Page 55

43 8 1
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*This page is devoted to all married men and women*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 55 💦💦

    Mommy ta kalli Suhana itama Suhanan kallon nata takeyi. Boka yace "idan baku amince ba kuna iya tashi ku bani guri amma na fad'a muku za kuyi dana sani,in kunne yaji toh jiki ya tsira". Mommy ceh tace "a'a Boka,kayi haquri zamuyi dukkanin abinda ka umarce mu da yinshi", boka yace "to kun sama wa kanku lafiya,sharad'i na biyun kuma sai mun fito zaku ji shi".

   Yana kaiwa nan ya tashi ya shiga daga ciki. Bayan ya shiga neh Suhana ta fara kuka tana fad'in "haba Mommy,ya zaki yi min haka. Kin san cewa ina aure kika amince mishi,kuma koda banda aure ma hakan ya kamata,na rasa da wanda ma zan kwanta saida wannan qazamin halittar,gaskiya Mommy kin cuce ni baki kyauta min ba". Haquri Mommy ta shiga bata tareda tsoratata akan abinda rashin yin hakan zai jefa su ciki. Suhana na matuqar son mijinta kuma bazata iya rasa shi ba,hakan yasa ta amince tabi bayan Bokan.

*Wa'iyazubillah,matar aure da wani qato,hakan ma kuma boka qazami,jaki,wanda Allah ya tsine mishi kuma yayi alqawarin ba zai shiga al'janna ba,haka wanda ya bishi ma ba zai shiga,mata muji tsoron Allah mu farka mu daina wauta dan wannan wauta ceh da jahilci. Da ke da mijinki da shi bokan Allah neh duk yayi ku to akan miye zakiyi tunanin boka zai iya tsara muku rayuwa? Allah yasa mu gama da duniya akan hanya madaidaiciya,ameen*..

    Sun kai kusan awa biyu suna abu guda,har Mommy ta gaji dan tun d'azu Farhan ke kiran wayan Suhana bata amsa,qarshe ma a silent ta saka wayar ta maida mata ita cikin jaka. Can dai saiga Suhana ta fito da gyalenta a hannu d'ankwalin ta kuma ta yafa shi haka a kanta. Kuka take sosai dan har idonta yayi ja ma. Da qyar Mommy tayi ta rarrashinta har tayi shiru dan bata son su shiga jama'a a gane tayi kuka.

   Bayan bokan ya fito saiya basu wani magani a d'an roba tareda fad'in yadda za ayi amfani dashi. Bayan nan kuma sai suka tafi,a hanya Mommy ta fad'a ma Suhana cewa Farhan yayi ta kiranta a waya saita san abinda zata fad'a mishi kafin su isa gidan. Ko amsawa Suhana batayi ba dan ita yanzu in akwai wanda take jin haushin sa to a bayan Mommy yake dan a cewar ta komai miye ya faru da ita ai LAIFIN tane tunda da bata kaita gun shi ba da baiyi mata hakan ba.

    Bayan sun koma gida straight d'akin da aka sauqe su Suhana ta wuce,a kwance ta samu Farhan na faman danna waya. Qarasowa tayi tazo ta kwanta gefenshi tareda d'ora kanta a qirjin shi. Farhan neh yace "where have you been,I've been trying your line since but you didn't pick it?". Suhana ta d'ago kanta daga jikin shi sannan tace "am sorry baby,I never know that you called",jakarta ta janyo ta shiga neman wayar. Koda ta ciro saita gwada mishi a silent wayar take shiyasa bata ji ba,daga nan bai qara cewa komai ba kan hakan.


    Koda dare yayi fita sukayi suka yo takeaway dan Farhan ba iya cin abincin gidan zaiyi ba,itama Suhanan hakane a rigimarta. Harda su Mommy a takeaway d'in,bayan sun dawo sai kowa ya karb'a nashi yaci. Daga nan kuma bacci kowa ya shiga yi dan dare ya riga da yayi.

     www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now