Babi Na Goma Sha Bakwai

1.9K 225 103
                                    


KANO TA DABO TUMBIN GIWA

La'asar sakaliya jirgin su Salman ya sauka a birnin Kano, bayan sun sauka, ya iske Malam yana jiran shi. Gidan baki na tahir guest palace ya kaisu. Anan abinci mai lafiya suka iske sannan ya yi wanka suka sallaci magriba ya dauke shi suka fita zuwa gari. Duk da ba wanna ne zuwa sa na farko garin Kano ba, amma kasancewar wannan zuwan da wayonsa kuma ya fito birnin Saudiyya sai ya kara gane cewa Zazzau ta fi Kano haɗuwa. Washe gari Bayan sun kammala karin kumallo ne suka je gidan Inna Amina, nan ma dai sama sama suka gaisa don suna hanya.

Murnar ta kasa ɓoyuwa yayi, faɗi take ba kakkautawa "Ɗana ka ga mahaifinka toh Ya wajen su RAHANATU" dariya kawai yake bin ta da shi tun da ya amsa mata da farko.

Ko da mijinta ya taso daga Barcin da ya ke bayan asuba ya ga salman din cewa yayi "Me ya dawo daku gidan nan bayan na sa katanga tsakanin ku da iyali na, ita in ba zata iya hakuri ba sai ta tashi ta bi ku" Ya faɗi yana zazzare idanu, a zuciyar sa addu'a yake Allah ya sa wannan ya samu ya haye Salmah. Bai karasa Mafarkin ido biyu ba ya ji abin da ya girgiza shi.

"Dawowarsa kenan daga Saudiyya, Mahaifin su ya turo masa kuɗin jirgi ka ga har umra yayo Wallahi" Ya ji inna Amina ta faɗi, hanjin cikinsa sai da suka murɗa don bai taɓa tunanin zasu rayu cikin gata ba bayan ya kore su, a tunanin sa sun gaji da gararanba ne suka dawo duk da Idanunsa sun karanto masa hutu a tattare da shi. Shiru duk suka yi sai chan yayi shahadar faɗin

"Zo ka fita min a gida, kuma duk sanda ido na ya sake tozali da kai a gidan nan tabbata sai na wulakanta ka" Ya karasa yana kumfar baki haɗe da nuna masa hanyar kofar fita.
"Amma... "

" Kar ki damu inna, da mota muke a waje za'a kai ni har gida, Kinga ba sai mun ɓata masa lokacin sa ba, na barka lafiya baba " Ya karasa Yana kallon baba cike da murmushi" yana fita kuwa suka ɗauki Hanya, anan yake bashi labarin da ba su samu damar yi ba tun bayan saukar sa, tiryan tiryan ya ke faɗa masa labarin tun da ga isarsa Saudiyya har dawowar sa. A cikin haka ya ce " wai wanene Hadi sheɗan?"
Shiru ya ziyarci motar suna tafe sai karar iskar motar kawai ke tashi. Chan dai malam ya nisa ya ce
" Hadi na nan, ya shiryu in ka ganshi zaka rantse ba shi ne wancan dinnan ba" Ya faɗi Yana murmushin da bai wuce fatar bakinsa ba.

"Toh wai me ya faru bayan tafiyar ummi na, kwanaki kace mana kai ne mutum na karshe da ta haɗu da kafin barin ta marke. Ta bani labarin abin da ya faru zan so jin karshen" Ya faɗi yana mai maida hankali don ya ji komi.

"Hmmmn! Da tuki zanji ko da labari? Amma bari na faɗa maka a takaice"

MARKE MAY 1990

Tun bayan da ya rakata har motar su ta tashi zuwa Kano, ɓarin zuciya da ke faɗin gaskiya ta addabe shi, surata masa girman laifin da ya aikata musamman na karshen yake, sannan kuma take zuciyar sa ta kwaɗaitu da son gudan jininsa da ke kwance a cikin RAHANATU.

"Ta ina zan fara, in koma on bi ta ne ko, amma duka kuɗin hannu na na bata" Ya faɗi ma kansa. Chan dai ya tashi daga Kasan bishiyar da RAHANATU ta zauna ya yi hanyar hayin su.

"A gaida Hadi Shaiɗan in ka ga Hadi ka ga Shaiɗan! Ni duk garin nan babu matashin da nake kauna kamar ka, kayi mana maganin kafircin malam Tanko" aka faɗi a bayansa, waigowar da zai yi suka yi ido huɗu da liman.

"ka san duk wani ilimi da ba na addini ba haramun ne, sannan ko na addini yarinya ta iya kul huwallahu ya ishe ta ibada. Allah da ya ce wala tabarujjal jahiliyatil ula, Kaga kenan ita mace a bar ta a cikin gida, fita waje sau uku ne a rayuwar ta, in an haife ta a fito da ita limami yayi mata huduba, zuwa gidan miji, daga gidan miji zuwa kabari. In kuwa ba zata je ɗebo ruwa bane wanda a garin nan ai kai sheda ne kafin sallar asuba suke yi.
Toh shi malam Tanko bayan tura ta mace zuwa kafirci, yaki jin shawara haka zata dinga ketare manoma tana tsallake su zuwa makaranta. Garin haka ta ɗauki alhakin ka ta sa sha'awarka ta motsa, an nema maka aurenta yace karatu zata yi. Da Ace zancen cikin nan ya bayyana kafin rasuwar sa sai an yanke masa haddin barin yar sa tayi zina. Ai ka kwantar da hankalinka jihadi kayi, ai abin alfahari ne gare ka ita ke da abin tsiya" kalaman liman suka kara masa wani karfin gwiwa, da tinkaho cewan shi ɗin ya kai har ya isa. A haka ya isa gidansu matan Mahaifin sa suka kara hura masa kai.

SILAR AJALI Donde viven las historias. Descúbrelo ahora