Silar Ajali 2....
Assalamu Alaikum warahmatullah sweetiesssss. Dafatan kuna lafiya, so sorry for d late update. Things r though here daz y. Amma Insha Allahu zan kokarta yi muku wani gobe. Pls Vote and comment. Am not happy with the low votes Recieved Abeg danna tauraro, sannan shiga akwatin faɗin ra'ayi ki rattabo mana naki..
With much love
Ummu-Abdoul"kin wani tasa ta gaba kina kuka, bari in je in dawo mu tafi Salmah" Ya karasa yana mai kallon Salmah bayan ya jefi Inna da harara
"ina zamu je ne Abba" Ta faɗi tana share kwallar da ya ciko idanunta"gidan mahaukata na dorayi zan kaiki, su rike ki kar muje wataran kiyi inda bazamu kara ganinki ba" Ya faɗa a tausashe yana shirin fita ne ta ce
" Abba dan Allah to zaka kaini boarding school in karasa karatuna in mun dawo daga ɗorayin" kawai ya zuba mata ido, idonsa rau-rau kamar mai shirin fashewa da kuka, sai ya fice ba tare da cewa uffan ba. Inna kuwa kasa kunshe kukanta tayi.Nan take Salmah tace "inna ki daina kuka ki sa min buttermint da madara mutafi" kasancewar ta da son buttermint. Tun lokacin kuka take har Abba ya dawo ya sanar mata za shi Kaduna wani taron gaggawa, amma kaninsa Gambo da dan sa Mahmood zasu kai ta.
***
Wajajen karfe biyu na ran ne suka iso don tafiya da ita. Rungume ta tsam inna tayi tana kuka, tana jin zafin abin da mijinta da dangin sa suke shirin yi. Take ta ji ta tsani RAHANATU, ace ka haifi ɗa ka watsar, duk da kwanaki a shirin Darajan mata da ke zuwa a rediyon firidom anyi hira da kungiyar sccvolunteers masu rajin kare hakkin mutane daga kowani irin cuta sun ce"yayin da akayi ma yar ku fyade, saurin aurar da ita ba shi ne mafita ba saboda akwai wani radadi da suke rayuwa dashi. In an san wanda ya aikata mika shi ga hukuma shine abin yi don kare wasu da ga shiga tarkon shi, sai a kai yarinyar asibiti don nema mata magani. Ba wai maganin jikinta kawai ba har da na kwakwalwanta domin fyade kan zare ma wanda aka yi ma sinadarin tausayi, yana busar masu da zukatansu hakan zai sa su kasance masu kafiya, da son kansu da yawa..... " ranar hawaye ta yini tana yi tana sauraron shirin. Ta so ace mutane zasu dinga damuwa da halin da Yaransu ke ciki yayin da aka musu fyade, don iyaye damuwar su kawai su aurar da su kar ta jawo masu abin kunya.
" Allah na tare da ke Salmah, Kije zai kare ki kinji, ga buttermint ɗinki, zan dinga zuwa duba ki kullum" Ta karasa tana kuka, a haka suka rabu dukkan su shaɓe shaɓe da hawaye
***
Da isarsu asibitin ofishin shugaban asibitin suka isa kamar yanda Abba ya umurce su, bayan sun masa bayani, kallon Salmah yayi da ga sama har kasa sannan yace "ita ce Sani yace ku kawo min kuwa?" Ya tambaye su cike takaici"Eh itace" faɗin Mahmood
" Wallahi bazan kar6i yarinyar nan ba, wannan wane irin rashin tausayine, ba ku san zama da mahaukaci yana maida mutum irinsu ba" Ya faɗa s fusace
Bai kara cewa komi ba ya sa waya ya kira Abba,
"Dr taimaka ka amshe ta yanda na faɗa maka, zan zo in karbe ta in lokaci yayi" Ya tare shi kafin ya masa wani maganar. Jiki a sanyaye ya sauke wayar, Ya Kalle ta yace "kina son zama anan ?"Na daga masa kai kawai tayi, haka kawai ta ga ya kama kwalla yana fadin "Wallahi da 'yata ce bazan iya mata haka ba" Ya faɗi yana Share kwalla, Salmah kuwa zuciyarta ya bushe ba ta ko damu da kwallar da su ke yi ba, kara rikon jakar buttermint dinta ta yi kamar kwace mata za'a yi.
Sakatarensa ya sa ya kira masa wata likita mai suna Aisha, bayan ta gurfana a gaban shi ne yace
" dauketa amman karki hadata da sauran mahaukata, zai kyautu ki barta a wajenki har na zo.
Maimakon su fita sai ta fara auna ta haɗe da mata wasu yan tambayoyi, nan ta hasala tana kunci ta ce "ciwon yarinyar nan in ma da shi bana asibiti bane" nan kowa ya msta shiru, ganin haka ta ce salma ta bi ta su je.
Da suka fita ne ta tambaye ta "dama an taba kaiki ne, ko nan aka fara zuwa da ke"
YOU ARE READING
SILAR AJALI
General FictionDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...