Tabuk cityShiru tayi bayan tafiyar sa, sam hankalinta ya kai kololuwa wajen tashi. Wayarta ta ciro ta latsa wasu lambobi sannan ta kara a kunnenta.
"Hajiya Rahanatu ina yini" aka faɗa a ɗayan bangaren bayan an ɗauki kiran.
"innar yara kina lafiya? Ya kuke ku duka?" Ta tambaya zuciyar ta na kuna.
"muna lafiya lau, su Salma dai yau satin su uku da komawa MARKE. An sami wani azzalumi da ke neman ɓata ta, shine na tura su wajen goggo. Na tabbatar da ma yanzu sun zama Yan gari" Ta karasa tana dariya. Itama Rahanatu dariya tayi wanda za'a Iya cewa yafi kuka ciwo.
"Allah dai ya kare mu da zuri'ar mu daga sharrin azzalumai, ita goggon kuna saya kuwa? " Ta tambaya cikin kulawa.
" Goggonki har yanzu kauyis ce, cewa tayi tunda ba baba bata da wanda zata kira, ko la'akari da ganin mu a nesa bata yi" Ta karasa da dariya kuma.
"Allah jikan baba, yasa yana dausayin Aljanna, zan turo miki kuɗi don Allah ki je ki duba goggo. Nagode Allah bar zumunci " tana kaiwa nan ta kashe wayar a lokacin kuma ta fashe da kuka
" Ya ci ace na koma gida haka nan, ina kawar gidanmu" Ta faɗi a gida. Nan take zancen mahaifinta ya dawo mata;"karatun ki shine hanyar ceton mu, ke kamar gona ce da muke shuka muke fatan girban albarkacin noman mu anan gaba, karatun ki ne zai sa mu san dadin cire kudi mu biyawa kanmu bukata, karatun kine zai sa wata rana mu daina lissafa abincin da muke ci, karatun ki ne zaisa wata rana mu iya siyan sutura har mu manta adadin wadda muka mallaka, karatun kine zai hana mu kwana da yunwa, karatun kine zaisa a rika tunawa damu a matsayin masu rufin asiri. Dan haka kada kiyi wasa da karatun ki rahanatu"
Kuka sosai tayi kamin ta share hawayen ta tayi hanyar zuwa gidan ta. Nan ma a kujerar falo ta zauna tana tunanin rayuwar ta, tun da ta baro gidansu da ciki wata uku wanda Hadi duk ya ja mata wannan.
MAY 1990
"Rahanatu meyasa zaki min haka, na kwallafa rai na akanki me yasa zaki min haka" faɗin Mal Tanko ranshi na masa suya,
KAMU SEDANG MEMBACA
SILAR AJALI
Fiksi UmumDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...