Babi Na Goma Sha Tara

1.5K 165 41
                                    

MARKE 2012..

"Ni ko Salma wannan wace irin rayuwa ce,  kin ga yanda kika koma kuwa" faɗin Shukra ta gidan Alhaji Aminu da tun zuwan su sallah Karama suka haɗu da salma a masallaci suka zama kewaye.  Duk da kasancewar ta yar birni yar gayu hakan bai hana ta kaunar Salmah ba tsakanin ta da Allah.

" Kinsan kaka, wacce ta haifi uwa ? To itace mu taja mana masifa, Lakin duka laifin iyayenmu ne, da suka haifemu suka kasa rike mu A saudiyya, wai acewarsu saudiyya babu karatu, kuma ana 6ata kananun yara, To ita kakarmu babanmune bata so,  saboda asalin sa ɗan Sudan ne alhali su ne fa Silar haɗuwar Umminmu da shi.  Ba 
rashin ci ba sha, amman babu nutsuwar hankalin cin, Ita kawai mu tashi mu tafi makaranta, bata kula da dukkan damuwar ba, Sannan ta ɗaura mu kan tsoro, kullum muna daki ni da Suhayl,  yaya Salman ne kawai ke fita zuwa aiki, wlh ko makota bama shiga,  haka banta6a zuwa fati ko suna ko biki ba, koda na dangi ne hana karya tun bikin su rufaida da naje shi ke nan" Tayi shiru tana kuka wanda yafi jini ciwo.  Shukran ma dai hawaye take yi. A zuciyar ta mamakin kaka irin goggo take yi.  Rashin uwa bala'i ne

"Kawai ɗazu  muna daki ni da Suhayl, kinga tunda ta koya mana  haka ai akan tsoro zamu tashi ko?  Toh sai take ce mana munafukai Wai komai da munafunci mu ke yi,  Kee ko irin abin nan na mata na wata wata, gogg batasan ina  yi ba, wallahi dai dai da pad yayanmu ke kawo min,  in ya samu yan canjinsa in ba Haka ba ɗan kwali na nake amfani da shi." chan Salmah ta ɗaura cikin gunjin kuka

"Haba!  Wannan wace iri  rayuwa ce,  wai me ya ja wo miki wannan azabar ne?  Yaushe ta fara hakan don gaskiya ya kama ta a kwato muku hakkinku,  shi yayan ba zai iya kwatar muku hakkinku bane?" faɗin Shukra a kausashe ranta a ɓace.

"ku da yan birni daban ne,  ai dole mu zauna tunda ba mu da wajen zuwa. Duk manta wannan, shekara ɗaya da rabi kenan  wanta ya kira su ita da kawu Jamilu ya masu wa'azi a kanmu.  Tun lokacin ba mu sake samun wani matsala da ita ba, duk da dai ba dariya ba fita din amma ba zagi amma kuma ba kyara. 

Daga makarantar islamiyya sai na boko kawai ke fitar da ni,  yan kawaye na duk sun yi aure sai ni kaɗai, bayan nan sai mahaifiyar mu ta zo,  wannan zuwan nata ya tabbatar min da goggo munafukar mata ce,  kin san yanda ta ke Mana kamar zata mai da mu cikin ciki. 

Satin mahaifiyarmu tayi sati ɗaya  da zuwa ne ashe Malam Abdoul mai mana english shi ne ya zama Silar Ajalin kakanmu mai kaunar umminmu ba kamar goggo ba,

Abinda ya faru kuwa shi ne zuwa yayi neman gafaran umminmu Ta rufe idanunta ta ci mutuncinsa,  goggo ma haka dalilin da ya sa bai Tsaya min ba kenan,  da har yanzu yana makarantar mu ai da baza'a taba min haka ba" Ta karasa tana sauke ajiyar zuciya

"Toh wai me yayi ne,  kashe kaka yayi ko ya aka yi ya zama Silar Ajalin sa" Shukra ta tambaya tana zare kunnuwa, burinta ta ji abin da ake jita jita a kai shin gaskiya ne ko zancen da Salmah ta fara faɗa mata yanzu.

"Se kin zo gobe zan faɗa  miki amma da wuri zaki zo,  kuma zaki  bani wayar ki na kira ummi na" Ta ce tana dariya.

"zan baki habibti"

"Allah sarki  kin tuna min da Ummitr,  tana  chan cikin Larabawa da Haris ɗinta,  na san zai dafa mata ta cigaba da karatu ta haɗe kamar ki" Ta ce tana murmushi wanda ke kara bayyana yanke war kauna a tattare da ita.

