tayi sanan tace jummai ga shi aman dan Allah ki daina aika na gürin mutane irin su alhaji garzali wlh tsoro nake ji

Yimun shiru banza kawai jummai ta daka ma hüda tsawa, idan ban aike ki wajen irin su alhaji garzali ba ki Samo mana kayan duniya Ina kike so na aike ki

Hüda ce ta zumburo baki sanan tayi gaba dan tsayawa Yima jummai bayani bata lokaci ne dan jummai bazata taba yarda da ita ba

Zee kuwa da Pretty gidan su zee suka je, a tsakar gida ta tarar da yayanta uku suna zaune kowace tana Dana waya dan aikin su kenan kullum chat da samarin banza su tura musu hotuna sukuma su tura Musu kudi dan ciyar da kansu da yin bukansu na yau da kullum

Sun dade da gama secondary aman mahaifin su yaki bari su cigaba kawai Sabida kar ya biya musu kudin jami a dan gani yake yana fara biya Musu zasu talauta shi

Yusra ce ta kali zee tace yan makaranta andawo kenan , daga Kai kawai zee tayi sanan ta janyo hanun Pretty suka shige dakin kwanansu

Tabe baki hauwa tayi sanan tace Allah ya kara uwar shishigi ae ga abunda shishingin yaja miki

Murmushin takaici yusra tayi sanan ta cigaba da Danna wayarta dan kuwa ta shakka abunda zee tayi mata sosai

Drawer din kayan su ta nufa bayan ta ce pretty ta Zauna akan wani gado madaidaici Wanda su kusan 4 suke kwana akai

Kaya ta shiga zaba sanan ta zube su a kan gadon tace ma pretty gasu tayani zabe dan Allah kinga kinfini sanin Kaya

Pretty ce ta shiga daga kayan tana dubawa tana gama ta saki dan siririn tsaki sanan ta girgiza kanta tana kallon zee tace

Ke yanzu zee waenan sune kayan da zaki saka muje party dinan tab wlh da kin kwafsa wanan ae bola ce they are trash wlh ta fada tana yamusta fuska

Jikin zee ne yayi Sanyi sanan tace Preety kin sani banida wasu Kaya wlh yanzu ma ina ganin muna cikin shekara na 4 da baba yadaina mana kaya waenan ma da kika gani mama nace ta mun shine nake dan kwaliya na dashi

Gidan nan da kika gani kowace saidai kima kanki kaya da wasu abunuwan ke hatta sabulun wanka da wanki saidai ki siya da kudin ki kinga yan Matan da kika gani a tsakar gida duk sisters Dina ne kuma kowa da uwarta kuma duk basa gidan nan dan haka rayuwar hakuri Muke yi a cikin gidan nan babu abunda yake mun dadi gwanda ma su da samarin su dukda ba wasu mutanen arziki bane ba aman dai suna musu hidima kuma baba bashida mastala da haka nikuma dai kina gani kamar jaba banida mai tayani ballantana na samu a dinga mun wani abun zee ta fada tana share hawayen da ya gangaro mata a fuska

Preety ce ta girgiza Kai sanan tace ya isa zee aman kisani daga yau Komai yazo karshe kinga wanan wahalar saidai kiga anayi I promise you zaki samu samari masu Kyau da kudi ke dai kawai kiyi biyaya ki nuna musu keba yar kauye bace ba toh fa zaki ga hidima I promise you

Gyada Kanta zee tayi sanan tayi murmushi tace nagode kawata yanzu wane kaya kike ganin zan saka

Preety ce ta gyada Kai sanan tace karki damu a nan gaskiya babu kayan da zaki saka kije irin wanan gurin sai a raina ki aman yanzu kizo muje wani boutique sai na zabo miki kaya ko kala 2 ne before ki samu naki kudin kema ki siya

Rungume ta zee tayi cike da farin ciki sanan ta sake ta tana dariya tana zuba mata godiya

Ba komai Preety tace sanan suka fito daga dakin suka nufi hanyar waje bayan sunyi wa su yusra salama

