Tun daga abin da ya faru a masallacin idi gulma ya fara yawo a kauyen marke kan cewa su salma Shegu ne ba ta hanyar aure aka haife su ba. Ba bu halin a gansu da yaran unguwa musamman ma dai salma iyayen zasu fara
"kar na sake ganin ki da Shegu, shege ai kwashe albarkan 'ya'ya yake, "
Ko kuma su ce
" kuna biye ta Shegiyar yarinyar nan sai ta raba ku da mazajen aurenku don ita kam babu mai kwasar ta"
Hakan ya kara tada musu da hankali musamman ma goggo, nan kuma ta ɗauki karan tsana ta ɗaura ma Salma. Kullum faɗi ta ke
"Shegiyar yarinya mai bakin jini, kin zama min bala'i ban san mai yasa ta saka miki suna na ba"
Nan rayuwa yai ma salma kunci, duk da karancin shekarunta ta san ta zauna tana tunani. Kaɗaici yayi mata yawa, in da abin da ta tsana yana bayan zuwa makaranta boko ko muhammadiyya don da wuya taje ta dawo lafiya. Kawayenta ma sun daina biyo hanya da ita saboda tsawatar musu da iyayensu suka yi amma kam a harabar makaranta suna tare da ita. Sannan suka daina shigar mata faɗa don an hare musu kunne akan lallai da gaske ita Shegiya ce.
***
"Dalla Shegiya ki dena kallona kafin ki ɗebe min albarka, ko wani yace uwarki ta je yawon karuwanci, wa ya sani ko ba ku kaɗai bane don an ce da cikin Hadi ta bar marke" faɗin wata Hajjaris tana mai tunkuɗe Salma da tazo wucewa ta gabanta.
"Zo nan Salmah" faɗin malamin turancin su da ya gama jin komai. Tun bayan dawowarshi daga hutun shekara ɗaya da rabi da ya yi ta kula ya ke bata kulawa ta musamman don har an fara Gulman son ta yake. Sum sum ta bi bayan shi hawaye na riga rigen gangarowa kan kuncin ta.
"me ke faruwa ne Salmah, na kula kin yi duhu kin rame sannan kin rage zama tare da kawayenki, yanzu kuma ga kalaman er rakaɗin nan akanki me ke faruwa faɗa min" Ya na magana da gani hankalin sa a tashe yake. Maimakon ta bashi amsa sai ta sa masa kuka, wanda ita kanta ta san rabon da tayi irin sa ta manta don kuka ne wanda ake yayin da aka samu kafaɗan jingina akai.
"share hawayenki, ni ma tamkar uba nake a gare ki, ki faɗa min damuwar ki in bai fi karfina na ba zan magance miki" Ya faɗi cikin sigar lallashi.
"tun sallar idi na bara wancan ne ake kiran mu Shegu, a hankali har kowa ya yarda cewa mu Shegu ne, kawaye na duk sun guje min wai ance shege na kwashe albarka. Goggo kullum cikin hantarar mu take musamman ma ni, gashi tun da muka zo garin nan kusan shekara uku sau biyu inna Amina ta zo, tace innarmu zata zo har yau bata zo ba" Ta karasa tana mai kara sakin kuka.
"kai! Je ka ss2 ka kira min Salman Imran" ya faɗi ma wani yaro da ya zo wucewa.
"ki yi hakuri, ni nan sheda ne akan mahaifiyar ku, mutuniyar kirki ce, asali nine mutum na karshe da ta gani sanda zata bar garin nan." Ya karasa yana mai ɗaura tabarau a idonsa.
"ka san ta ne dama " Ta faɗi da sauri
" Asalin mu yan garin nan ne, ina da shekaru ashirin da ɗaya, kaddara ya raba ni da garin nan. Da yawa ba zasu gane ni ba. Amma dai RAHANATU yar halak ce, ya ta gari ce, kusan abu ɗaya mabambanta ya raba mu da garin nan. Kullum... " isowar Salman ne ya sa yayi shiru.
" Zauna" Ya ce masa bayan sun gaisa.
"shin ka san Mahaifin ku? " Ya tmby shi direct
"zan iya tuna shi amma gaskiya ba zan gane shi ba" Ya faɗi kamar ana tirsasa shi yayi magana.
"Suna tare da mahaifiyarku sannan shi ɗan asalin ina ne? Ya sake tambaya duk da wani sashi na ranshi na faɗa masa ba zai samu amsar sa ba.
