Babi Na Goma Sha Biyu

1.7K 256 66
                                    

Cikin nasara suka isa birnin Yambu, (yambus sana'iyyah) cikin ikon Allah bata kara sati ɗaya ba ta samu makarantar kulliya. Duk da ta ɗan samu matsala da farko amma da jajircewa da naci sai gata tana fahimtar karatun sosai.

Sannu a hankali ta fara wayewa,  nan ta gano da yawa daga cikin abubuwa da malaman ta na islamiyya ke faɗa musu na biyayya ga miji al'ada ce ba addini bane, kuma sun ci karo da addini  musamman ta fannin saɓa ma Allah don a faranta ran miji. Nan fa ta gane aure ibada ce,  bautar Allah ce ba bautan miji ba,  an shar'anta ma mace yin ma miji biyayya ne matukar ba wajen saɓon Allah ba ne.  Sannan mata ma na da hakki akan mazajensu kamar yanda maza ke da hakki akan su.  Duk ta zauna sai tausayin yan uwanta mata da ke Afirika ya cika mata kai don ana cutar su da sunan Musulunci,  ana tauye musu hakkin da musulunci ya basu a hana masu neman ilimi don kar su san musulunci yayi su yan gata ai ta azabtar da su. 

Ranar da aka koyar da su Darajan mata a musulunci na cikin ranakun da tai kwanan zubar kwalla.  Don ko ita ta kasance cikin wa'inda rashin karatun addini ko Ace juya al'ada zuwa addini ya shafa.  Hadi ya mata fyaɗe,  ga laifin zina akansa ga na fyaɗe amma duk aka barshi ya sha don shi ne mutum ita mace ba mutum bace. Tunanin girman Manzo SAW take da yanda yake shawara da mata kafin ya aiwatar wasu ayyuka nashi ciki kuwa har da abin da ya shafi jihadi. Ta kara auna darajar annabi,  taga ba'a yi ba kuma baza ayi wanda ya kamo kafarsa a daraja ba amma duk da haka yana shawara da matayensa ai sai ta ga lallai ko dai mazan Afirka basu da ilimin addini ko suna take sani wajen ba mata addininsu abin takaicin ma juya shi zuwa musulunci ya ce da suke yi.

Ko da aka taɓo rayuwar mata sahabbai sai ta ga matan Afirika na kokarin kwatanta  biyayya ga miji sai dai garin son mallakar miji sai suka saka gaggawa a ciki hakan ya sa suka fara biyan yan 419 da sunan malamai wajen neman biyan bukata. Sukan manta addu'a da ibada a lokutan jin Daɗi sai matsalar aure ya taso su sai su fara biyan bokaye da yan bori suna neman taimako su kuma su damfare su.

Haka dai tayi ta fahimtar abubuwa tana kara samun ilimi, nan rayuwar su ta kasance abin sha'awa abin jin Daɗi,  sukan yi duk wani nau'i na ibada don tsira tare gobe giyama. 
                            ***
Tana ajin karshe kulliya ta samu juna biyu,  murna wajen su ba'a cewa komi.  A shekaran ne kuma Iran ya samu aiki a jami'ar Tabouk. Ba tare da ɓata lokaci ba suka sake yin ighama suka koma can da zama.

Bayan wata tara ta haifi ɗan ta santalele mai kama da Ubansa, nan suka raɗa masa suna Salman.  Rainon Salman ya jinkirta mata komawa makaranta don ta so komawa ta haɗa digiri ɗinta.  Tana yaye Salman kuma ta sake samun wani cikin wanda ta haifi ya mace mai kama da ita. Wacce ta ci suna Salmah

Tun bayan haihuwar Salmah bata sake daukar ciki ba sai da Salmah ta yi shekara biyar  duniya.  Cikin sai ya zo mata da kasala da rashin son wanka.  Kasancewar wannan ne na farko da ya zo mata da matsala sai ta saki jiki maimakon ta daure ta dinga gyara.  Kafin a ce me ta zama kazama ta ajin farko.  Daga haka Imran ya dena zama gida,  ya fara kula mata tukari musamman yan Kasar Ethiopia da abin da ya kai su kenan.

Wasa-wasa y daina kula da hatta abincin da zasu ci. Sai da yake ta samu karantar da yaran shugaban jami'ar (lesson tutor)  sai take amfani dashi wajen kula dasu.

A tunanin ta bayan ta haihu abin zai canza amma ina ko bayan haihuwar Suhayl ba abin da ya chanza sai ma karuwa da yayi. Kullum addu'a take yi amma hakan bai chanza ba, anan ne ta shirya zuwa umra don ta kara rokon Allah ya shirya mata mijinta,  don lokacin kawo wata gidan yayi ya ajiye kamar matarsa kuma tana buɗe baki tayi magana zai ce in bazata iya zama ba ta tafi.

A wajen ɗawafi ne ta haɗu da Amina da mijinta wani ɗan majalisa ya biya musu. Tayi murna kwarai da gaske,  sun yi hira sosai na bayan saduwa sannan suka rabu bayan ta amshi lambar teleho din makotarsu amina.

Ganin abin na shi ba na karewa bane  bayan ta yaye Suhayl har ya shekara uku ya sa ta kira Amina ta tambaye ta ko zata iya rike mata Yaranta.  Ta ɓoye mata halin da suke ciki sai ce mata tayi rayuwar Saudiyya da tsada. Amina na amincewa kuwa ta shirya musu tafiya ba tare da Imran ya sani ba.  Ba shi ya ankara da rashin su ba sai da sukayi wata huɗu a Nijeriya. Nan ya sa mata bala'i da masifa akan sai ta bar masa gida ta nemo masa yaransa.  Ta na faɗa ma matar shugaban makarantar aka sama mata boys quarters take zaune da gurbin karatu a jami'ar.

                          ***

"Hmmmn!  Tayi ajiyar zuciya bayan ta gama tunanin rayuwar ta.

"gida zani,  in na je su kashe ni" Ta faɗi tana mai mike wa daga kwanciyar da tayi.

Here we go peepz.. 

Rate Silar Ajali from 1-5 let's c our matsayi...

Wish me luck,  collected my MSc admission 2day.

SILAR AJALI Where stories live. Discover now