Hankalin Goggo ya kai kololuwa wajen tashi, juyi take kan gado idanunta babu ko alamun barci. Ta saka wannan ta kwance, duk hankalin ta bai kawo mata mafita ba. A iya sanin ta ba za ta yarda a kai jininta gidan marayu ba amma kuma in aka kore ta ina zata nufa da yara ita ba wata sana'a take kwakkwara ba. Haka dai ta kasance har sai da kiran assalatu ya fargar da ita lokacin da ta Share kwance.
Tashin Salma da ke kwance a gefen ta ya dawo mata da dukkan bakin cikin da take tunanin babu a lokacin. Kallon ta tayi, ta gama addu'ar tashi da ga barci ta Mike nan take wata irin tsanarta ta dake ta, "yanzu ita ma ɗin ba tsira tayi ba da ga jan abin kunya, mata ko tsiya" ta faɗi a ranta."kawai ki ba da ita a gidan marayu ki huta da abin bakin cikin da zata iya Kwaso miki" wani sashi na zuciyar ta ke shawartan ta, kafin ta kai ga amincewa Ɗayan sashin tace da ita
"Me zaki ce da Allah yayin da ya tambaye ki dangane da amanar kiwon da ya baki. Ki haɗe su ki rike duk rikicin da za'a yi" batai wata wata ba ta amince da shawarar. Da wannan karfin gwiwa ta tashi ta ɗauro alwala ta gabatar da sallan asuba.
***
Ko da hakimi ya isa gida ya taradda hajiya Aziza a turakansa. Sanye take da rigar barci doguwa, kanta babu ɗankwali kitsonta ya kwanta gunin sha'awa, nan take ya fara jin abu tun daga tafin kafarsa har kwanya. Zuciyarsa na kara narke mata, "Daɗi na da ke kenan sanin ciwon kai" ya faɗi a ransa bai tsaya ɓata lokaci ba ya dumfare ta ya rungumo."Kinyi kyau hajiya ta, always looking sweet my dearest " ya faɗi a saitin kunnen ta, nan take abubuwa suka dawo masu a rai, rayuwar su na jin Daɗi sanda yake aiki karkashin mahaifinta.
" tunanin me kake yi bayan ga azizarka a tare da kai? " ta faɗi tana dariya kasa kasa.
" Tunawa nayi da kuruciyar mu, hakika da duk haka mata suke da sai in ce ba za'a samu yawan mace macen aure ba ko zaman ukuba a aure, Allah ya sada ki da aljanna yanda kika zama sanadin wayar dani cewa mata ma mutane ne da suke da hakki a aure kamar maza" ya faɗi yana shafo kitso ta.
"ai da sauran ka yallaɓai, ba zamu gaji da magana ba don muna fatan samun nasara da canji yayin magana, wasu na tsoron saki sai suka ki magana hakan ya sa suke zaune cikin ukuba"
"Maama me yayi saura bayan ina iya kokari wajen ganin na kyautata muku. Ko halinku na yan boko zaki nuna min. " ya karasa yana murmushi don ya san abin da ya tono.
" Ai tsiyar yan Afirka kenan, ba dama ace kar a muzguna ma mace sai kuce boko, alhali musulunci ya koyar da mu haka. Zancen yaran RAHANATU ne, shin da ace Batul ce ta wajen mu wannan al'amari ya same ta haka zaka aiwatar? Dazu na ji zancen ku da wancan jahilin, wanda ya ki karatun arabi balle a sa ran zai yi boko. Wallahi kuna kai yaran nan gidan marayu zan haɗa ku da hukuma. Sannan ka san cewa na bar gidan nan kenan"
"tsaya Azizah, kin sha wani abin ne da daddaren nan da zaki haɗa Batul da Rahane, bazan taɓa haɗa jini da shegu ba don ni tsarkakakke ne haka duka mata na" ya faɗi yana kumfar baki. Sanin da tayi zai ji haushi sai ta saki ranta ta yi dariya sannan tace
"Meye bambanci tsakanin su biyun? Duk su biyu yaranka ne ko Kaki ko kaso, sannan ai ita dole aka mata, amma ina ce nan ka sa Sanah komawa gidan Nasiru Nasiru, duk da cewa da ake ɗan luwaɗi ne? Da wanda aka ma fyaɗe da wanda ke aikata luwaɗi Wanne ya fi? Sannan ita dai aure tayi ta haife su, ga yarka chan ka Barta a auren da wuta zai kaita saboda tsinuwar Allah da yake kansu. Duk mijin da yayi luwaɗi ai zai yi da matarsa" nan hakimi ya cika yana batsewa.
"ke dai baki da magana sai ta saki, yanzu duk kokarin amso taimako da nake yi daga wajen malamai baki gani ba, mai gani har hanji yace ayi hakuri zai daina" ya faɗi a iya kan gaskiyarsa kenan.
"tab, ga shirka ga luɗu Allah ya shirye ku. Duk auren da zai kai mace ko yan uwanta gidan boka Wallahi ba aure bane. Ni dai na gama magana kuka kuskura kuka kori yaran nan Wallahi hukuma zasu shigo ciki. Haba Allah ya ɗaura muku hakki ku nemi watsarwa, na barka lafiya" ta tashi ta barshi zaune. Ta san ba zai juri fushinta ba shi yasa ba ta kyashin nuna fushinta a kansa.
***
Tun da ta tafi yake tunanin abin da ya faru da yar sa Sanah.
SATI BIYU DA SUKA GABATA
Ya shigo gida ya iske yarsa da ke aure a ɗan Musa ta dawo gida. Da fari yayi tunanin ziyara ta kawo masu sai da Hajiya Aziza ta masa bayanin kara Sanah ta kawo.
"Kowa fa hakuri yake a gidan miji shin ba zaku faɗa mata hakan ba, ni ba abin da zan ce illa kar ta soma kashe aurenta. Uwar ta ma hakuri take da ni" ya fadi a fusace, nan take ta mayar masa da cewa
"neman ta fa yake ta baya, sannan kace kar ta dawo, cewa a kayi in an aurar da mace Shike nan bata da hakki akan ubanta ? Ko mai kake nufi "?
" Akan ta aka fara auren ɗan luwaɗi ko cewa akai su sauran basu da mata, kar ki kashe mata aure ko don ba ke kika haife ta ba" ya bata amsa
"don ba ni na haife taba sai in bari tayi ta kwasar tsinuwar Allah da sunan aure, aure fa ibada ce, kuma ibada sai da biyayya ga Allah ba saɓon sa ba. Haba" tana gama faɗi ta barshi a zaune.
Haka tana kuka da magiya ya tasa keyarta har zuwa dakin ta. Ta kira shi sau biyu tana rokon sa shi kuma yai mirsisi , chan ne abokin sa ya shawarce shi da su nema mata taimako daga malamai.
Da tunanin nan barci mai nauyi yai gaba da shi har sai da aka kira assalatu sannan ya tashi yai harama.
Gbagam Gbagam!
Sowie for D late update, I lost 200k words unsaved and u knw now Nepa pple r doing us yanga.. Insha Allah I will have a long seaster so Dat I will typ @ night...
Acknowledge Pls with a simple votes and comments.
Thnx alot for the previous, u make me feel loved and honored.
Jazakumullahu bi ahsani jazaihi..
Loving you
Ummu-Abdoul
YOU ARE READING
SILAR AJALI
General FictionDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...