Babi Na Ashirin Da Takwas

1.5K 151 57
                                    

This chappy is urs Rukayya, zahra, miss yakasai and all other Nigerian students studying in Sudan and are part of our journey. Allah ya baku sa'ar karatu ya tsare mana ku ya sa ku dawo cikin nasara.

2 more chapters to go Insha'Allah. In ban cinye Charji ba in turo muku Anjima if not d 2 gobe insha Allah.

Thank you all for being part of  Silar Ajali, love u so much for d sake of Allah..

Ummu-Abdoul

Instagram @ua_author

Tun da ta fara gudu bata sanin in da take sauke kafafu ita de fatan tsira take. Hangen cincirindon mutane a inda ke nuni da bakin titi yasa ta fara tafiya tana haki har kai ga wani dogon gini ta jingina. Nan ta ankara ba takalmi a kafafun ta ga shi duk taji ciwo. Tashi tayi da niyar dumfarar mutanen ko za'a samu wanda zai taimaka mata. Duk da kasancewar zuciyar ta na kidan lugude bata fasa zuwa ba. Ɗaga kan da za ta yi  bayan ta kawo karshen ginin kuma bakin titi sai ganin rubutun kofar gate din wajen yasa ta gane makaranta ce take ta karance su da boko da larabci duk a bayyane

International University of Africa 
(جامعة افريقيا العالمية‎‎) "
Hakan ya kara mata kwarin gwiwa har ta isa gare su.

   " Ku taimaka min! Help me please! Agithnie!" Haka dai ta ke faɗa cikin shesshekan kuka tana hargitsa yaruka ukun, duk da bakin ta bai goge da larabci ba. Kallon sabon kamu ake mata har dai wani yayi kokarin tunkarar ta yace

"zo baiwar Allah " Ya fadi yana yafito ta.

Ta isa gareshi bakin ta na ambatar addu'a.

" Daga ina kike, me ya same ki?" Ya faɗi yana son tantance lafiyar ta.

"suna na Salmah, daga Kano nazo ganin mahaifi na sai wani ya sace ni shi ne na gudo na ɓullo ta nan" ta karasa cikin kuka.

"bari na kaiki wajen shugaban daliban Najeriya, kinga bakano ne, kila da taimakon da zai miki. Share halayenki, nima dan Nijeriya ne, amma dan yobe ne" Ya karasa fuskansa yalwace da murmushi.

Wani ni'ima ya ziyarci zuciyar ta a hankali ya fara wanke tsoron da ya mamaye zuciyar. Binsa take cikin sauri har suka kawo wani gini da taga an rubuta "Nigerian students union secretariat"  bayan sun yi sallama suka shiga ne mutumin da ta biyo ya kalli wani yace

"Ya Naqib, ga yar uwa na kawo maka, yar garinku ce ta ɓace"

"kace masu neman abin duniya, zaku haura Saudiyya ko, ke ma a dole se kin zama hajiya Kano to jidda ko" Ya fadi yana mai watsa mata wulakantaccen kallo. Hakan ya tsurar da ita, kuka ta saki tana fadin

"Wallahi na zo ganin mahaifi na ne shi ne aka sace ni, ka taimaka ka maida ni  Kano mahaifiyata da  yan uwa na duk suna can" Ta karasa tana kama kafafunsa. Janye wa yayi da sauri, waya ya dauko ya danna ya kara a kunne, bata ji abin da yace ba ta dai ga wata sa bata wuce sa'ar ta ba tazo.

"Zahra ki je da wannan, tayi wanka ta huta zuwa gobe Insha'Allah sai mu ji daga gareta. In muka same ta da karya mu mika ta da hukuma.

A tsorace take, haka suka fita zuciyar ta na bugawa har zuwa dakunan kwanan da Ɗalibai. Bayan tayi wanka suka zubo mata  fara da mai haɗe da salak, Haba take ta manta wani tsoro ta far ma abincin.

SILAR AJALI Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin