Page 67

48 7 2
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 67 💦💦

    Rungume Mommyn tayi tana cigaba da kuka,bayan d'an qanqanin lokaci Mommy tasa hannu ta d'agota tareda share mata hawayen dake ta faman zabarya a fuskarta. Tace mata "be strong my child,you ain't a small kid anymore don't you know?,you have to be strong and patient kinji,Allahn daya had'a mu ya kuma raba mu shi zai sake had'a mu kinji",sam Suhana bata fahimci inda zance Mommy ya dosa ba hasalima kanta ya d'aure neh. Mommy ta cigaba "na sa an kira ki dan nayi miki nasiha kan kibi rayuwa a sannu,hanyar da muka d'ora ki daga farko ba mai b'ullewa bace dan haka ina roqonki da sauya ko zamu samu Rahamar ubangijinmu nida mahaifinki",daga nan Mommy ta shiga kuka.

    Itama Suhanan kuka take yi dan gabad'aya Mommy ta d'aure mata kai,da qyar ta iya daidaita kanta tace "naji Mommy amma bana so kina irin wannan maganan please, yana d'aga mun hankali it seems kamar you want to leave me as well",murmushi mai cikeda maganganu a cikin shi. Tace "you're not a child as I mentioned earlier, nasan zaki iya kulawa da kanki ko bayan raina dan bana ji a jikina zan kai labari,ke dai kawai be a good child and always pray to your parents kinji". Hawaye neh yake ta zuba shar-shar daga idon Mommy,tayi nadamar duk wani abinda tayi a rayuwa,tasan cewa bata kyauta wa Suhana ba dan duk halinda take a yau akwai nata kamishon.

    Washegari da yamma Allah yayi wa Mommy cikawa,sai dai tayi kyakyawan cikawa dan da kalmar shahada ta rasu. Suhana tasha kuka kuma tana kan sha,bayan anyi wa Mommyn wanka aka ajiye ta wa 'yanuwa su gama mata addu'ar da zasuyi kafin aje ayi mata sallah a birne gawar. A wajen ma ba qaramin kuka Suhana tayi ba dan daga qarshe kanma d'agata akayi a wajen.

    Days ltr,
Lokacin da dangin Mommy suka zo tafiya taso ta bisu dan tasan indai ta zauna a wajen dangin Mahaifin ta sai sun qarasa ta ganin cin mutuncin da suka tayi wa Mommy kafin ta rasu. Koda tayi qoqarin bin nasu sai dangin Daddyn sukayi uwa sukayi mad'aukiya akan ba inda zata,gidan wani qanin Daddy zata koma da zama. Dangin Mommy basuyi musu ba dan sun san qarfin dangin uba akan na uwa.

   Bayan wasu kwanaki tas ta tattara kayanta ta koma gidan immediate qanin Daddy,tsakanin shi da Daddyn bai wuce shekaru biyu da rabi ba. Tun ranar data koma gidan ta fara fuskantar rayuwar qunci,kun san dan idan mahaifinka yanada dukiya akan sauran danginshi,to dole a cikin dangin nashi akwai wanda suke jin haushin hakan,bama haushin sa shi kad'ai ba hatta iyalanshi ma basu bari ba,Allah ya kyauta.

   Bayan an raba gado na Suhana a wajen shi yake,yace shi dai duk rintsi ba zai ci hakkin maraya ba amma kuma ba yanzu zai damqa mata ba sai randa tayi aure. Haka ta cigaba da rayuwar ta cikin qunci da kewar iyayenta,abinka da bata saba da wahalar ba. Gashi matar baffan nata azababbiya ce dan shima kanshi bata barshi ba balle kuma Suhana,kullum cikin bauta take yi musu itada yaranta. Shima kuma babu abinda yake cewa gameda hakan.

   A sannu a hankali Suhana ta fara sabawa da rayuwar ta a haka,sai dai kafin ta saba tasha wahala sosai duk da ance ba'a sabo da wahala amma ita kam har ya bi jikinta,Suby qawarta kuwa tuni ta fita harqarta ko waya bata yi mata,idan ta kira ma bata amsawa. Kai qarshe ma blocking d'inta tayi a duk wata kafa na sada zumunta sannan tasa ta a black list yadda inma ta kira ba shiga zaiyi ba. Hakan ko ba qaramin d'agama Suhana hankali yakeyi ba.

    www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now