page 45

54 10 4
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 45 💦💦

    Washegari da rana bayan sallahn azahar Likitan ya kira shi dan dama sunyi exchanging contact, akan yazo ya d'auketa ne dama. Farhan yace mishi yana zuwa yanzun nan kafin yayi hanging call d'in. Wani tunani ne yazo mishi sai ya tashi ya nufi side d'in Suhana, bincike ya shiga yi wanda shi kanshi bai san na miye ba.

   Wayanta ya hango akan kujeran da ta zauna jiya dan haka yayi maza yaje ya d'auka ya shiga dubawa ko zai samu wani abin. Babu abinda ya samu kuwa a ciki dan ta canza wancen layin nata kuma Michael bai da wannan sabon layin. Ganin be samu abinda yake nema ba yasa ya ajiye wayar sannan ya bar side d'in ya koma nashi. Keyn mota kawai ya d'auka ya fice ya bar gidan.

    Yana zuwa ya d'auko ta ba tareda wani b'ata lokaci ba. Har suka fara tafiya,har suka iso babu wanda ya cema wani komai. Suna isowa aka bud'e musu gate suka shiga,kama daga kan me gadi har 'yan aikin gidan saida suka yi mata sannu da ya jiki. Sama-sama ta amsa dan damuwan dake kanta nada yayi mata yawa.

    Suna shiga side d'inshi yayi tana biye dashi har d'aki. Bayan ta rufo qofar sai ta dawo ta zauna gefen shi akan gadon. Ya d'ago ido ya kalleta ba tareda yace mata komai ba,ita kuma wannan shirun nashi ba qaramin cinyeta yake yi ba ta fi so ya fito suyi wacce zasuyi ta qare musu. Haquri ta shiga bashi kan abinda ya faru da ita da kuma na rashin fad'a mishi da tayi.

   Shi dai abin ya bashi mamaki jin tana ta yin magana d'aya dan bai tab'a sanin cewa bata san tana da HIV ba amma alamu sun nuna,ko kuma ta zaci bai sani bane,tunani dai iri-iri yayi tayi shi kad'ai. Can da ya gaji da jin labaran da take ta bashi akan abortion d'inta sai ya dakatar da ita dan shi ba wannan bane ma ya dame shi ba,yafi damuwa da cutar data sanya mishi.

    Ce mata yayi "why are you talking rubbish? Even once you didn't talk about the HIV that you share with me. Do you really think I wouldn't come to know about it? You are jocking with me",yana kaiwa nan ya fice ya bar mata d'akin tsabagen takaici,palour ya koma ya zauna zuciyar shi na tafasa.

   Suhana kuwa kasa motsawa daga inda take ma tayi dan taji wani baqon lamari a gareta,ita dai tasan a iya rayuwar ta batada HIV to akan miye Farhan zai d'aura mata wannan mummunan qazafin. A fusace ta miqe ta bishi palourn inda ta sameshi zaune idon shi jawur hakama fuskar shi,abinka da Jan fata.

   A kanshi ta tsaya ta soma zagge mishi masifa dan a ganinta raina mata hankali yake shirin yi. A iya saninta batada wannan cutar to akan miye zaice tana dashi. Babu mamaki ma shine yake da ita yana tunanin kar ta zo ta sani a samu matsala shine yake neman laqa mata. To bai isa ba.

   "Why do you think you can fool me? Do you really think I'm idiot, it will be better if you accept it that you have AIDS,I think it will be better",Suhana ce tayi wannan maganar,shi kuma bai ko kalle ta ba balle ya tanka mata sai dai a halin yanzu yana iya yi mata komai dan baya cikin hayyacin shi.

   Duk irin zage-zagen da tayi mishi bai isheta ba saita ta kira shi da 'he goat'. Ba qaramin harzuqa shi wannan kalmar tayi ba,bata ankara ba taji mari tas a fuskarta,sannan ya ja ta zuwa d'akin shi tareda danna lock ya rufe..

    www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now