Babi Na Biyar

1.8K 229 45
                                    

A very big thank you 2 ol for the love you shower me with.

Guess what Silar Ajali has hit #625 in general fiction within 6days. It's just 4 post of hundreds coming (lolz) Insha Allah I will keep updating fast fast make una keep voting and commenting till we hit #1.

Jazakumullahu khairan...

Bayan sun karya da waina ta tasa su zuwa makarantar gwamnati da ke cikin marke. Bayan sun cike takardu ta biya kuɗi sannan ta juya da suhayl inda shi ma ta sa shi a firamarin garin.

Bayan shigar aji ne ta iske kawayenta su Rufaida da Ummita a ajin da Jiddo da bata gani jiya ba karamar murna tayi ba ganinsu su ɗin ma haka. Basu kai ga fara surutu ba malamin turanci ya shigo,

" Good morning class " ya faɗi bayan ya rubuta sunan darasi da kwanan wata.
" who born you sir" Kawai ya fito bakin jiddo tana murmushi.

"fita ki zube a gaban aji, Ace mutum bai da tarbiyya, haka kike ma ubanki a gida" Ya ce yana ciccijewa

Nan sai ummita ta fara dariya, salma ta tare mata suka kai ta kyalkyatawa. Ran malamin yai mummunar ɓaci duk ya rasa mai zai musu ya huce haushi. Bulala ya ɗaga zai fara dukansu nan take salma ta fara kuka tana faɗin

"Ni sabuwar, don Allah malam kayi hakuri"

Ajiye bulalar yayi ya tsaya yana kare mata kallo, dariya ta bashi yanda take kyarma a gefenta kuma jiddo ce sharɓe sharɓe da hawaye,

"ku biyo ni" Ya ce musu a tsawace, nan suka fita har da tuntuɓe sauran yan ajin na musu dariya.

***
Isarsu ɗakin malamai ya sa su tuka mashin. Har sun fara ya tuna salma ta ce da shi ita sabuwar zuwa ce ya sa ya tara su gabanshi sannan yace,

"me kike son zama a rayuwa?" Ya mika akalar tambayar zuwa ga rufaida, saboda tun bayan dariyar da su kayi ta koma wata salaha, a tunanin sa salahar ce.

"Inna ta tace in zamo mace mara gardama ga miji, ko mai namiji yayi daidai ne"

"ke fa " Ya ce yana kallon Ummita

" ina son zama malamar asibiti in dinga taimakon marasa lafiya mata, amma aure za'a min daga mun zana jsce" Ta faɗi a marairaice.

"ke fa? Mara kunya baki kamar reza" Ya faɗa yana hararar jiddo.

"Ni, biki na watan maulidi ne, da yardan Allah saura wata bakwai kenan, innarmu tace a sabuwar shekara zan cika goma sha huɗu "

" wa ya tambaye ki dogon zance? " Ya ce yana tsala mata dorina a jiki.

" Ke kuma fa sabuwar zuwa"

"Ni ban sani ba, buri na ɗaya in koma wajen innata a Saudiyya, jiya naji ana cewa za'a kai mu gidan marayu" ko me ta tuna kuma sai tayi shiru,  nan kuma duk sukayi shiru chan dai malamin yayi kokarin magana.

Kuyi maneji da wannan.  In na iya tashi Anjima zanyinayi da yawa se yi clearing again but I will try my best.

SILAR AJALI Where stories live. Discover now