Mutanen marke suka ɗauka, duk inda mutane suka taru ba mazan ba ba matan ba duk zancen kenan "Mahaifin su Salmah ya aiko da kuɗi Salman yaje" . Wasu su kara da "ai an ce bai da lafiya ne zai ɗaura shi a kan hidindimunsa ne" labari dai kala kala masu hassada su ce "ai so ya ke ya bautar da shi kamar yanda shi ma aka ce a wahale yake zaman Saudiyya." nan fa yan son jin gulma suka fara tura ya'yansu zuwa ga Salmah in kuma suke da dama su ka fara zarya gidan Goggo.
Duk abin da ake Salmah ta kan ba malam labari su yi dariya. Don tun ranar da ya musu alkawari ta maida shi aminin ta, sannu a hankali har suhayl ya saba da shi. In yana cikinsu kuwa nan zaka ga tsantsan farin ciki a kan idonsa da yaran.
"Baba malam sai ka ji Batul wai ni take so da kawance, ka san de yanda ta fi kowa hantara ta da ita da yar kura. Anya ba wani munafunci ta zo yi ba? " Ta karasa tana tagumi.
Dariya yayi kafin ya ce mata
" ki bi su da yanda suka zo miki, banda wulakanci dai, Kinga duniya ba'a rike mutum gam gam, haka ba'a kin mutum da tsanani shi yasa. Ina su Ummitr, duk da na san fin karfi aka musu amma in aka ce zasu juya miki baya yanda suka amshe ki farkon zuwan ki zaki amince? Haka rayuwa ta gada, in na faɗa miki abubuwan da nayi a da Ina mai tabbatar miki ko kallo ba zan ishe ki ba. Saboda haka ko da yaushe ki bi kowa da fatan alkhairi."
"ka yi rashin ji ne Baba? Kace ka san mamata, faɗa min ya take sanda take garin nan" Ta Yi saurin katse shi
"mutuniyar kirki, ga nutsuwa, ga son karatu, ke duk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani ɗan adama bi ta hanyar duk saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani matashi dake kauyen da makwabtan kauyukan sun shaidata ne a matsayin daliba mai zuwa makarantar boko.
Da yawa daga cikin su suna ganin haukar iyayenta da suke iya barinta tana bata sauran adadin shekarunta a hanyar neman karatu.
Ta samu tarin makiya da mahassada a garin nan, wasu a dalilin sun furta suna son ta mahaifinta malam Tanko ya ce shi yar sa karatu take. Shi ya sa da ta haɗu da JARRABI mutane basu yi mata uzuri ba illa ma aka yi amfani da maraicin ta suka tozarta ta, ita kuma Goggo Kunyar nan da ake ma ya'yan fari ya sa ta taimaka masu wajen hantarar ta. Kar ki damu, duk Yanayin da take cikin Salman zai zo mana dashi. Mu cigaba da mata addu'a, Insha Allah muna tare da nasara. Allah ya muku albarka "" Aameen ya rabbi " Ta faɗi cike da murna, don ba'a taɓa faɗa mata kalamai masu cike da alkhairi ba dangane da mahaifiyarsu, nan take kaunar malam ya cika mata zuciya, don ta tabbatar da ba wanda ya kai shi son su.
***
Ko da Salman ya isa Kasar Saudiyya, gari mai tsarki ya fara isa yayi umra, inda ya roka ma iyayensa gafara da shiriya da kuma rahma. Ya roka ma yan uwansa da kuma sauran yan uwa musulmi. Malam ma ya sha addu'a da fatan samun biyan bukatun duniya da lahira. Daga nan ya shiga jirgi zuwa birnin Tabouk, cikin tafiyar mintuna hamsin suka isa. Anan ya iske mace sanya da nikabi amma sagale a wuyarta wani irin kwali ne an rubuta sunansa SALMAN IMRAN ɓaro-ɓaro akai.
Kamar yanda ta shaida masa a wayar da suka yi kafin ya taso, zuwa ya yi ya rungumota ta baya. Nan take kuma sai ya saka kuka. Itama duk juriyar ta sai da hawayen da ke makale a idanunta ya sauko.Bayansa ta shiga shafawa alamun lallashi har sai da taji yayi shiru ba tare da tace da shi wani abin ba. Ganin yayi shiru ne ta ɗaga kansa ta kalle shi, duk da nikabi ya ɓoye murmushin da ke kwance a fuskar ta, idanunta sun gagara ɓoye kaunarta gare shi.
"yaro na ka girma, kana shirin fi na tsawo" Ta faɗi cikin farin ciki.
"Marhabanbika yaa khalilie " Ta faɗi tana mai rungumar sa da kyau. Daga haka suka shiga mota zuwa gidanta. Idanunsa na kan gine-gine da tsare tsare da tun da yayi wayau bai taɓa cin karo da irin sa ba.
ESTÁS LEYENDO
SILAR AJALI
Ficción GeneralDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...