Hey sweeties
double update for you, the 3rd is coming shortly. Insha Allah
Asalin RAHANATU
Asalin Malam Tanko ɗan kauyen Zangon Aya ne a can lardin Kasar zazzau. Kakansa na cikin wa'inda suka kafa kauyen MARKE.
Ya samo suna Tanko kasancewar sa shi kaɗai ne namiji a tsakanin mata. Amma duk cikinsu shi kaɗai yai tsawon rai sai ya'yan yayyin mahaifinsa da sauransu dai. Yana da shekara goma sha takwas Allah yai ma mahaifinsa rasuwa hakan ya sa bai samu yin karatun boko da mahaifinsa ya kwallafa rai a kai ba. Yayar mahaifinsa ya damka shi gadi gidan hakimi lokacin aminin yayan babansa ne hakimi.
Ko bayan rasuwan hakimi da na ɗa sabon hakimi Malam Tanko mai gadi bai bar gidan hakimi ba sai ma gata da yaga sabon hakimi ya masa na bashi gidan zama da kuma ɗaukan wasu Sabbin masu gadin. Hakan ya ba shi daman yin aure in da ya auri salame mai fura.
Malam Tanko fari ne kyakkyawa, don ya dauko hasken fatan mahaifiyarsa wacce ta ke Fulanin garin malumfashi, dogo ne gashin sa a a kwance yake. Duk da kasancewarsa mutumin da mara galihu in ka ganshi ka san Allah yayi halitta a wajen. Hakan ya sa mutane ba su yi mamakin aurensa da salame ba kasancewar duk a sa'o'inta babu mace mai diri kamar ta. Wankan tarwaɗa ce, idanunta fari kamar madara. Mace ce mai kunya da natsuwa amma akwai ta da son a san cewa yayanta ya je makarantar boko da turawa, bi ma'ana tana da son a san ita wata ce.
An yi aure cikin kwanciyar hankali amarya ta tare a gidan nan. Malam Tanko mutum ne mai daraja iyalinsa hakan ya sa duk wani sile da sisi da ya shigo aljihun sa a kan Salame ya ke karewa. Suna cikin haka ciki ya bayyana a jikin Salame, nan fa murna ba kama hanyar yaro a wajen malam Tanko.
Yayin da wasu ke fatan samun haihuwar maza shi malam Tanko tun da ya ji karatun sheikhin malamin nan Abubakar Gumi wata rana da ya je kauyen su da'awa ya ke cewa "Annabi SAW ya ce duk wanda ya dara haihuwar mace alamun Rahma na tattare da shi ne" Ya ke rokon Allah wannan Rahman
Idan abokansa suka ce "Allah ba ka magaji" Ya ka ce "Allah ya min Rahma".
Bayan wata tara kuwa ta haifi yar ta mace mai kama da mahaifinta sai dai idanunta irin na mahaifiyarta ne. Bayan kwana bakwai yarinya ta ci sunan RAHANATU.
Tun haihuwar ta kuwa ya nuna ma yan gari ita ɗin yar gata ce, don rokon Hakimi yayi a haɗa masa ladan sa na wata uku ya siya rago. Hakan kuwa akayi don rago da bunsuru ya yanka mata. Nan fa su liman suka samu abin faɗe wai 'ya mace ko ba'a mata yanka ba ai ba komi amma don kaskanci ya yanka dabba har biyu a haihuwar mace. Hakan bai sa ya kula su ba illa kara kaimi ya yi wajen kula da ita.
Tana da shekara shida Salame ta sake haihuwar mace, wacce ta ci suna Aminatu a shekarar ne kuma gwamnati ta gina makarantar firamare a filin da ke tsakanin marke da kauyen da ke gaba da ita don wadatar ilimi a yakin.
A shekaran ne kuma yaron hakimi da ke zaune waje mahaifiyarsa da hakimi aurota sanda ya ke dawowa daga karatun da yaje. Aka mata sharri cewa wai tana kawo kwarto ɗakin ta ranakun da ba ita ke da girki ba. Ganin ita kadai ke ɗa a gidan ga wani ciki. Lokacin Hadi na da shekara huɗu, tun da ta sa kai sai da aka je aka kwato yaran biyu Hadi da kanwar sa Safiyyah. Kwanan Safiyyah biyu a marke chanjin yanayi ya zama Silar Ajalinta.
Dawowan Hadi ya sa malam Tanko sha'awar boko, duk suka zauna da Hadi shi dai ya bashi labarin boko
"Wai baba Tanko da girman ka zaka shiga bokon ko ya kake so muyi" wata rana Hadi ya faɗi da ya gaji da jin tambayar.
YOU ARE READING
SILAR AJALI
General FictionDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...