Page 35

72 8 3
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 35 💦💦

3weeks ltr,
Yau ta kasance ranar laraba ceh,kuma yau su Mommy zasu kai Suhana Uganda dan bud'e sabon shafin karatunta acan kamar yadda ta buk'aci suyi mata.

Around 6 na yamma suka isa inda suka nufa masauk'in bak'i wato hotel na garin.Koda suka je kai tsaye d'aki reception d'in suka shiga inda Daddy yayi magana da receptionist d'in ta harshen turanci kan sunada buk'atar d'akuna biyu.Bayan sun gama maganar Daddy ya biya kud'i sannan wani yazo ya rik'e musu kayan da suka shigo dashi sannan ya shige gaba dan nuna musu d'akin nasu.

Bayan ya kaisu kuma saiya dawo.D'akin Suhana daban sannan na Mommy da Daddy guda d'aya.Bayan sunyi sallahr isha'i sai suka fito zuwa k'asa dan d'akin nasu a sama yake,mutane neh kaca-kaca a wajen,wasu na hira wasu suna shan drinks,wasu na caca-caca.Kowa da abinda yake.

Wani b'angare Daddy ya keb'e musu suka zauna,wajenda babu hayaniya sosae sannan ya kira wani waiter a wajen.Kowa ya fad'i abinda yake son ci sannan waitern ya je kawo musu abubuwanda suka buk'ata.

****
Washegari da safe suka nufa makarantar,basu wani b'ata time ba suka gama duk wani processes da ya kamata suyi dan already akwai wanda Daddy ya sani a kuma babba ne a wajen.Bayan sun gama sai suka koma hotel d'in da suka sauk'a.

2days ltr,
Da safe suka shirya suka sauk'e Suhana a school dan a cikin makaranta zata zauna kafin suka wuce 9ja.Koda suka dawo gida duk tasu sun damu dan basu saba zama babu Suhana ba,bama ya Mommy ba k'aramin missing Suhana tayi ba.

Wajen Suhana kuwa farin ciki takeyi dan anan babu mai saka mata ido tunda kowa rayuwarshi yakeyi.

Tana kwance a d'akinta tana kallo a youtube,qaramar wayarta ceh ta shiga ringing.Ba tareda ta duba wake kiranta ba ta amsa,"hellow".Daga d'ayan gefen aka amsa,a lokacin ta gane mai kiranta ba kowa bace illa Suby qawarta.Hirarsu suka sha sosai kafin tayi hanging up.Ana cikin haka kuma wayar Mommy ta shigo,d'agawa tayi tareda fad'in "hellow Mommy yanzu nake shirin kiranki Allah",Mommy tayi murmushi kafin tace "I know my child,u know Mommy can't wait too much to hear ur voice that's why I've to call now".

Murmushi Suhana tayi,"hmm,Mommy kenan harkin fara missing d'ina neh?",Mommy tace "sosai ma,the house seems incomplete without u my dear.Ke dai kawai abinda nake son kiyi shine u should concentrate on ur studies please,I don't want to hear something bad from u again,kinji?",Suhana tace "don't worry Mom,Suhana isn't a small kid now".Mommy tace "I know,but ki kiyaye still".Suhana tace "it's ok Mom,ina Daddy nah?".

Mommy tace "Daddyn ki ya fita ni kad'ai ceh a gidan saidai ki kira shi yanzu".Suhana tace "toh,I'll hang up now",Mommy tace "bye" sannan tayi hanging up. Bayan nan saita kira numbern Daddy,ringing na farko ya amsa "hellow",tace "hi Dad,shine baka kirani ba koh? Mommy ta riga kirana".Cikin shagwab'a tayi maganar,shi kuma yace "am sorry dear,yanzu nake shirin kiranki dan harna kai kan sunanki sauran nayi dailing neh saiga kiranki ya shigo,u know Daddy won't forget with u ai".

Saida tayi dariya kafin tace "yeah,I know my Dad.Ya hanya toh?".Daddy yace "lafiya lau,ya kike hope babu wata matsala koh?".Suhana tace "everything is fine here,don't worry Dad.I just miss the both of u shikenan",Daddy yayi y'ar dariya kafin yace "we already miss u too,but u shouldn't worry tunda mun fad'a miki zamu ringa zuwa miki in kina so ai".

Suhana tace "shikenan Dad,barin je nayi alwala yanzu",Daddy yace "it's ohk saina koma gida I'll call u insha Allah",tace "tam".Bayannan sai tayi hanging call d'in.

    hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now