And this is for everyone, I really appreciate you, yes I mean you reading this, I so much love you for the sake of Allah and I pray we become nebors in Aljanna of the highest Rank.
The read and ignore, the read and vote only, the read vote nd comment r d 3 categories of lovers we have in this journey and Alhamdulillah I appreciate, I hop to get more from u guys in our next journey.
Much love
Safiyyah Ummu-Abdoul***
Kwance take kan gadon Rukayya, tun bayan da ta gama shan corn flakes barci ya kwashe ta. Dukan da Zahra ta sakan mata ya tashe ta a firgice.
"Tashi mun shiga uku" nan take barci ya watsake daga idanunta
"me ya fa... ? " bata iya karasawa ba sakamakon ganin hotonta a jarida.
"Na shiga tara ni Salmah me kuma nayi?" Ta faɗi tana rushe wa da kuka. Nan su Rukayya suka shigo suna lallashin ta.
"Salmah satin ki biyu fa anan, duk da yaya Adam ya ce mu ɗan kara hakuri yana neman hanyar fita da ke ne, amma kuma kin san nan ba Nijeriya bace, ko ba komi bizanki ya kare tun da na wata biyu aka baki, sannan gashi kin ɓace, dole hukuma ta shiga ciki ka'in da na'in, yanzu duk ba kuka yakamace mu ba, mu nemi yaya Adam mu faɗa masa halin da ake ciki" faɗin Yakasai.
Hakan ne ya kara musu karfin gwiwa, suka kira shi. Bayan sun kora masa bayani ne yace musu
"Shi yasa nace kada ta fito babu niqab, ina nan ina neman hanya, kun san saboda boko haram sun kai hare hare kauyukan jihar Borno shi yasa aka rufe dukkan bodoji shi yasa ba'a samu shiga da ita ba. Amma bari mu gani, kun san dai in aka kama mu da ita za mu iya rasa gurbin karatun mu ko, don ba karamin criminal case bane, don haka ku yi takatsantsan" Ya gama sannan ya ce a mika ma Salmah wayar itama kwantar mata da hankali yayi sannan ya musu sallama.
***
Murmushin Rashin dalili yake tun da ya ajiye wayar. Ɗaga hannu yayi ya ce"Allahumma zawwijnie Salma bi fadlika ya Arhamar Rahimeen"
"Kai haka manzo SAW ya koyar, maimakon ka yi istikhara ka yi ma kanka zaɓi kenan, wai wace Salmah" Faɗin Ahmad abokin Adam
"Hmmmn Annabi SAW ya ce a ɓoye nema ka bari in na samu sai in bayyana " Ya faɗa shima yana dariya.
" Toh Allah sa ba kaaba zamu je daurin aure ba don in ka ga kare na shinshinar takalmi" shima ya jefe shi da shi
"a'a Jerusalem zamu je" Ya maida masa da bakar magana. Tun daga haka Ahmad ya samu abin tsokana, karshe ma sai da Adam fita yayi ya bar masa dakin.
***
Kwanci Tashi sai da Salmah ta kara wani sati daya da su Zahrah kafin su kayi shahadar kuda suka damfari gidansu.A sati ɗayan Adam ya maida hankali wajen binciken gidan su da kuma mahaifinta anan ya kara tabbatar da gaskiyar labarin da ta basu. Don duk hanyar da za'a bi waje fita da ita ya gagara.
Sai da suka yi sallah isha'i sannan suka tafi zuwa gidan su Salmah. Zaune suka iske dattawan gidan suna hira kamar yanda al'adar su take a gidan. Adam da Ahmad suka fara iske su, bayan sun gaisa ne Adam ya fara magana cikin harshen larabci.
"Ni ne shugaban Ɗaliban Nijeriya da ke jami'ar Afrikiyya. Kwanakin baya mun tsinci wata yarinya, ta kasance cikin rudu, sai jiya da na ga hotonta ana cigiya. A da ce mana tayi ita yar Nijeriya ce, sai a jiyan jiyan ne da muka tsare ta take ce mana dangin mahaifinta na nan, toh yau mun yini muna bincike kafin daga bisani muka gane nan ne. Kuyi hakuri ban bi ta hukuma saboda ba kasancewa na ɗalibi" kankan da kai da zaɓin kalamai da Adam yayi yasa ba wanda ya Musa masa, sai ma godiya da suka yi masa. Sannan aka kira su Salmah kowa sai murna yake, su Zahrah sun ga karamci haka su adam da ke waje. Hira sosai suke da iyayen salma da kakanninta. Garin tambaya da ake musu ne aka gano Adam da Zahra yaran Yayar Haroon Karima ce, yayin da Rukayya er Haroon ce Yakasai kuwa yar kanwar Haroon salima ce. Murna kamar IMRAN zai maida su ciki. Nan ya basu labarin zaman sa gidan su Haroon da kuma yanda Mahaifin Haroon ya tsaya masa har ya samu auren RAHANATU.
