Babi Na Uku

2K 286 96
                                    

Ko da suka isa gida, Goggo ta fara haraman ɗaura abincin rana, yayin da Salmah ke manne da ita

"oh ni Salame, se kace wata kaska ina ɗaga kafa kina saukewa, ki je cikin yan uwanki ki zauna" ta faɗi sa'ilin da ta bita zuwa madafa.

"zan tayaki ne fa Goggo, na iya Girki ina ma innarmu a kano" ta faɗa cikin murmushi yayin da Goggo ta saki baki tana kallon ta galala.

"Ita Aminar ce ke saka ki Girki? " ta tambaya tana mai kallon idon ta don ta ga iya gaskiyar ta.

" a'a muna taya ta ne dai, a haka har muka koya, ranar da na fara yin tuwo ko Goggo, rabin sa gari ne, ranar baba sai da ya make ni wai na faye rawar kai" da fari tana maganar tana dariya ne sai da ta ambaci sunan baba ta gimtse fuska tunawa da tayi da abin da ya baro su.

"Oh ni salame, ko dai Almatsutsai gare ki ne, ana raha sai ki gimtse fuska, ko dai Kanon zaki koma mu huta" Ta ce tana lakuto mata haɓarta. Dariya kawai Salma tayi ta watsake.

A haka suka kammala abincin su na rana, suka ci bayan sauke farali ɗaukan su tayi zuwa makarantar islamiyya da ke bayan Layin su.

Bayan gwajin da aka yi musu nan aka sa Salman a aji huɗu, Salma aji uku suhayl kuma rabin aji. Goggo bata tafi ba har sai da ta amshi takardar shiga sashin hadda tare da alkawarin zasu fara zuwa ranar Alhamis kasancewar sashin na karatu ne ranakun Alhamis zuwa Lahadi.

Sun shiga azuzuwan su ana darasi na biyu. Salma ta iske malamin fiqhu na karantarwa. Nan ta iske kujerar farko a gefen mata da mutane uku ta zauna cikon na ukunsu, ta natsu tana sauraran karatun.

"Assalamu Alaikunna, kaif" ta ce dasu bayan malamin ya fita.

Sai da suka kalli juna sannan suka amsa da "Waalaikumus salam wa Rahmatullah wa barakatuh".

"ismie Salmah Aarif " ta faɗi tana mika musu hannu.

" Rufy kiyi shiru in ansa, kar ta raina mana wayau, don ma jiddo bata zo ba da ita zata yare mana ita" cewan ɗaya daga cikin su,

Dariya ya kucce ma Salmah, ita dama tsoronta irin islamiyyarsu ta Saudiyya ce da ba'a wani yare sai larabci duk da kasancewar suna yankin da mafi akasari bakaken fata ne.

"Wacece Jiddan Halan, don Wallahi kun bani dariya, ni fa na sha ba'a wani yare sai zallar larabci ne fa" ta karasa tana dariya. Nan duk sai suka haɗu suna tuntsira dariya kamar wasu sabbin kamu.

"wai tsaya, Salma wai dama kin iya hausa ne kike yare mu, har da wani Alaikunna " faɗin mai kiran Rufy nan suka kara sakin wani dariya.

" Ai Barta Ummita da fari na aza fa bata iya ba, sai da na ga ta kara karya harshe na ga ai ko da Larabawa take kama" inji Rufy. Suna tsaka da dariya wani malamin ya shigo, suka yi tsit kamar ba su ba har sai da aka kaɗa tashi.

Nan ne Ummita ta haye samar tebur ta ce

"ga bakuwa an kawo muku a aji, mu dai gare mu ba bakuwa bace don yar wata Goggonmu ce, balarabiya ce kuma, ba ma son shisshigi da neman es, ehe"

"kuma Sunanta Salma Baralabiya, saura su wa'e su turo wasika Wallahi abinda muka yi lokacin jiddo kaɗan ne akan wanda za muyi ma Salmah" Rufaida ta amshe, nan suka tafa suna tuntsire da sabuwar dariya.

Mamakinsu ya cika Salma, duk da tana da tsokana tun tasowarta amma zaman gidan inna ya sa duk ta daina saboda rashin sakewa Matukar baba na gida.

A bakin kofar makaranta ta haɗu da Salman da Suhayl nan ta gabatar masa da Kawayenta suka yi gaba yan mazan na biye da su a baya.

A hanya take tambayarsu gidan su sai suka faɗa mata Mahaifin Rufaida yayan Ummita ne, ita kuma jiddo yar kanwar mahaifiyar Rufaida ce. Ummita ta kara da cewa "ke kuma daga yau yar Goggo na ce. Duk da kuwa Goggo salame kawar kishiyar Mamana ce. Kinga ke ma ya ta ce" nan Rufy ta kai mata duka ta ce

"sai aukin son girma amma duk mun girme ki"

Nan fa Ummita ta kumbura tana shirin yin rigima sai da Salman ya shiga tsakani sannan ta yi gaba ta Barsu a baya. Su kuma suna ta mata dariya har suka kai kwanar da ta raba su, duk suka yi hanyar gidajensu.

"Assalamu Alaikum Goggo na" ta faɗi tun daga bakin kofa, Ras! Ta ji gabanta ya faɗi don bata san irin tarbon da zata samu daga Goggo ba.

"Waalaikumus salam yaran albarka, ina suhayl ya karatun zo ka faɗa min mai gidana" ta ce tana gwasale Salma. Bayan sun gaishe ta ne take tambayarsu karatun su, sannan suka yi alwala don gabatar da sallan magrib.

Bayan sallan isha'i ne suka taru don cin abinci. Suna tsaka da ci ne aka yo sallama, ashe Kanin Goggo ne da yayanta hakimi. Nan aka sake sabon gaisuwa, su Salma na shirin tashi suka zaunar da su

"abin da ya sa muka yo takakkiya ba komai bane sai zancen yaran nan, mun tattauna da Yaya ga shi nan ni ban goyi bayan a cigaba da rike su ba, yara dai yaran zina ne, ba zamu gurɓata alayenmu ba, shine muka yanke mika su gidan marayu, in har tana son Yaranta da gaske ta dawo gida tayi aure" Kanin ta ya faɗi yana jijjige-jijjige kamar zai mari Goggo.
Kukan da Salma ta saki ya kara karya zuciyar Goggo duk da zancen Kanin nata ya ɗan sa mata tsanar su.

"Amma Jamilu ka bani kunya, har zaka kalli kwayar ido na ka danganta jikoki da zina, Naji yan zinar ne me kai su gidan marayu zai haifar? Ni dai zan rike su tsakani na da Allah, yaran nan guda nawa ne da za'a fara jifan su da muggan kalamai. Toh gaskiya da sake"

"Mun baki nan da kwana uku ko ki mika su ga gidan marayu ko kuma in sa a tayar da ke a garin nan" faɗin Hakimi rai a ɓace, ba tare da ya jira amsarta ba ya Mike ya fice daga gidan, nan Kaninsa ya bi bayan sa shima

Hey darlings...

Hop u r all doing great, it's a short chappy but am coming back later 2day Insha Allah.

How do you c Silar Ajali.?

We v just started, shower some love by voting and commenting pls

SILAR AJALI Where stories live. Discover now