Babi Na Ashirin Da Bakwai

1.4K 154 58
                                    

Assalamu Alaikum warahmatullah. Da fatan kuna lafiya. Am so sorry for the long break, exams plus fasting things. Ubangiji Allah ya sa muna cikin yantattun bayi a watan ramadan, ya yaye mana matsalolin mu ya kyautata rayuwar mu.

Albishir din da zan muku shine nan da 2wks zan kammala Silar Ajali bi izni Rabbi. Sannan imidiately zan muku posting wani da already akwai shi a kasa ko a kammala gidan  aurena.

Anyways, thanks for sticking around. I love you all for the sake of Allah...

"Shin akwai abin da zai sosa maka fatar ka sama da faratanka?" Inna ta tambaya tana mai tsare ta da ido. Ganin bata da shirin magana kuma da alamun jikinta yayi sanyi sai ta cigaba da cewa
"kin sa kai kin tafi, yaranki kuma ko oho, haka ake yi? Ban san me yasa son duniya ya ke rufe ma iyayen zamanin nan da har sukan manta cewa yara amana ne a gare su, kina tinkaho Goggo salame kika bar ma ajiyar yaranki kin manta cewa ke ɗin da ta haifa ta gagara riko ta sake ki kika bi duniya. Wallahi in basu yafe miki ba tun wuri ki nemi wajen zaman ki a wuta, don amana ba zai barki ki tsallake siraɗi ba" Ta faɗi zuciyar ta na mata zafi. Ganin shirun yayi yawa sai ta cigaba

"kar ku ga laifi na, kin san hadisi ingantacce ya zo cewa amana da zumunci zasu jira ɗan Adam a siraɗi kowanne a gefe da gefe sun saka siraɗi a tsakiya, duk wanda yaci amana ko ya yanke zumunci ba zasu bar mutum ya tsallake ba. Fisabilillahi RAHANATU Wanne ne baki taɓa ba. Ki ji tsoron Allah ki tuba ki nemi gafaran ya'yan ki" tana kaiwa nan ta  mike ta bar su zaune jugum.

                                ***
An ɗaura auren Salmah da Taha , Wallima kawai IMRAN ya haɗa, sannan ya mika ta ga dakin  mijinta yana mai mata nasiha. Farin ciki ne fal a zuciyar ta don itama dai gata yau a matsayin matar aure. Kallon ciki da falon da ya kama mata ya zuba katifa da abin da ba'a rasa ba take tana faɗin

"Happy independence Salmah" ta faɗi tana yin tsalle a kan gadon fuskanta cike da fara'a. Sam bata ji wani ɗar ko tashin hankali da amare ke ji ba, ita farin cikin ta yancin kan da ta samu.

                   
                            ***
Sai karfe ɗaya na dare ango ya shigo, bai yi yunkurin isa gareta ba don a tunanin sa ta daɗe da yin barci. Iyaka kwanciya yayi sai minsharin  shi ta ji, dariya ta fara ciki ciki don aunowa tayi minsharin da yake ita da aminanta ne kewaye da shi da sun more dariya.

Washe gari bayan sun idar da sallah asuba ya bata kudi ya bata yan jinai 5 guda ashirin, ya sa kai ya tafi. Murna ya cika ta don a zaton ta kyautar da ake cewa miji na ba amarya washegari biki.  Barci tayi mai isar ta se kiran sallah azahar ya tada ita. Ta tashi tayi sallah ta fara neman abin da zata ci. Raguwar naman da suka ci da safe ne ta dauka ta ci, sannan ta koma barci, da la'asar ta sake tashi tayi, nan kuma sai ta fara tsorata ganin bai ko leqo ta ba. Kawar da tunanin tayi, ta cigaba da sabgoginta.

                              ***
Tun tana kallon lokaci akayi karfe tara, goma, sha ɗaya, sha biyu babu shi babu alamun sa, nan ta kara tsurewa,
"ko dai yayi hatsari ya mutu ne" Ta ce da kanta, bata tsorata ba sai da ta tuna bata da waya, bata san hanyar da zai fitar da ita zuwa gidansu ba, ga miji bai dawo ba. Wani irin kuka ta saki tana mai tausayin kanta.
Tunanin su Rufaida, su ummitr take da rayuwar su, yan uwanta maza su Salman da Sulayl har ta kawo rayuwar ta a Kano, zamanta da mahaukata sai taga ai da a Aljanna take tunda ga wa'inda ta sani kuma suke sonta.

Barci ɓarawo ne ya sace ta, ta tashi tayi sallah tana kuka, ta idar kenan  ta ji ana buga mata kofa, tsoro ya hana mata motsi don tunanin ta an zo a kashe ta ne itama.

"Salmah" muryar mahaifinta da taji ne ya sa ta sakin murmushi, ta je ta buɗe kofar, bata jira ya karasa shigowa ba ta rungume shi tana mai sakin kuka.

"kiyi hakuri, kiran gaggawa aka yi ma mai gidan ki a can Saudiyya, amma kwana bakwai kawai zai yi ya dawo" Ya faɗa cikin harshen Hausa da bai gama nuna ba.

