LAIFIN WAYE?? (Page 1-32)

1K 31 10
                                    

[7:20pm, 3/30/2017] Hamagee: 💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*Marriage is that relation between man and woman in which tha Independence is Equal,the Dependence mutual and tha Obligation Reciprocal".* *Best wishes for Happy Wedding Anniversary..* *May the love that you share lasts a lifetime and may you accomplish all the dreams that you have entwined together!*
*A very happy Wedding Anniversary to a wonderful couple!* *@ _sweety Billy Galadanci aka Mom Nu'aim_,Luv u loads sweethrt...* *This page goes to you* 🙌🏽

💦💦

Page 01
Wata budurwa ceh zaune kan dressing mirror tana tsara kwalliya kamar me zuwa gasar sarauniya,kyakykyawa ceh bata wasa ba,wanda kyan nata ya dace da sunanta wato *Suhana*.Suhana kyakkyawa ceh son kowa qin wanda ya rasa,nima kaina dana ganta saida na kusa tuntub'e tsabagen kyonta,gata fara tass.

Banji mamaki bama saeda ta tashi daga kan stool dinda take zaune na gaban dressing mirror d'in,doguwa ceh saedae ba can ba,batada jiki ko kad'an,saedae irin qirar coca-kolan nan ceh,to save your time,babyn ta had'u..

Bayan ta gama shirinta saeta d'au wayarta ta fito palour,inda ta tararda Mamanta zaune tana faman canza channel d'inda take kallo,ae tuni Maman ta tsaya tana qare ma y'artata kallo,kirari ta shiga mata kamar yadda ta saba yi mata a kullum "Suhana kenan,kin cancanci sunanki d'iyata,son kowa qin wanda ya rasa..Uwar mata lantarkin gida kenan,bani bada ki sae ma millionaire koma ince billionaire dan wannan kalar taki bata zaman ko'ina bace illa ta zaman palour,Suhana sarauniyar mata,kowa ya ganki dole yyi kishi,jaa zamaninki".

Koda Suhana ta gaji da wannan surutun maman nata,saeta ceh "ohh,isn't it ohk Mommy,na gaji da wannan zigarkin nikam",Maman tace "toh ae yabon gwani ya zamo dole,kin san hausawa sukan ceh 'so sone,amma son kai yafi',so kinga idan ban yabi nawa ba wazae yaba mun?"ta qare maganar tana me zurawa Suhana dake shirin qarasowa idanu..

Suhana tayi wani murmushin dake qara mata kyau,ga dimples d'innan tabarkallah,sun wani lotsa ciki,infact,her beauty is an extraordinary one.Ta kalli maman tace "gaskiyarki neh Mommy,gwanda mutum ya yabi nashi dan bbu me yabon mka shi..shiyasa nake sonki Allah",Maman tayi smiling tareda fad'in "that's my girl"..

Suhana ta karb'i remote d'in hannun Maman ta canza Sate d'in zuwaga INFINITY,inda ta shiga channel na *Joyprime*.Nan suka cigaba da kallon su cikeda jin dad'i.

Ba'a jima ba gateman nasu yyi sallama,suka ansa.Suhana ceh ta tashi taje dubawa,koda ta bud'e qofar sae yace da ita "wae ana magana dake neh a waje",Suhana ta wani b'ata rai tareda fad'in "ni kuma??",gateman d'in yace "eh,haka yace",Suhana ta d'anyi jim kad'an sae kuma tace "amma a iya sanina ba wanda yace mun zaizo guna yau,by the way ma meyasa bazae kiran ba,anya kuwa ka tabbatar ni ake nema??".

Gateman d'in ya d'aga kai alamar eh,Suhana tace "let it be,ina fitowa",nan ta koma cikin gida ta sanarda Mommynta yadda sukayi da gateman d'in sannan ta d'au gyalenta ta fita dan ganin waye..

A tsaye yake ya d'an jinginu da jikin motar shi,sae faman latsa wayarshi yake,da ganinshi ka ga d'an gidan masu shi,dan ko kayan jikinshi ya isa ya tabbatar maka da cewa d'an masu akwae neh.Ko kad'an beji isowar ta,shi dae kawae ya d'aga kai saiya ganta neh,murmushi yyi tareda fad'in "haba meh kyau,koh sallama bbu! Ai ban zaci kin iso ba",wani shegen harara Suhana ta watsa mishi tareda fad'in "what do you mean? Nazo gurin nan dan sauraron surutun ka?toh am sorry kashedi nazo maka"..

*HAMAGEE*

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now