IMRAN...
Tun da ya sauke wayar Salman ya shiga tashin hankali, hawaye ya fara zuba a idanunsa, takaicin kansa da RAHANATU ya cika shi. A sanyaye ya karasa sashinsa inda yake zaune da amaryar sa Aisha,
"Sannu da dawowa" tace da shi tana mai murmushi, ganin yanayinsa ya sa ta shan jinin jikinta. Zama yayi gefenta yana mata murmushi da ya fi kuka ciwo,
"Na faɗi jarabawar da Allah ya min na matsayin uba" Ya faɗi a cije, sai hawaye kuma shar! Tsam ta tashi ta kawo masa ruwa mai sanyi ya sha, ya saki ajiyar zuciya, a hankali ta ke tausa masa kafafunsa lumshe idanu yayi, hawayen ya tsaya amma sai sakin ajiyar zuciya.
Sun fi karfin minti talatin a haka, can ta tashi ta kai masa ruwa yayi wanka, ya fito nan ne ya ji kamar ana sauke masa nauyin da kansa yayi. Zaman da yayi kusa da ita haɗe da cire mata tagumin da tayi ne ya ankarar da ita dawowa shi. Murmushi ta sakar masa ta kauda fuska.
"in karo maka ruwa kasha ko? Ta tambaya idanunta cikin nasa tana mai aika masa sakonni wanda yake ji tun daga kwanya har tafukan kafarsa. Janyo ta yayi jikinsa ya raɗa mata abu a kunne yana shafo cikinta da ya turo riga. Dariya tayi tana ɓoye fuska a kirjinsa. Shi ɗin ma taya ta yayi. Sannan yace
"ɗan ki ne ya kira ni, wai ashe Salmah bata da a lafiya ina matsayin ubanta ban nema mata lafiya ba. Har ya kai ga an mika ta asibitin mahaukata duk da ciwon ta jinnu ne" Ya faɗa muryar sa na nuna tsantsan haushin da yake ji.
"Subhanallah, inna lillahi wa wa inna ilaihi rajiun, mahaifiyarsu fa?"
"shi ya sa Allah ya ce mu nema ma yaranmu uwa ta gari kuma ku nema masu uba na gari, wannan hakkinsu ne da in ka kasa za'a muku hisabi akai ranar gobe kiyama, da ga ni har ita mun gaza anan. Bata zaɓa musu ba nima ban zaɓa musu ba" Ya karasa yana mai kukan da yafi jini ciwo.
"ai ba kuka zaka yi ba, akwai masu magani da dama a nan, yanzu dai ka shirya dawowarta, in ta zo sai a nema mata magani a aurar da ita, ka ga shi kenan yar ka ta dawo kusa da kai. Ko a cikin yan uwa ba za'a rasa ba. Don Kaga akwai masu ilimin zamani ma a cikinsu. " haka ta cigaba da karfafa masa gwiwa tana nuna masa ai gara ya dawo da yar sa kusa da shi don sauran dole su nemi dangin su kasancewar su maza.
A ranar ya cika da alfaharin samunta a matsayin mata, don shi ya san so ɗaya ne kuma rahanatu yake ma wannan so ɗin.
***
Tun da suka tsaida maganar dawowar Salmah Sudan ya shiga bincike akan malamai da zasu mata maganin jinnu, da ya tabbatar da ya samu ingantacce ba mai tsubbu ba a Unguwar Ma'amoorah. Gini nai ya ji gini na asibiti mai tsada, amma duk magungunan musulunci suke badawa. Nan ya shiga ya tambayi yanda abin yake suka masa bayani kuɗaɗen da irin magungunar. Bai bar asibitin ba sai da ya yi booking.
Washegari ne ya kira Salman ya tura masa kuɗin da zasu shirya ma Salmah tafiyar. Sannan ya faɗa ma iyayensa da sauran yan uwa Salmah na tafe. Nan murna ya karade zuriar, take aka fara shirye, ana aika ma yan uwa na nesa da na kusa.***
Ranar da aka kira shi kan cewa jirgin su Salmah ya taso nan ya cika da murna. Yar da rabon da ya ganta tun tana da shekara hudu zuwa biyar ce zai gani a yanzu. Can ya tuna da rabuwar su da RAHANATU, take zuciyar sa ta tunatar da shi kalaman su na karshe ga junansu. Take ya zaro waya ya danna lambobinta. Kara na uku ta ɗaga, zazzakar muryarta na masa sallama.***
RAHANATU...Zaune take, ta dawo daga wani taro da aka yi na yan asalin Kasar Nijeriya da suke zaune a Kasar Saudiyya. Hankalin ta ya tashi saboda wanda ta gani a wajen hakan ya sa ta barin wajen ba don ta shirya ba.
Suna zaune kamar an ce ta ɗaga kai nan ta haɗa ido da shi. Bata wani saba da shi ba ko san da ya ce yana son ta, amma ko ya siffansa ya chanza ba zata taɓa manta fuskar da ta ɓata mata rayuwa, fuskar da kan zo mata cikin kashi a 70% na Barcin ta tun faruwar abin. Fuskar da mamallakin sa ya zama SILAR AJALIn mahaifinta da ta fi so duk duniyar nan. Fuskar da ta hana ta tausayin ya'yan ta lokacin da suka fi kowa bukatar ta. Take ta ji ta tsani zaman Saudiyya, bata kai ga tantance abin yi ba taji muryar sa na faɗin.
VOCÊ ESTÁ LENDO
SILAR AJALI
Ficção GeralDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...