Zata tada sallah kenan taji motsi a bayan ta, a firgice ta juya don bata san ko waye ba, ido biyu tayi da wanda ko gawar sa bata kaunar gani nan take ta gimtse fuska, duk wani tsoro ya kau ta tsare shi da kallo
"ke banza ce Wallahi, zuwa nayi in taimaka miki da wajen zuwa, kar kiyi gigin komawa gida don hukuncin kisa za'a yanke miki in ji liman. Wai kin kashe tsohonki"
Ko ɗar bata ji ba don limamin da ta gani yau ko feɗe ta aka ce ze yi ba za tayi mamaki ba. Kallon mai maganar take bata ce komai ba, can ta juya ta sallaci rakaa biyu. Har ta idar yana zaune a gefe duk da haka ba ta ce dashi komi ba.
"Ga wannan, ki rike a hannun ki ya ishe ki yin komi, ni ma jiya da su baffa suka je Katsina ganin sarki ne ya basu ni kuma na ɗauko yanzu da suka nufo wajen jana'iza." Ya karasa yana mai mika mata rafar naira ashirin.
Kallon shi take ba tare da ta mika hannu ta karɓa ba, ita tun da take kuɗi mafi daraja da ta rike shine naira biyar, amma Ace wai ita ce ake ba naira ashirin ba guda ɗaya ba, bandir abinda take tunanin ko mahaifinta bai taɓa rikewa ba. Bata ankara ba ta ji mutum a jikinta la lulubenta yake ta ko ina.
"kiyi hakuri sau ɗaya kawai zan miki, ɗanɗanonki ne akwai garɗi da tsayawa a zuciya. Zan kaiki har kasuwar gabashi in sa ki a mota" Ya faɗi cikin raɗa. Karfinta ta sa ta tura shi amma ina ko motsi bai ba. Haka tana ji tana gani sake bin hanyar da ba nashi ba. Bata iya komai ba sai hawaye da kunar zuciya. Da ya samu natsuwa haka ya sa ta a kariyan kekensa da bata san ya zo da ita ba ya ɗau hanyar kasuwan gabashi. Cikin ikon Allah motar Fijo J5 ta cika saura fasinja ɗaya ta shiga ba tare da tasan inda motar zata nufa ba.
"in namiji ne ki sa masa Hadi masoyi in mace ce kisa mata raha masoyiya. So ya sa aka same su hahahhahaha" Ya karasa yana dariya bayan ya mata raɗa ne a kunne.
Haka sukai ta tafiya, banda kuka babu abinda ta ke yi, wata mata kusan Saar goggonta ce zaune kusa da ita. Ganin kukan yai mata yawa ne ta ce
"baiwar Allah kiyi hakuri, komi na duniyar ma ai ɗan hakuri ne, wajen wa zaki je a birnin Kano" Ta faɗi tana kallonta, ilai kuwa ta hango firgici sosai a idanunta."gudowa kika yi " Ta faɗi cikin raɗa ganin firgicin da ke idanun RAHANATU.
Girgiza kai tayi, hakan yasa matar tayi shiru gudun kada ta jawo hankalin mutanen cikin motar. Haka sukai ta tafiya za'a ba za'a ba har suka isa garin Kano karfe goma na dare. Matar bata ɓata lokaci ba ta shawo kan RAHANATU zuwa gidanta. Sai washe gari bayan sun ci sun koshi sun huta sannan ta bukaci jin abin da ya fito da ita daga gida. Bata ɓoye mata komi ba ta faɗa mata komi dangane da ita, ko da ta gama dukkansu hawaye suke yi.
"RAHANATU zan saki a hanyar da zakiyi kuɗi amma fa sai in zaki yarda a cire cikin jikinki. In an cire sai ki koma makaranta daga nan har Allah ya kawo mai son ki. Kar kiji tsoro, ki saki jiki guminki zaki nema, ga ki da kyau da kira mai ɗaukan hankali. Kinga zaki yi kasuwa ba ko kaɗan ba".
Manage this short chappy...
Insha Allahu Anjima I will come with a long chapter nine. Se mun kai karshen RAHANATU bi izinillah.Thnx for sticking around. Much luv
![](https://img.wattpad.com/cover/96511005-288-k419738.jpg)
STAI LEGGENDO
SILAR AJALI
Narrativa generaleDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...