Silar Ajali
Alkalamin SAFIYYAH UMMU-ABDOULBABI NA DAYA
Kwance ta ke kan gadon karfen ta, zuciyarta na bugu fiye da bugun sa, cikinta na murɗa mata tamkar mai shirin gudawa, duk da haka kwakkwaran juyi ma kasa yin shi ta yi, tsoro ne fal a cikin ranta Kasancewar ba ta san abinda daren yau zai zo mata da shi ba .
Da ya ke wata ya kai ashirin da shida, duhun daren ya wuce misali, gari yayi baki kirin ko ganin tafin hannunta bata yi. Sassanyar iskar bazara da ke kaɗawa,da kuma kugin iska da ke tashi daga rassa da bishiyoyin kankarar bai hana zufa keto mata ta koina daga jikin ta ba, sai ma tsoron da ya ke daɗa shiga cikin ran ta don har ganin kamar gilmawar inuwar mutum take hakan ya sa ta kara gimtse idanunta gam, don bata ma son tsautsayi ya sa ta buɗe su. Duk da dai ba ta san takamamman lokaci a yanzu ba, ta san dai akalla karfe ɗaya na dare zai yi.
"Ba shakka ya kusa zuwa, yanzun kuwa zai zo"
Ta faɗa a ranta don kuwa kusan sati daya kenan a jere ya kan zo mata Idan ta na bacci sai dai kawai ta ji hannaye na bin kafar ta ko ma jikin ta, da fari ta yi zaton ko tunanin ta ne ko kuma aikin aljanu ne, sai da ta kama hannu ta rike kamin ta tabbatar da mutum ne ba aljani ba.
Ko da ta fadawa Yagana, wato babbar ɗiyar kanwar mahaifiyar ta wacce ta ke hannun ta, ita kuma ta ba ta shawarar ɗaukar mataki.
Jin kamar an tura kyauran ɗakin, gaban ta ya faɗi , ta yi karfin halin daɗa jawo goran da ta ajiye kusa da ita hannu na rawa, sannan ta yi lamo kamar mai bacci. Kusan minti goma ne ya shuɗe ba tare da ta ji wani abu ba, har ta fara tunanin tsoronta ne kawai, ilai kuwa sai hannu ta ji yana shafar kafar ta, daskarewa tayi a nan wajen don kasa numfashi tayi tsabar firgita, ji ta ke rayuwarta ta zo karshe don duk tattalinta wani na shirin wargaza mata rayuwa duk da karancin shekarunta.
Ta na jin hannun na shafa ta, har aka zo ga cinyarta, ganin hannun na yin gaba-gaba fiye da kullum ya sa ta yi saurin ɗaga sandar ta rantama dai-dai saitin da take tunanin mai hannun na wajan.
Ta ko ci sa'a dan kuwa ihu ta ji an saki, hannun na rawa ta ɗauki fitilar toci ɗin da ta b'oye karkashin matashin kai ta kunna don ta tabbatar da muryar da kunnuwanta suka jiyo mata. Kunnawar da tayi yasa hasken ya garwaya ɓangaren da ta haska cikin ɗakin.
Nan take idanun ta suka sauka a kansa in da ya ke kwance ya na burgima, jini ya wanke fuskar sa sanadiyar fasa masa kai da ta yi. Ganin hasken ya sa shi tashi zai fice a guje.....kan ya kai ga bakin kofa, ya ji muryar ta da ke kakkarwa, cike da mamaki ta ke furta
"Baba.....Baba...Baaaaba"
Dakatawa yayi, sai da yai jim na wasu dakiku kana ya juyo ya na mai watsa ma ta wani irin mugun kallo, nan ta kara tsorata ganin irin raunin da ta ji masa, sannan ya fice da sauri.
Cike da tsoro, ta kasa ko motsa yatsanta balle ta nemi tashi daga inda ta ke dan kuwa sam ba ta yi zato ba, ba ta taɓa tunani ko kawo abin cikin zucuyar ta ba
"Baba! Baba!!!!! Baba fa......."
Abin da ta ke ta maimaitawa cikin zuciyar ta kenan amma kwakwalwarta ta kasa ɗauka, don kuwa idan har Baba zai iya aikata mata wannan mugun aiki haka, toh wa za ta yarda a duniyar nan?
***
Washagari da asubar fari ta ji hayaniyar Baba da Inna, wacce ke cikin ɗanyen jego, hayaniya ce ke tashi daga tsakar gida wanda ya sa Sauran mutanen gidan firfitowa don jin ba'asi da samun rahoton kai wa gaba, abinka da gida ba su kadai ba, gida na haya mai ɗauke da ɓangare ɓangare har goma.
Hakan bai sa Baba ya sassauta ko ma ya dai na kururuwar da kumfar bakin da ya ke ba, Jin ana buga qyauren ɗakin da ta ke, ya sa ta tashi da sauri ta na mai raba idanu.
YOU ARE READING
SILAR AJALI
General FictionDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...