Nagode kwarai da addu'ar da kuka min, Allahu ya saka da alkhairi. Ya muka kara ji da hakurin Sheik Alhasan said Jos. Ubangiji Allah ya jikan shi ya sa kabarin sa ya zama raudha min riyaadil Janna. @karylove (maman Mus'ab) pls Accept my condolences.
Tulin tsarabar da suka kaima Goggo ne ya rufe bakin ta fatanta a ce wani saurayin ne ya ma salma wannan kyautar ba ruwanta da ko da ace wani abin ne ya faru.
Haka rayuwa tayi ta tafiya babu daɗi sai godiyar Allah, wulakanci yau daban na gobe daban, burin ta dai a samu Salmah da wani mugun hali ta samu abin yayatawa. Ana haka rannan salma ta wanke kayanta, taje daukan dutse guga da yake goggo ta daukeshi daga dakin Salmah takai nata, nan kuwa tayi fir ta tace "ba zan ba da ba, wa'inda suka haifo ku basu san zaku yi guga bane, Shegiya da ido kamar na mayu"
Bata ce da ita komi ba ta saka hijabbinta na zuwa makaranta a yamutse ta tafi islamiyya, hakan ya kara kona ma Goggo rai don har ta dawo mita take akan zancen.
Washegari ta same ta bayan ta kammala duk wani aiki da ke gaban ta ta ce mata " dan Allah inje gida Batulu mai nika in goge, kin ga goggo hijabbin ya kara yamutsewa da na wanke" Ta karasa tana marairaicewa abinka da dan makaranta ga shi tana ganin ta kai ga balaga dole a fita a tsabtace,Nan take ba musu tace " eh"
Da murnarta ta shiga ta yo guga ba ta tsaya ko mi ba ta kamo hanyar dawowa.
Ta na shigowa zaure tana wakar ta da tafi soSarmadan ya masoyi Sarmadan sarmadan
Sarmadan har abada ni da kai..Bata kai aya ba taji yakushi a fuska, ba ta dawo daga duniyar da taje ba ta hau dukanta da tsinuwa, take kayan ya zube a kasa faɗi take
"tsinanniya, ki zo ki fita ki bar min gida, mara godiyar Allah, mai farin kafa yaushe zaki samu mai kwasa, kar ki fara shigo min gida" Tana faɗi tana watsi da kayan salma, Har takalma tana jefa mata wasu jikinta
Sannan ta cigaba da "Allah ya Tsine miki Albarka idan kika doshi wani daga cikin dangina".Nan fa mutanen gari suka zagaye su suna kallo babu wanda ya yi yunkurin hana goggo abin da take. Take bakin ciki ya cika Salmah, tunani inda zata take don take ta dau alwashin babu ita babu wani dangi na ta. Tsugunawa tayi ta ranka tsince kayanta, anan ne wani mai shago kusa dasu ya miki mata jakar vivah kusan 7 yace "gashi ki sasu ciki" Ta amsa ba gardama bayan ta kammala kwashewa ne ta tarkata ta yi bayan gidan ta zauna, ba tare da ta san me zata yi ba.
Can mairo makwabciyarsu ta leko ta kirata, tace "Salmah tashi ki tafi kano ga kuɗin mota, ki je wajen Abbanku na Kano tun da ranar da ɗan saura"
Girgiza kai tayi ta ce "ban fa taɓa zuwa da kaina ba, kaimu akeyi shima sau ɗaya,"
Tace "to ungo waya kira abban, ba kwanaki naji ya baku lambar sa ba da ya zo,"
Shiru tayi ta tuna zuwan sa da yanda ya buda ma goggo wuta akan musgunawar da take ma Salmah. Abba shine babban ɗan Hajiya Aziza, aiki ya kai shi Kano, yana da son mutunta mutum, ya tsani zalunci. Tun farko jinin su bai haɗu da goggo ba, abin ya tsananta sa'ilin da ya ji labarin korar RAHANATU da akayi.
"Kin yi shiru toh" Ta sake faɗi
" ai banda shi ne" Ta amsa a ciki
"ina da lambar Asmau, matarsa, gashi ki kira ta kiyi mata bayani, in ya so sai ki kama hanya." da rawar jiki ta amsa ta kira inna ta faɗi mata, ba tare da wani tunani ba tace maza ta taho gurinsu.
YOU ARE READING
SILAR AJALI
General FictionDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...