Babi Na Goma Sha Uku

1.8K 245 56
                                    

Alo my love my Valentino my hevry  hevry...  Wolla I so much appreciate yr luv.  Thanks for ur votes,  recommendations and comments.  We r finally #2 in the general fiction.  Pls keep voting and commenting let's hit 1...

MARKE  2007

A watannin da su Salma su ka yi a marke sun saba da rayuwar chan.  Basu da wata matsala don Goggo bata bari su fita ko ina daga makaranta sai masallaci ga mazan. 
   Yau ma kamar kullum sunyi gungu suna tafe suna hira,  tasowar su daga makaranta kenan.

"Wai Salmah shike nan baza ku koma Saudiyya ba kenan?  Ni fa in ni ce uwata da Ubana ke wata Kasar toh bazan zauna ba.  Taɓ!  Chan fa an ce ya haɗu ba kamar nan ba." Ummitr ta faɗi wacce dama kullum hiran ta Saudiyya, don bata da buri kamar shiga jirgi.

"Taɓ ba sai mutum na da uba bane zai je,  ai in shege ne haka za'a turo shi gudun yai rayuwar tukari" karaf farida Farha ta ce don da ma abin ya daɗe yana tsingulinta tun sanda Amma mai hura ta shigo ta  faɗa ma innarta cewan su Shegu ne.

Ummitr ta cire Hijjabinta ta ɗaura a kugu, ta tura ɗan kwalin ta zuwa gaba,  tayi tsalle ta chakumo rigar Farha, 
   "me kika ce,  yau sai kin faɗa mana inda kika jiyo"  faɗin Jiddo tana mai make ta a keya,  rufaida kuwa ɗebo kashin shanu tayi ta nufi bakin ta zata sa mata.  Nan fa ɗalibai suka taru  a wajen Salmah na kuka  ita ma Farha kukan take tana mai basu hakuri.  Se da suka yi mata ligis kafin suka kyale ta suka nufi gida.

Su ummitr na tsaka da cin abinci Zulai ta shigo da masifanta.

"Akan wani dalili ne  zaku yi ma Farha irin wannan cin zalin, ko dan kun ga ita kaɗai ce za ku zo ku yi mata taron dangi." Ta faɗi tana jan kunnuwan Umitta da Rufaida da ke cin abinci.

"Wayyo!  Wayyo ni Allah na kunne na zai tsinke" ummitr ta faɗi da iya karfin ta.  Hakan ya fito da matan gidan

"lafiya Auta me ya same ki" faɗin hajiya babba, watau kakar Rufaida.

"Hajiya kya ce haka mana,  ai ku ke ɗaure ma ta gindi take ma duk wanda ta so tsaurin ido.  In ban da haka  ina ita ina dukan Farha, ai ko a girme ta girme ta" Ta faɗi tana haki ba tare da tayi la'akari da tsufan hajiyar ba.

"da yake ma ita sakarai ce sai ta zauna karamar yarinya kamar ummitr ta taɓa ta. Toh Wallahi akul ɗinki,  malam amanar ta ya bar mana ba zamu bari a zalunci marainiyar Allah ba" faɗin Indo mabi da hajiya babba.

Nan zulai ta fara gunguni don dai a haife duk sun haife ta, tsabagen son Yaranta ne kawai da ya mata yawa yasa ta tsallako ta zo rama ma ɗiyarta.

"Wai me ya faru ne,  zulai ai ba haka yaci ki yi ba, duk su duka abin ki hukunta su ne,  Farha, jiddo da Rufaida dai duk yaranki ne,  ummitr kuwa kanwar ki ce.  Amma fa in da kara" faɗin Habi mahaifiyar Ummitr kuma wacce tafi sauran sanyi da hakuri.

"fitsarar da ta saba zata mana, in ban da rashin hankali har ke ce zaki taɓa uwar Malam, duk da kasa ya rufe idanunsa ai butulu ne mai manta alkhairi " Faɗin hajiya babba tana mai barin wajen gaba ɗaya.

Itama zulai bata ɓata lokaci ba ta ja tsaki ta bar sauran matan a tsaye.  Nan da suka fara cecekuce akan halin ta na rashin girmama manya.

                             ***
Tun da aka yi wannan, maganar bai sake tasowa ba har suka kammala ajin aka tafi hutu.  Nan aka fara azumi kuma wanda hakan yai daidai da hutun da suka samu a islamiyya. 
    Sam azumin bai wani damunta. Saboda da rana sukan je tafsiri da su Rufaida duk da su ne yan samun baya,  su kafa chafta duk wanda ya gitta sai anyi da shi.  Daga baya suka tsiri karanta littafan soyayya.