"ni ma ban sani ba, kila da gaske mu shegun ne shi ya sa ta turo mu kusan shekara goma ba waige. Mun zo ina da shekara takwas, salma shida suhayl biyu da yan watanni. Yanzu shekaru na goma sha bakwai, salma mai sha biyar ko kuda bai taɓa cewa y a na son ta ba, sai yaushe?" shima ya sa kuka kamar karamin yaro.
Bai hana shi ba har sai da ya gaji ya yi shiru. Sannan ya ce
"kai ne babba, zan biya maka kuɗin jirgi ka je umra, se ka nemo iyayenku, yanzu ka nemo lambar wayar Amina, se mu samu na ita RAHANATU ɗin, sai in kira in ce zaka zo"
"ai ina da lambar" Ya katse shi, bai jira cewarsa ba ya ruga a guje ya je ya ɗauko.
Nan ya amsa sannan ya sallame su, nan suka fita cikin farin ciki da shi malamin albarka.
***
Zaune su ke tana zuba masa fura shi kuma yana ta zuba mata shagwaɓa."Abdoul da ace ban maka aure ba da na yarda da wannan shagwaɓar amma tun da na yi ka tashi ka je can kai mata " Ta faɗi ganin yanda ya narke a kan kujera yana jiran furan.
" kai kai kai mamata ai ko tsufa mu kayi ba wacce, za ta ga shagwaɓar nan sai ke, kai Allah ya kaimu Aljanna a can zai fi daɗin yi tunda ba ko ɗigon bakin ciki" Ya faɗi yana dariya.
"Aameen ya rabbi, ya su Salmah, da fatan kana kokarta wa, hakan zai sa Allah ya dube ka ya kawo maka komi cikin sauki" Ta faɗi tana dariya.
"Wacece salma kuma hajiya" faɗin wacce ta shigo wacce kallo ɗaya zaka mata ka hango kyawunta, fara ce ba can ba, tana da cikakken sura da ba ko wace mace ke da shi ba. Sanya ta ke da bakar jallabiya ta yane kanta da gyalen shi hakan ya kara fito mata da kyawunta. Zaman da tayi saitin kafar sa tare da jan masa yatsa ya ɗauke idanun Hajiya daga kan ta.
"yar mijinki ce" faɗin hajiya tana mai mikewa.
"Ya kuma? Na shiga uku ni Zainabu ta ina zan fara" Ta faɗi a fili
"Abdoul da ma ban yarda da dawowarka garin nan ba, ashe duk damuwar da ka ke nuna wa akan rashin haihuwa ta duk karya ce, ka san kana da wasu ne, munafuki azzalumi" Ta faɗi tana kai ma sa duka ta ko ina.
"Kinga, ina da su ko da kika auren, ke kan ki matsala ce a gare ni balle in zauna ina faɗa miki matsala ta" Ya faɗi yana mike wa don ya ga tana shirin tara masa jama'a.
Ganin yana shirin barin ta wajen ne ya sa ta Mike haɗe da rungume shi. "kayi hakuri masoyi na ka san ina bala'in kishin ka shi ya sa Kaga na damu"
Gam ya rike ta Sanan shi ma yayi mata raɗa da cewa " ki kwantar da hankali ke kadai ce matata a yanzu, asali ma su ɗin uwarsu na aure a Saudiyya. Ina son ki da yawa" Ya fadi yana mai shafa bayan ta. Aranshi faɗi ya ke " ina zan iya da rigima" ita kuma murna take, nan take ta fara tallar makilin don ta gama yarda da shi ko don ba ta taɓa kama shi da laifin cin amanar sa ba tun haɗuwar su a bariki har zuwa aurensu.
***
Cikin sati uku duk wani shiri na tafiyar salman an gama, malamin su din da kan shi ya je yayi ma Goggo da hakimi maganar kuma duk suka yi Na'am da hakan.Wasiku kala uku uku Salmah ta rubuta ma mahaifiyar su da mahaifinsu tana mai nuna musu Yanayin rayuwar da suke ciki na tsangwama da aibanta su da kiran su Shegu da ake. Sannan ta ce su aiko da kuɗi duk su koma gaban su da rayuwa.
Shagon Danladi mai hoto taje tayi Kala kala, duk ta haɗa a embilo ta ba Salman ya sa kayan shi.
Ranar Alhamis jirgin su ya tashi daga filin jirgin Aminu Kano da ke birnin Kano, ya rabu da yan Uwansa cike da fargaban shin zai samu abinda ya je nema ko ba zai samu ba?
Thank you for your time and consideration. Keep reading, voting, recommending and commenting. Silar Ajali is no where without you. Loving you
Ummu-Abdoul taku ku kaɗai
YOU ARE READING
SILAR AJALI
General FictionDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...