Kyan alkawari cikawa. Da kyar na iya haɗa wannan, na dawo meeting a gajiye, karshe karshe ma ina typing ina gyanyaɗi. So filis manage dis.
Cikin sati biyu sunyi nasaran cire cikin da ke jikin Rahanatu, Laraba mai dalili kowa ya san ta a matsayin kilaki mai zaman kanta sannan magajiya ga kananan karuwai. Tana da hanya ga manyan alhazai da yan boko masu kuɗi. Ta kan haɗa taro asirrance inda take ɗaga sabuwar karuwar da ta samu, taron kn wakana duk daren goma sha uku ko huɗu ga wata lokacin wata yayi haske. Wanda ya zuba kuɗi mai yawa shi yake tafiya da karuwan. Tun da ta samu farar yarinya mai diri ta ji sanyi a ranta don kuwa babu kwastamomi a lokacin.
Musamman ta biya mai gyaran jiki tayi ma, aka mata kunshi da kitso nan take kyawunta ya fito, tayi kyau abinda. Sai da ta tabbatar da ta sha ababen da zai motsa mata sha'awarta duk don kar ta gardama ranar taron
"ki kwantar da hankalinki in muka taki sa'a sai ki kwashi bandir bandir na wazobiya don na san zakiyi tsada, da kuɗin zan saka ki a makaranta har ki kai ga cin ma burin mahaifinki, Kinga dai kamar wasiyya ya bar miki, in baki cika ba wutar Allah zata ci ki" da irin kalaman nan ta samo kan Rahanatu sannan tasirin magungunar da ta sha yasa bata ko gardama ba.
***
IMRAN SALMANSaurayi ne matashi ɗan shekara talatin da biyu, Asalin sa ɗan Kasar Sudan ne, Imran na da son karatu ba ko kaɗan ba amma kasancewar sa daga zuriar da ba'a karatun boko yasa bai samu damar cigaba da karatun ba tun bayan kammala sakandire har sai Kasar Saudiyya ta kai agajin taimakon karatu ga mutanen Kasar Sudan sannan ya samu wannan dama.
Bayan an sama masa gurbin karatu a jami'ar da ke yankin yambus sanaiyya wato yambu industrial city. Tun bai saba ba har ya saba. Sannu a hankali har suka kammala matakin digiri suka ɗaura har sai da suka kai ga matakin digir digirgir Sanan suka waiwaye gida. Nan ma kwana biyu yayi ya iso birnin Kano don abokinsa Haroon ya faɗa masa saukin samun aiki a garin na Kano.
"Imran ka shirya yau zan kaika wani wajen da se kanka ya ɗaure, ko hukumar shari'ar birnin nan basu taɓa sanin wajen ba" faɗin Haroon cikin harshen larabci.
Dariya kawai Imran ya sa don shi a rayuwar sa ba abin da ya fi so kamar shakatawa, tunaninsa kuwa wani wajen zai kai shi, don ya kai shi wajajen shakatawa a lardin Kano da dama kamar su ruwan tiga da ɓagwai. A haka ya shirirantar da maganar suka cigaba da hira da shirin zuwa intabiyu da zasu yi a kwana uku.
***
Karfe tara na dare Haroon ya tada Imran da ya fara barci suka kama hanya. Hasken wata ya sa basu bukaci fitila ba suka gangara zuwa wani gida chan a unguwar Nalambata kusa da fage.
Naira ɗaya suka biya suka shiga gidan inda mutane sun taru iya taruwa. Don akalla zasu kai 50 a zazzaune kan tabarmin kaba.Can se ga yarinya karama cikin riga da wando da suka ɗame ta suka fitar da surarta, kanta ya sha kitso hannunta yayi jajir da lalle yayin da na kafafunta yayi baki kirin saboda takin da aka sa mata. Saman kujera aka mikar da ita kafin Laraba ta tsaya a tsakiyar mazaunin mazan ta ce "ga haja. Cinikin kwana bakwai kawai za'a bada"
"me ake yi anan" Imran ya tambaye Haroon kasancewa baya jin hausa. Nan Haroon yayi masa bayanin abinda ya fahimta da irin taron Laraba. Nan ya kalli Rahanatu babu abin da yake hangowa sai tsantsan rashin wayonta da kankantar ta, takaici fal a zuciyar sa ya dai zauna yana kallon ikon Allah.
Ciniki ya fara tun daga naira ɗari har aka kai dubu ɗaya da ɗari biyar. Nan ta tsaya chak ba motsi ba komi, ana shirin sauke ta ne Imran ya taka ya fita ya isa har ga Rahanatu ya cire rigar jikinsa ya lulluɓe ta da shi Sanan ya ce cikin gurɓataciyar hausan sa da ya tsinta a bakin su Haroon da yara bayan zuwan sa kano;
"Zan aure ta, zan baki naira ɗari biyar da mota beetle (kande ba ɗuwais)"
"Bamu yarda ba, cinikin kwana bakwai tace, zaka ci ka rage mana, amma don bakin ciki kabila da kai kazo ka ce zaka tafi da haja, kila ma arne ne baku ganshi fari ba" faɗin wani hakimi cike da kumfar baki.
"Haroon zo ka faɗa musu ko su yarda ko in rubuta kara akan sun sace min mata" Ya faɗi da larabci, nan take Haroon ya fassara musu yana mai cike da mamakin abokinsa.
"Kinga Laraba basu ita, kin ga larabci suke irin yaran nan ne da ake ɗaukan su aikin bincike, in zance ya koma gun mai martaba Wallahi zamu raina kanmu, kun san baya son baɗala " faɗin wani zaune da Babban riga.
Nan waje ya hargitse masu tsoro suka bar wajen tun kafin a zo ayi gaba da su, wasu kuma na zaune suna jiran su ga an ture ma buzu naɗi. A Haka Haroon ya fakaice ido ya fice da Rahanatu bayan ya yara ma Imran inda zai jira shi.
Basu ankara da rashin ta ba har se da suka fice, nan fa wasu suka kara tsorata suna cewa "ai wannan Kyawun nata yafi karfin a ce mutumce. Da gani ka ga aljana gashi ta ɓace, shi ma dai in aka bibbi dangi ne mu gudu" Haba ai ɗaya Baya jiran ɗan uwansa suke barin wajen.
Muje zuwa sannu a hankali, ba'a yi komi ba Yet more chapters more RAHANATU Salma issues more more more. Keep voting and commenting plsss
Loving you.....
ESTÁS LEYENDO
SILAR AJALI
Ficción GeneralDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...