Kai tsaye wani shagon siyarda kananan kaya suka nufa nan ma zee ne da pretty suka sauka suka shiga shagon driver yana jiran su a mota

Suna shiga pretty ta nufa inda gowns suke irin na yan kanti dinan ta shiga dubawa nan ta samu wani gown mai siririn Hannu kamar shimi daga kasa kuma ya tsage tundaga kan cinya har kasa

Nuna wa zee tayi tana murmushi tace wlh zee kika saka wanan saikin ruda maza, zaro idanuwanta zee tayi tana kallon kayan tundaga sama har kasa sanan ta dafe kirji tace yanzu wanan Kayan zan saka haba mana pretty saikace wata inyamura

Bata rai pretty tayi sanan tace au atamfa kike so ki saka muje party ko hijabi

Girgiza Kai zee tayi sanan tace kiyi Hakuri Preety kawo ina so zan saka

Kokefa Preety tace sanan ta mika mata Kayan tana sake duba wasu nan ta dauko wani shikuma mai dogon hannu ne aman iyakar sa cinya gashi a dame daga gaban rigar kuma a bude take da shape din love

Shima mika mata shi tayi sanan ta nuna mata inda zata Chanza kayan bayan sun gama biya

Mai dogon hanun ta zaba dayan ta saka a leda sanan suka fito suka nufi mota itama Preety ta dauko kayanta suka koma shagon ta Chanza

Itakuma wani gown ne shima mai hannun shimi shikuma iyakar sa gwiwowin ta shima bai karasa rufe shi ba haka ta saka abunta suka fito suka nufi gurin party din a wani club

Suna isa club din pretty ta janyo hanun zee suka fito, pretty ko a jikinta shigar dake jikinta aman zee gaba daya jinta take kamar wace take tsirara sai rabe rabe take ga Kai ba dankawali abun duk wani iri take gani kamar ta ruga mota tace ta fasa aman bazata iya ba

Suna isa maza da mata ana Rawa nan aka shiga yima Preety kirari itakuwa takawa ta shiga yi Tana rawa kamar macijiya abunta sai karya jikinta take tana rawa shikuwa jikin nata ya bata hadin Kai dan kuwa sai lankwasa shi take kamar ba kashi a jikinta

Nan fa aka hau shewa da ihu wani saurayi ya fito nan ya bude rafar yan dubu daya ya shiga lika ma pretty nan mutanen wajen suka shiga ihu da masa kirari bad boy bad boy bad boy shikuwa sai lika mata kudin nan yake kamar baisan zafin su ba

A haka saida ya lika mata dubu dari sanan ya janyo ta jikinsa yana dariya ya rada mata a kune Preety save this energy for me anjima for now it's okay let's go have some drink

Murmushi pretty tayi sanan ta kalle shi itama rada tayi masa tace this dance cost you 200k dan I don't care da kudin da ka lika mun so is that a deal ta fada tana daga masa gira

Murmushi peter yayi sanan ya gyada mata Kai alamun ya yarda sanan ya kuma jan hanunta

No nazo da kawata pretty ta fada tana kwace hannunta let me get her sai nazo wait for me

Gyada Kai Peter yayi sanan ta koma gurin zee wace gaba daya jikinta ya dauki rawa kamar mazari tana kallon ikon Allah Ashe haka pretty take wai ita kam yanzu ta fara tsorata da wanan rayuwar rashin kamun

Hanunta pretty ta janyo ba tareda tace komai ba ta samu Peter sanan tace peter this is my friend zee , zee ga big boy peter sunanshi

Gyada Kai zee tayi cike da tsoro sanan ta sakar ma peter murmushi tace sannu ko peter

Murmushi shima peter ya saki sanan ya ce au zee nice to meet you sannunki kema

Gyada Kai kawai zee tayi dan har yanzu jikinta bai daina rawa ba , nan peter ya janyo hannun pretty suka nufi vip din cikin club din Dan nan ne na manyan yara maza da mata .......

Ramin karya (Hausa novel )completedWhere stories live. Discover now