Chan sai ta cigaba

"ina ss1 bayan tafiyar ummi na, goggo ta fitar da wani  salo na hana min sabulun wanka da wanki,  dalilin ta naje shagon makocinmu na karbi wayarsa na kira umminmu na faɗi mata abin da ke faruwa Shike nan laifin dana san na mata  ta tsaneni haka, ta rinka jamin bala'i kala kala, bara kiji kaɗan cikin  kalaman ta kaina,

"Salmah Allah ya haɗa ki da masifar data fi karfinki a duniya,

Salma Allah yasa a kaiki kabarinki na balbalin wuta,

Allah yasa ki dauko abinda iyayenku zasu dawo, koda basu shirya ba (ciki)"

Burinta in  zama yar iska, sai Allah ya kare ni, Wlh Shukra a aike ka  kudi su faɗi, toh batasan kaddarar haka ba, inji wani dan karamin yaro Abban gidan bayan gidan na , wlh haka yace min Shukra  goggo batasan kaddara ba.

Lefi kalilan zan mata  in tun karfi takwas  na safe ne, wlh haka zata koro ni kofar gida
Tace inkika shigo sai ta kasheki

To me take nufi Shukra  na tafi karuwanci ko ?
To haka zamuyi ta bin bango,  Suhayl ya shigewarsa makwabta, Ba ci, ba sha, sai dare in yaya ya dawo, sai ya wuce damu cikin gida, haka zamu lallaɓa mu shige dakin mu, Shi kuma ya fita ya nemo mana awara ko shayi da bread mu ci,  daddare fa, Idan aka bashi kudin aiki, sai yaki kashewa, sai ya kawomana ya bamu duk dan muyi farin ciki. To kinji kadan ko, ki taya ni da addu'a.  In kin zo gobe zan baki labari.  Yanzu ki zo ki tafi kar goggo ta zo ta iske ki a gidan nan,  ki ja min bala'i." Ta karasa tana dariya zuciyar ta na kuna.

Tashi Shukra tayi tana Share kwalla,  kuɗin hannunta ta mika mata tace "ki ɓoye wannan in Yaya ya dawo ki ba shi, sannan ya baki takardar sa na gama sakandire in zamu tafi kano Abban mu ya sa mu masa ko difiloma ne ya sama masa gurbin yi. 

Murna wajen Salmah ba kamar ta hadiye Shukra,  godiya take mata kamar ta mata kyautan duniya gaba ɗaya

                          ***
Washe Gari karfe goma na safe yai ma Shukra a gidan Goggo,  a zaure ta ci karo da Salmah tana Share hawaye goggo ta koro ta

"ki zo mu je hanyar Day ɗinku,  na ga akwai wajen zama, Share hawayenki,  ss2 fa kike Salmah mu Kinga kwalliyar da mu ke yi,  saboda yanzu ai mun yi jan wuya.  Saura shekara ɗaya fa mu gama mu shiga jami'a " Ta ce tana kokarin sa ma Salmah farin ciki aiko sai da ta murmusa.

Yafito Suhayl tayi ya biyo su,  nan suka zauna suka ci dankalin turawa da kwai.  Basu taɓa ci da wayonsu ba, amma ba su so ya kare ba.

" Wai hanta ne wannan?  Me ye aka haɗa da shi? " Ta faɗi tana kai loman karshe a bakin ta

" kuna jin Daɗi a Birni abin ku,  da muna Saudiyya mu ma Haka zai kasance kenan ko" Ta faɗi idanunta raurau zata yi kuk

"Haba ya ta meye na kuka,  ki zama mai gode Allah a duk Yanayin da kika samu kanki,  kina son kashe kanki ne Salmah?"

Daskarewa tayi a wajen don sam bata taɓa  tunanin sake haɗuwa da shi ba.

"Baba Malam" Ta faɗi yayin da ta ga Suhayl ya rungume shi ta tabbatar shi ne yayansu ya kawo musu lokacin da suka fi kowa bukatar sa.

"Me kuke yi a nan?  Kun ci ko ku tuna da yaya yana chan yana neman muku kuɗi" Ya faɗi yana dariya,  nan ta rufe fuska duk da ta san shi sarai da tsokana.

"Wai labarin Umminmu zan ba kawata"

Shiru duk su ka yi tun ba shi Abdulhadi ba da ya ga kamar tonon asirinsa ne amma kuma ba komi ai tun da yaran ba su taɓa juya masa baya ba.

"Ni zan baku labarin tun da na san sanda akayi abubuwa da dama a ciki kuwa har da haihuwar RAHANATU " ai ko sai suka sa dariya.  Tabarma suka Shimfiɗa a Kasar bishiya suka zazzauna sannan ya fara da cewa

Labarin Salmah da goggo is a true life story.  It happened to a sister ban kara komi akai ba,  even though rayuwar ta Tayi haske yanzu tana zaune da mijinta da Yaranta cikin kwanciyar hankali.  Muna rokon Allah ya sa duk kuncin da ta fuskanta ya zama mata kaffara ranar gobe kiyama.  Wani kuncin ma sai a babi na ashirin da ɗaya...

Pray for my angel Dr Hanifa (CEO hanifa creations and couture) she clocked  7 yesterday. Allah ya raya mana ke ya Haskaka rayuwar ki ya nuna mana aurenki ga best of husbands Aameen

SILAR AJALI Where stories live. Discover now