Sai faɗi yake
"Jinin Haroon sun min karamci a karo na biyu, ni kuma na damka ma Adam auren Salmah na har abada, don Allah kar ka ci amana kada kace a'a, sannan ka zama Silar dawowan farin cikin Salmah ko bayan bamu"Gurfanawar da Adam yayi cike da farin ciki ya ba kowa mamaki, don mafi akasarin wa'inda ke wajen a tsorace suke kar ya ki karban tayin.
Basu rabu ba sai da Adam ya haɗa IMRAN da Haroon a waya nan abokan biyu suka cika da farin ciki don sun fi karfin shekaru goma sha biyar rabon su da juna, sannan ya faɗa masa alkhairin da yake son kullawa, farin cikin da Haroon yayi baya iya misaltuwa sannan sukayi sallama.
***
A sati ɗaya duk wani cukucuku da Grand khadi Haroon da wasu yan uwan Mahaifin su Adam sunyi don shigowa Kasar sudan. IMRAN na filin jirgin saman Khartoum don bai amince su Haroon su iso su jira ba.
Rungume juna su kayi suna hawayen farin ciki, tun daga filin jirgi har gida hira suke, a gidan ma da kyar suka rabu aka samu Haroon shima ya watsa ruwa kamar sauran abokan tafiyan sa."Wai ni ina RAHANATU ne, ko na ce Rayhan ɗinka tun da muka zo amarya kawai muka gani" Haroon ya tambaya bayan sun gama cin abinci.
Hakan yasa Imran ya kwashe duka abin da ya faru tun zuwa su Sudan har rabuwar su, da yanda Salmah ta dawo hannun shi har auren da ya mata da rabuwar duk bai ɓoye ba.
"lallai a rayuwar ku akwai darasi babba, ni daga kai har Rayhan din ban ga wanda yafi wani son kai ba, ita zan kara da cewa ilimin ta bai amfane ta ba don ko zamanin jahiliyyar farko ba'a yi abin da ta yi ba. Amma duk wanda ya ce duniya ne akan gaba, ko yace ba zai yafe laifin da aka masa ba, ko ya ce shi don wani abin da ba'a so ya same shi Shike nan ko oho ko da sauran mutane zasu mutu toh tabbas yana tare da wahala. Amma da yake haka kaddarar ku yazo, sai mu yi fatan Allah ya yafe muku da mu duka ya raya zuria"
"Aameen ya rabbi Haroon, Allah ya bar mu tare har gaban abada har a Aljanna "
" Aameen ya rabbi aboki na" Ya faɗi shima yana dariya.
***
"Kin san tun yaushe na ke son ki? Tun ranar da na fara kyalla ido a kan ki, kishin ki ya taso min don a tunani na kina cikin masu haurawa Saudiyya, Salmah ki amince da ni mu gina rayuwa mai inganci" Ya faɗi yana kallon ta so yake su haɗa ido amma taki, kunya duk ya rufe ta."Kinga in muka yi aure farkon abin da zan yi shi ne nema miki gurbin karatu ki karanci shari'a, ni kuma Kinga zuwa lokacin na ɗaura doctora (phd) zamu kammala a kusan tare, sai mu koma Nijeriya mu cigaba da rayuwa " ita de kallon shi kawai take, chan dai ya sake cewa
" ni fa tun da na fara sonki na fara mana wannan Mafarkin "
Dariyar da Salmah ta saki ne ya tsaida masa zancen sa. Amma a hakikanin gaskiya jin zancen take kamar ana shuka irin sonsa ne a zuciyar ta. A take kuma yana tsirowa kuma yana rassa da yabanya ta ko ina.
" Kullum ki dinga mana addu'a kinji, Allah ya cigaba da haɗa zukatanmu yasa mu zama maaurata a gidan aljanna " Ya faɗa mata cikin rada. Dariya kawai tayi haɗe da rufe idanu.
YOU ARE READING
SILAR AJALI
General FictionDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...