Shiru duk su ka yi na wasu yan lokuta kamin bisani malam ya ce,
"Salmah ina iyayen ki?"
"mamanmu na Kasar Saudiyya, tare da Mahaifin mu. Na san dai ya taɓa tafiya aka ce ya je Sudan wajen yan uwansa. Mun dawo Nijeriya ina da shekara shida yanzu Kaga ina sha biyu, tun lokacin ban sake ganin su ba. " Ta karasa tana shassheka.
" gidan wa kike zaune anan,? "
" Wajen Goggo Salame, itama yau kwanar mu uku da dawowa wajenta. Da muna Kano ne wajen inna Amina" Jin hakan ya sa hankalinsa tashi. "tabbas idanunsu iri ɗaya ne, kai akwai kamanni ya akayi ban gane ba tun ɗazu" zuciyar sa ta faɗa masa.
"Ya sunan mahaifiyarki? "
" RAHANATU "
" what! Ya faɗi da karfi har sai da suka ɗan firgita.
Nan kuma sai ya ɗan waye ya kakalo murmushi wanda iyakarta fatar bakinsa. Sannan yace
"tare muka fara karatu, sai dai a gabanta nake, ki yi kokarin koyi dahalayenta don kuwa ita ɗin ta gari ce, ki kwantar da hankalinki babu inda za'a kaiki, tun da kika ga goggo ta kawo ki makarantar nan toh ina mai tabbatar miki da ba zata bari a kaiki ko ina ba.
Abu na gaba da zan faɗa muku shine ku sani aure ba shi ne karshen duniya ba, kai shi ne Mafarin mafarki, sa ma rai jin Daɗi ne kawai a aure shi ke sa mata shagaltar da rayuwar su wajen faranta ma ɗa namiji. Garin haka har su faɗa ma halaka walau bin bokaye ko wani abin.
Kunga karatu, yana da matukar mahimmanci a aure, in kina da ilimi kina aiki zaki taimaka ma al'umma, kai ko bakya aiki zaki taimaka wajen koyar da yaranki, hakan ba karamin daraja zaki samu ba a idon mijinki, se kiga bai iya wulakanta ki ba. Saboda haka ku sa ma ranku karatu baya hana aure, haka aure baya hana karatu. Duk su biyun manzo SAW ya umurce mu da muyi.
Idan Allah bai nufe ku da karatun, kun san dai kowa da kaddararsa, toh ku tabbata kun dogara da kanku, ku kama sana'a ko da ace riban da zaku samu kaɗan ne, sau da yawa bani bani ke kawo matsala a gidan aure. Amman in kun yi karatu ko kun rike sana'a ba zaku samu wani matsala sosai ba.
Abu na karshe shine akan laifin da kukayi, in har mutum na neman albarka a karatunsa toh dole ya kasance mai girmama malamansa. Ba ku ji hausawa na faɗin malami yafi uba ba, ko harafi A mutum ya koyar da kai ya cancanci darajawa da girmamawa. Hakan zai sa mutum ya kasance mai nasara. Ku je Allah ya muku albarka"
Jiki a sanyaye suka kama hanyar ajinsu, basu taɓa zaton zai kyale su haka ba tare da ya zane su ba. Suna kauce ma ganinsa ummita ta fara dariya, nan suka tsaya kallonta.
"kun lura da yanda malam ya bi salma da ido kuwa, anya ba saurayin mama Rahanatu bane don tun da ta ambata ya shiga wani yanayi" Ta kara sa dariya aiko salma ta kai mata duka ta goce, nan fa suka fara ma juna dariya.
"Jiddo ke Wallahi son aurenki da yawa yike, ni wallahi da za'a barni ai sai na kammala zanyi aure Wallahi " faɗin Rufaida
" ke dilla aure daɗi ne dashi Wallahi, bari Ado ya kawo min wayata, zaki ga bidiyon da ya ce zai saka min. In ya zo zance wani lokaci yana nuna min Wallahi nan sai in fara jin lema lema kamar nai fitsari, yace min kaɗan kenan daga cikin daɗin. " Ta faɗi tana juya idanu.
" ku mu shige kangon can ki bamu labari, ance soyayya daɗi gare shi. Ni don kawai ina son zama likita ne kuma ance wanda ya fara baya iya karatu. " faɗin ummita. Salma kuwa kallonsu ta tsaya yi don ita tun da take bata taɓa kawo soyayya nan wuri ba, Kano da ta baro duk saointa karatu suke yi sai an gama candy ake aure. Haka dai ta bi su zuwa kangon suka zauna sannan Jiddo ta ɗaura.
" Kunga ya ce in mukai aure, akwai abinda zai dinga saka min sai na suma don daɗi, wai kamar Susan kunne. Sannan akwai inda yake tattaɓa min nake jin Daɗi, amma fa amana fa, kar ku faɗa ma kowa Kunga dai ku yan uwa na ne, ke kuma salma aminiyar mu ce." Ta karasa tana mai mikewa saboda hango discipline masta ya damfara wajen. A guje suka wuce aji aka cigaba da darussa har aka tashi.
***
Bayan sun koma gida abinci suka ci suka huta, bayan la'asar suka kama hanyar islamiyya, suna gab da barin gidan suka haɗu da hakimi, zai shiga wajen goggo. Salma da ta san ajiyar su a kanta da yan uwanta ta tsorata ainun. Amma dai bata ce komi ba, bayan sun gaida su ne Ya shige cikin gidan"Zan fi so ace ka aika kira na ne da ka taso zuwa gareni. Ai karami ke bin babba koda yaushe" Goggo ta faɗi tana mai Shimfiɗa masa tabarma.
"Mahimmancin maganar ya sa bana kyashin biyo ki. Akan zancen yaran nan ne, na amince ki rike su, duk wani taimako in bai fi karfi na ba zan baki" Ya faɗa yana murmushi a tunaninsa ya yi a bin kirki.
"Yaya amma da mai sa ka ce a kai su gidan marayu? Ni fa har na shirya kayana don na gwammace in bar garin da a sa ni a faifai, amma ganin zaka ba da naka gudunmuwan yanzu na faɗa maka, amma niyyata ko sallama bazan muku ba" tace a hankali amma daga jin kalaman ta an san wacce ta ke cike da fushi ne.
"kiyi hakuri, Shaiɗan ne ya so shiga tsakanin mu, amma Insha Allah ya sa yanzu duk abinda zasu nema na fanin Uba zan yi musu. Fata dai Allah shi raya mana". A haka suka zauna hiran zumunci har sai da aka kira sallan magriba bayan su salma sun dawo sannan ya tafi.
Here we go dear ones, and ol what jiddo said was said by a jss 1 student in the school I teach. In fact I have to remove some things to cut it short.
Wallahi the girl is use to sex, we caught her watching bf with some students with her rakani toilet fone.
Dear parent make una keep eyes on your children ooo. Teach them sex education before they get exposed to pornography.
Dear big sister, pls b good example to your younger ones. B sure u serve as a good example so dat you will b able to correct them.
Tell us ur experience.
One love
Ummu-Abdoul
VOCÊ ESTÁ LENDO
SILAR AJALI
Ficção GeralDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...