Sallah na da saura kwana uku an rufe tafsiri suna hanyar komawa gida suka yi karo da wani a mota kirar Honda civic, gilashin motar baki ne kirin,  ko da suka iso kofar gidan sai mai motar ya yafito su, nan suka kalli juna ita da su rufaida.

"Muje in mun ga alamun mai Satar mutane ne sai muyi masa ihu"  faɗin jiddo ba ko alamun tsoro a tare da ita.

A hakan suka karasa da sallamar su.  Bakin gilashin da ke sanye a idonsa ne ya sa suka kasa gane fuskar sa ko da Ace sun san shi.

"Sako ne daga Saudiyya,  gashi RAHANATU ta ce a kawo ma su Salman, na cikin bakin ladan nan shi ne na goggo salame.  Tace a ce tana gaishe ku duka zata zo nan ba da jimawa ba" cikin saurin murya ta faɗi sakon nan da nan salma ta amsa.

"Don Allah ka ce mata mu aminan Salma muna gaishe ta,  ni Asmau umkitr,  sai Hauwa Jiddo sai Rufaida,  don Allah kaji baba,  ko kaine Baba Imran" Ummitr ta faɗi kallo ɗaya zaka mata ka san tana cike da farin ciki kila ma fiye da  Salma.

"Bara mu kira maka goggon ku gaisa" faɗin rufaida ganin sauran duk sun ruɗe.  Ai ko haka suka dunfari gidan da gudu suna haki suna faɗa ma goggo salame, amma kafin su fito babu shi babu alamun sa sai ma dai shaidar taya.

"kai ko dai aljanni kuka gani,  in ba haka ba Ace sako tun daga Saudiyya amma bai tsaya an gaisa ba" goggo ta faɗi tana mai daura hannu a kirji.

"Aljani  kuma goggo" suka tambaya a tsorace.

"Eh ko kuma ɗan shafi mu lera ba, ku wuce mu je gidan yaya kafin a buɗe  don ba zan buɗe  in ɓace ba" Ta karasa tana mai jawo kyauren gidan nata. 

                              ***

"Hmmmn!" Ajiyar zuciya yayi bayan ya sauka daga kan titi.

   "Ta ina zan wanke kaina in nemi gafarar ta, na shiga uku"  faɗin mutumin nan yana mai cire tabarau da saukar da gilashin motar, gumi ke keto masa duk da kasancewa akwai sanyi sanyi kasancewar damina ake.

Fari ne ba chan ba,  sai dai kallo ɗaya zaka masa ka san cewa baya tare da wahala. Sai dai wani ɓari na fuskar sa na nuna damuwa a tattare da shi.

Akwai abubuwa da dama da suka zame masa "bakar kaddara"  wanda in da za'a tambayi burinsa bai wuce Ace ya sa kilina ya shafe shi ba ko ya wanke kamar yanda ake wanke datti a tufafi.

    Jan motar yayi ba shi ya tsaya ba sai a garin Gusau,  tafiyar awa biyu daga kauyen MARKE. Ɗakin mahaifiyarsa ya wuce,  masu yi musu hidima na gaida shi amma ko kallonsu bai yi ba duk da ba haka ya saba yi musu ba.

"Abdoul wai mai ya sa ba zaka yarda da kaddara, mai yasa ba zaka yi yakini akan Allah ya amshi tubanka ba.  Ba zance kayi abubuwan cikin rashin sani ba, amma ka bar kuruciya ya dibe ka.  Duk ba ma haka ba,  kayi hakuri na tabbatar duk inda take tana cikin farin ciki wanda hakan kaɗai ya isa ya saka ka murna"  Ta faɗi tana shafa masa baya kamar karamin yaro.  Shekarunsa talatin da bakwai a duniya amma bata taɓa gajiya da lallashinsa ko kuma shagwaɓa shi. Duk da kasancewar sa ɗan ta na fari.

Ajiyar zuciya ya ke saki,  hawaye masu zafi na kwarara daga idanunsa.  Sharewa tayi da tafin hannunta,  ta tashi ta ɗebo ruwan sanyi ta bashi ya sha.  Nan ta sa masa "LAA ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAL ZALIMEEN"  a bakinsa yana maimaitawa. Sai da ta ga ya fara samun natsuwa sannan ta tashi ta je ta cigaba da aikin.

Pls ku kara hakuri da ni.  But Insha Allah gobe zan sake wani May b 5k words if ɓa abinda Ya taso...

Su rufaida da aljan Hehehe na so ina wajen..

Ummitr Luv sannu da kokari ashe de Farha lazy ce...

Dearies  Are you seeing what am seeing???  Ɓa mu kai ko ina ba fa Ehe in fact yanzu muka fara.

Thnx pls comment,  share,  vote,  recommend..

SILAR AJALI Where stories live. Discover now