Page 58

42 9 0
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 58 💦💦

    Mommy tace "hakane kam amma abin da fargaba neh ai,ki sanar musu d'in muga abinda Allah zaiyi". Suhana tace "shikenan I'll call his Mom right away",Mommy tace "to in kunyi wayan saiki kirani dan in san halinda ake ciki",Suhana ta amsa tareda katse wayar. Neman contact d'in Maman Farhan ta shigayi tana addu'ar Allah yasa tana dashi dan bata tab'a kiranta ba sai dai idan sunyi waya da Farhan saiya bata su gaisa,nan d'inma ba sosai ba.

     Allah yaso ta tana da numbern dan haka ba tareda b'ata lokaci ba ta fara kira. Ta kira ya kai sau uku amma shiru bata amsa ba,maybe bata kusa da wayanne a tunanin Suhana. Ajiye wayar tayi a gefe sannan ta kwanta bisa gadon bada niyyar yin bacci ba,ai kuwa bada jimawa ba baccin yayi gaba da ita tama manta bata kira Mommy ta sanarda ita cewa ta kira ba a amsa ba.

    A can asibiti kuwa 'yan uwan Farhan neh jingim a jikin shi daga masu kuka sai masu tagumi,gabad'aya hankalinsu ya tashi barinma Maman shi da sisters d'inshi guda biyu wato Farheen wacce take binshi da kuma Farhana 'yar autarsu kenan,daman su uku neh a wajen iyayen su,Farhan ne babba. Farheen d'in tanada aure so harda mijinta yaranta biyu suka zo,Farhana kuma tana university yanzu haka.

     Ainihinsu 'yan Cairo neh zama ne ya kawo Farhan Uganda sannan yana aiki a wajen. Yadda akayi suka gano Farhan na asibitin kuwa ba komai bane illa,kwanaki uku kenan da suka wuce Farheen da mijinta harma da yaran gabad'aya sunzo Uganda kamar yadda suka saba bayan kowane wata uku sai sunzo an musu medical check up,kuma a wannan asibitin Likitan dake dubasu yake,so every three months suna zuwa Uganda ganin shi.

     Kasancewar mijinta baya jin dad'i yasa Likitan yace musu su bari suyi five days kafin a sallame su. Cikin nurses d'in dake kula da Farhan akwai wacce tasan Farheen da mijin nata,Farheen ta fito daga office d'in Likitan kenan saiga wannan nurse d'in zata shiga ita kuma,ga files riqe a hannunta da alamu zata kaima Likitan ne. Ganin Farheen yasa ta tsaya tana tunanin inda ta santa,itama Farheen d'in taso ta ganeta.

     Can tace "Madam Farheen right?",Farheen tace "yeah,you worked at this hospital?". Nurse d'in tace "sure,I remembered the time you get birth to your first child,I was the one who received your delivery then". Farheen tace "of course I remember,how're you and work?". Nurse d'in tace "everything is absolutely fine,tnk you. Do you come to check your brother's health?". Farheen ta tambaye ta cikeda rashin fahimta "which brother? I came here with my husband and children, he isn't feeling too well that's why we haven't leave yet".

    Nurse d'in tace "but your brother Farhan if I haven't forget his name,he's here unconsciously". Farheen ta rud'e a wajen,nan ta nemi tasan inda aka kwantar da Farhan. A wajen Nurse d'inan ta kaita har d'akin da yake,ba kad'an ba Farhan tayi kuka kuma hankalinta yayi mugun tashi ganin situation d'inda yake ciki by then.

     Wani abinda ya sake bata haushi kuma shine ganin Suhana bata asibitin,koda ta tambaya sai aka ce mata tazo tun d'azu ta tafi,alamun bata damu da jinyar tashi ba kenan. Sannan meyasa Suhana bata fad'a musu halinda yake ciki ba tayi shiru ta munafurce su. Wannan abu ba qaramin b'ata ma Farheen rai yayi ba.

     www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now