Page 65

56 7 1
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 65 💦💦

   Can ta dubi agogon wayanta sai taga qarfe goma sha d'aya har ya wuce. A nan ne ta fara zargin ko dai Mommy ta kai Daddyn India neh,amma a ina zata samu wannan kud'in. Can dai data gaji saita koma d'aki ta kwanta,bata jima ba nan ma tayi bacci. Washegari sai qarfe goma na safe ta tashi, babu batun sallahn asuba ta tashi ta shiga toilet tayi brush sannan tayi wanka ta fito.

    Wayan Suby ta kira inda suka sha hirarsu,anan nema Suby take ce mata zata zo garin gobe dan a yanzu ta koma gida gun iyayenta daman school ne ya kawo ta nan Kaduna. Suhana taji dad'in batun qawarta sosai dan sun jima basu ga juna ba sai a waya,bayan sun gama wayan Suhana tayi hanging.

★★★
India,
    Wanka akayi wa gawan Daddy kasancewar sun san cewa bashida 'yanuwa a nan kusa kuma akwai musulmai a wajen. Bayan nan aka yi mishi sallah da dai sauran hidimar da ake yi wa mutum idan ya mutu,daga nan aka kai shi aka binne. Shikenan shima tashi ta qare,Allah kasa mu gama da duniya lafiya,ameen.

    Washegari da safe Mommy ta farka garau,sai dai inta tuna da cewa babu Daddy a doron qasa saita fashe da kuka mai tsanani. Tana cikin wannan yanayin Likitan dake dubata yazo ganin yanayin jikin nata,nan ya shiga lallashinta kan ta daina d'aga hankalinta,mutuwa kowa yasani tana kanshi,yau mune gobe kuma ba mu bane so she should let things past.

    Koda aka sallameta bata koma gida a ranan ba sai gobe zata koma,bayan ta kammala biyan asibiti kud'in su saita nemi hotel inda zata kwana gobe saita wuce. Babu irin tunanin da bata yi ba gashi ita kad'an ta kamar rai,har yanzu bata sanarda kowa kan rasuwar Daddy ba tafi so saita koma gida kawai dan jimamin fad'in ma takeyi.

    Washegari ta tattara kayanta ta dawo gida,bata tsaya ko'ina ba kuwa sai gida. Lokacin da ta iso Suhana kuma bata gidan,ko ina taje? Sai Allah. Wanka Mommy tayi kafin tayi sallah,bayan nan ta fito ta nemi abu taci. Daga nan kuma ta shiga tura messages ma 'yanuwa da abokan arziqi kan cewa Daddy Allah yayi mishi rasuwa,bayan ta gama saita ajiye wayar ta d'an kishingid'a.

     Babu abinda take banda aikin kuka,duk lokacin da ta tuno da Daddy sai taji kewarshi ya cikata,barinma idan ta tuno yadda suke rayuwar su a da. Tasha kuka harta gode Allah dan da ganin ta kasan ta jima tana kuka saboda gabad'aya idonta sun kumbura sunyi jaa. Addu'a ta shiga yi ma Daddy na samun rahamar ubangiji,nima nace Allah ya jiqan Daddy,ameen.

    Can Mommy ta juyo hayaniya kuma kaman a cikin gidan neh,tashi tayi taje ta duba, bud'e qofarta kenan sai tayi ido biyu da Suhana,ga kuma Suby a bayanta daga dukkan alamu ita taje taryowa. Ganin yadda fuskar Mommy ya sauya,ga idonta sun kumburo sunyi jaa dasu yasa Suhana cikin tashin hankali,daga gani tasan ba lafiya ba. Da qyar ta iya fad'in "Mommy lafiya? Ina kka je tun shekaran jiya ban ganki ba ? Ina Daddyn yake,kun dawo tare neh?".

     A cikin wa'yannan jerin tambayoyin babu wanda Mommy keda niyyar amsawa,komawa ciki kawai tayi tana share qwalla. Suma cikin suka biyota,Suhana ta zaci akan maganar da sukayi neh dan haka ta shiga bata haquri "Mommy am sorry please, ban fad'i hakan da niyya ba ko kuma dan ban damu daku ba,nayi hakan ne dan ganin wahala kawai za ayi ta sha. Shi bai samu lafiya ba mu kuma mu qare cikin babu,amma kiyi haquri yanzu na amince a fitar dashi d'in,Mommy ki min magana mana".

     www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now