"in Kwaso kayana mu tafi can gidan ko" Ta faɗi tana mai murna zata wajen matar babanta mai sonta

"Habibty Sudan ba  Kano bane, anan in aka kai mace dakin mijinta mutuwa kaɗai ne ke sa ta fito, sai kuma saki wanda ba karamin abu ke sawa a yi ba. Ita mata zata tsaya komi wuya komi daɗi ta tsare dukiyar mijinta ta rike amanar kanta da ya bar mata, kin girma ne, zan dinga zuwa akai akai in duba ki, Allah yana tare da ke, ina rokonsa yayi miki albarka".

Haka yayi ta  lallashinta da bata baki cikin lallausan lafuzza haɗe da kawata mata gidan aljanna da hakurin ta zai bata yasa taji ta wasai, har bata wani damu da tafiyar sa ba. Abinci kawai Taci ta fara kallo duk da ba wani fahimtar yaren take yi ba amma itace har da kyakyatawa.

                            ***
Sati ɗaya, biyu, uku har aka shiga wata daya, biyu babu Taha ba alamun sa. Tun salma na damuwa har ta fara manta cewa da aure a kanta. Hidiman gabanta kawai take, tayi girka abin da take son ci, tayi barci tayi kallo. Kwanciyar hankali yasa tayi ja tayi ɓul-ɓul da ita, duk mahaifinta ya kawo mata ziyara da kalan hirar da zai mata, wanda da yawa akan sirrin zaman duniya ne da wasu kalubale da ya fuskanta a rayuwar shi. Ko kaɗan baya mata zancen Nijeriya don baya son abin da zai daga mata hankali, farin cikinshi ganin da yake mata yalwace da farin ciki.

Yau ma kamar kullum, zaune yake yana bata labarin yanda rabon su ya ja shi zuwa Nijeriya da yanda ya suka yi Rayuwar su a Kano kafin komawar su Nijeriya. Dariya take sosai don daga gani yana cikin shaukin kewar mahaifiyarta, kallon sa tayi tace
"ka je Saudiyya ka nemi sulhu da ummanmu don na ga kana ji da ita"

Shima dariya yayi sannan yace

"ai ina ga tun washegari zuwan ki Kasar nan mahaifiyarku ke Nijeriya, ban san me ya faru ba amma an ce min an kada ta ne" Ya karasa yana dariya

"Ko dai dama saboda ni ne taki dawowa? " Ta faɗi ranta a ɗan bace.

" Toh ke dai ba gaki hankali kwance ba, kinyi kyau kin fito sak balarabiya..."
Sallamar da Taha ya doko ya katse masa hirar sa. Da murna ya tarbe shi suka gaisa, sai a lokacin Salmah ta kare masa kallo.

Kyakkyawa ne ajin farko, yana da tsawo da idanu da sau daya ta iya haɗa nata da shi saboda kwarjini. Askinsa da yanda yake Shirya gashinsa ya taimaka wajen kara ɓoye shekarunsa, take taji ta kamu da son wanda aka kira da mijinta.

Gaishe shi tayi sannan ta Mike zuwa kawo masa abin tanɗa. Nan suka gaisa da mahaifinta sannan ya tafi shima. Tun da ta shigo da faranti dauke da ruwa da kayan marmari yake binta da kallo, motsin kirki ya kasa don gaba daya ta tafi da imaninsa. Kasa ɓoye maitarsa yayi, chak ya dauke ta sai zuwa kan gadon su. Magana ya mata a kunne in da iya fahimtar ta a larabci ta gane abin da yake nufi duk da ba ta ji duk abin da ya ce bane.

"mijinki ne kar ki bari tsinuwar Allah ya hau kanki" Ta tuna karatunsu na islamiyya, duk da a tsorace take bata nuna ba balle tayi yunkurin hana shi.

Hanyar da ta ga ya bulla ne yasa tayi saurin hankade shi, ta mike da sunan guduwa.

"Haza Haramun" kawai take iya nanatawa don shine kawai larabcin da take iya tunawa.

"Taɓ, tsinuwar Allah fa, ai ko da aka ce ayi biyayya ga miji ba'a ce har a saɓon Allah ba, ta faɗi a tsiwace tana maida tufafi. Bata yi aune ba taji an dauke ta daga baya.  Kan gadon ya maida ita duk yunkurin ta na son tsiratar da kanta. Dukkan karfin sa ya sa mata nan ta fara ambaton duk wani addu'a da ya zo kwanyarta. Ihu take da kuka har muryar ta ya dusashe, ta Sallamar don tana jin alamun zai samu nasara akan ta, kulle idanu tayi ta ce "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" , kamar ance ta waiga ta hango fitilar gefen gado, nan ta jawo da hannunta ta rutsa masa a kai, bai dago ba ta kara masa, nan kuma wani karfi ya zo mata ta hankade shi cikin jini ta ja hijjabin da tayi sallan la'asar tayi waje.

                             ***

SILAR AJALI Donde viven las historias. Descúbrelo ahora