Ba su zame ko ina ba sai gidan Hakimi Alh Yunusa Ladan. Yanayin yanda suka shiga a firgice yasa matan gidan tambayar su ko lafiya.
"ina fa lafiya, yaran nan sun jawo min jangwam" faɗin goggo zufa na keto mata ta ko ina.
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, Salame me ya faru" faɗin Hajiya aziza tana kallon yaran ɗaya bayan ɗaya tana neman gane yanayin da suke ciki. Ko waccensu ɗauke take da firgici a kwayar Idanunta.
"Gamo su kayi da aljani, ina zaune sai gasu da murnar su wai yarinyar nan tayo musu sako daga Saudiyya, in fito in gaisa da mutumin da ya kawo. Ina fitowa sai na iske waje wayam. Wai kuma motar kirin ce ba'a ko ganin shi da abin da ke ciki" Ta karasa tana mai sakin ajiyar zuciya haɗe da mika ma hajiya ledar da suka shigo dashi.
Nan suka zazzage kayan, lesussuka ne da takalma masu kyau. Da yadi na maza masu kyau da tsada. Ledan da aka sa takalman na da tambarin shago a garin jidda. Ajiyar zuciya hajiya Aziza tayi haɗe da murmushi sannan tace;"Wallahi kun ban tsoro, kila cikin sakon ne har da kada ya bari ku haɗu, don duk kayayyakin nan ba na Nijeriya. Sannan shagon nan marigayi Alhajinmu na yawan siyayya a ciki. Ke Salmah ba kuma Mahaifin ku bane"
Shiru tayi tana tunani, ita dai ta san ba zata wani gane mahaifinsu ba, don wasu abin ma yanzu zama da su Ummitr yasa take ganewa. Kenan kila Mahaifin nasu ya saki mahaifiyarsu ne irin na talle yayan ummitr. Tunda ita ma ance shi ya sa ya tafi birni ya barta da yaran ba ko abinci wai tana idda.
"ke Salmah baki ji bane nace ko Mahaifin ku ne? " hajiya ta sake maimaita wa.
" ba shi bane, amma kamar abokinsa ɗan funtua" Ta sami kanta da faɗin haka.
"Ni sai yanzu ma na gane shi" Ta ɗaura ganin duk sun tsare ta da idanu. Hamdala sukayi sannan yaran suka fita zuwa gida yayin da iyayen suka sa Goggo a gaba suna tsokana ganin yanda ta firgice.
Shagon Ado tela aka kai ɗinkin gami da rokon arziki. Haka ya ɗinke kayan tsaf safiyar idi suka samu.
Eid-l-fitr
Bayan mai alfarma sarkin musulmi ya sanar da ganin wata, kofofin rediyo da talabijin suka bada sanarwa, nan aka samu mai shela ya zaga gari yana faɗi.
Murna cike da ɗaukacin musulmin Kasar. Ciki har da al'ummar garin MARKE ciki har da Salmah, Suhayl da Salman.Washe gari da sassafe suka yi wanka. Nan sukayi kwalliya cikin kayan sallan su, Salmah sanye take da bakin leshi, mai jan duwatsu. Kayan ya fito da ita kasancewar ta fara, su salman da Suhayl kuwa yadi suka sanya mai ruwan sararin samaniya, kafin suka ɗauki hanyar masallacin idi.
Salma sai da ta jira Aminanta suka zo sannan suka jera da goggo suna tafe suna kabbarbari. Sun iske ana wa'azi, bayan zuwan limami aka tada sallah. Sannan suka tsaya huduba. A hanyar su na dawowa ne suka ci karo da wasu da salma ba ta san su wanene ba, ganin sun gaisa da goggo yasa suka gaishe su suka matsa gefe suna jiran goggo.
"Wancan mai bakin leshin ce yar wajen RAHANATU?" Ɗaya daga cikin su ta tambaya.
"Eh! Salma kenan sauran yan uwan nata maza ne" goggo ta amsa da murmushi
"ga mutum har mutum amma shege, Au shegun da yawa kenan aka turo miki, aka yi ma hadi kazafi amma da yake ba halinsa bane gashi nan ta haifo ba ɗaya ba, ba biyu ba, Allah kadai yasan yawan su. Kaico" Ta faɗi tana taɓe baki.
Kwaf! Ta ji an make mata baki, ɗagowar da ta yi idanunta ya sauka akan goggo idanunta tamkar gauta.
"kin ci albarkacin yau idi, bazan ɓata ibada ta da nayi kwanaki talatin ina yi ba, amma duk ranar da kika yi gigin kiran jikoki na da kyamataccen suna se na ci ɗammara mun ba hammata iska." Ta faɗi tana karawa gaba tare da su salma duk rayukansu babu dadi.
Bayan tafiyar su mata suka taru suna maida labarin abin da ya faru, masu son a san sun sani suka fara labarin ai karuwanci Rahanatu take a Saudiyya, wasu su ce ai Misra take ba Saudiyya ba.
"Ni sheda ce, Rahanatu aure tayi, don ko da ta bar garin nan Kano ta tafi. Akwai Haroon yaron limamin anguwar mu da abokinsa ya tsinto ta ya ce zai aure ta. Da aka tambaye megida na sai ya faɗa musu ba nutsatsiya bace. Nan ni ma na kara gishiri da magi amma na tozarta tozartawa mafi muni. Domin kuwa mijinta ya same ta cikakkiyar mace, aka yi shagali tun daga ranar matan unguwar suka tsangwame ni. Bamu iya kara wata shida a anguwar ba muka barta tsabagen tsangwama. Naji ance mijin ya tafi karatu Saudiyya ban sani ba ko sun dawo" faɗin tabawa matar me gadi. Nan jikin wasu yayi sanyi yayin da wasu suka fara faɗin ai ta rabu da mijin ne ta fara karuwanci ciki kuwa har da Hajara matar Jamilu kanin Goggo.
Tabawa batayi kasa a gwiwa ba taje ta faɗa ma goggo duk abin da ta sani dangane da zaman Rahanatu a Kano da abubuwan da ya faru a sanin ta da barinsu zuwa Kasar Saudiyya. Goggo tayi murmushin murna don har ga Allah ta fara kokonto kar dai da gaske su Salmah Shegu ne.
***
Tun daga abin da ya faru a masallacin idi gulma ya fara yawo a kauyen marke kan cewa su salma Shegu ne ba ta hanyar aure aka haife su ba. Ba bu halin a gansu da yaran unguwa musamman ma dai salma iyayen zasu fara"kar na sake ganin ki da Shegu, shege ai kwashe albarkan 'ya'ya yake, "
Ko kuma su ce
" kuna biye ta Shegiyar yarinyar nan sai ta raba ku da mazajen aurenku don ita kam babu mai kwasar ta"
Hakan ya kara tada musu da hankali musamman ma goggo, nan kuma ta ɗauki karan tsana ta ɗaura ma
Ku yi min hakuri boko ne wallahi. Ga boko, ga aiki, ga hidiman gida dalilin da ya sa na sauke WhatsApp ɗina kenan amma muna tare anan Insha Allah . Silar Ajali yanzu muka fara, Insha Allah muna tare cike da kauna har karshe... Nagode da kauna...
Don't forget to vote and comment
YOU ARE READING
SILAR AJALI
General FictionDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...